Part 12

858 44 0
                                    

💠💠💠💠💠

*BAMBANCIN AL'ADU.....* 💥

🌚🌚
💥

*©® 2018.*

*$tσrч____wríttєn.*
*вч*
_★нawwa м.υ {$mαѕhєr}.★_
*~___________________~*
★★★ ★ ★★★
___________________________
___________________________
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/

*вíѕmíllαhír-rαhmαnír-rαhєєm.*
_________________________
_________________________

*SADAUKARWA:-*_Ga mahaifina *LATE ALHAJI MUHAMMAD USMAN KUMO.* Allah чα ѕαdαr dα rαhαmαrѕα gαrєkα tαrє dα ѕαurαn αl'ummαr muѕulmí...ameen 😭._

*TUKUICI:*

*HASSAN ATK.*
*HUSSAIN ATK.*
_AND_
*KING BOY ISAH. 👑*


⏩2⃣3⃣


_______Da fad'uwar gaba janan ta iske haidar a parlour yana jiran fitowarta,jikinta a sab'ule take tafiya har shi kansa sai daya kula da hakan,tsayawa yayi da d'aura agogon da yake yana k'are mata kallo
"Lafiya kike kuwa baby...?"
Yayi tambayar idanunsa a kanta,kai ta girgiza masa tana k'irk'iran murmushin da ka gani kasan iya karsa fatar bakinta,saurin k'arasawa yayi ya janyota zuwa jikinsa
"Baby fad'amin me yake damunki,na ganki yau duk kinyi sanyi akwai wani abu da yake faruwa ne da ban san da shi ba...?"

"A'a babu komaifa hayatee..kawai dai inajin fad'uwar gaba ne,kuma ban san dalili ba..."

"Eyyahhh! baby sannu addu'a za muyi kinji,in sha Allah komai zai zama dai²,babu abunda zai faru kinji...?"
Da kai ta amsa masa,bakinta yana motsawa alamun addu'ah ta kwantar da kanta a k'irjinsa,bayanta ya shiga shafawa yana rik'e da ita
"Papa meya samu mami'nmu..?"
Kallon al'ameen yayi yana fad'in
"Bata jin dad'i ne.."
Rik'e k'afafunta yayi shima ya rungumesu yana fad'in
"Sannu mami Allah ya baki lafiya,papa Allah yasa mami baby za ta siyo mana..."
Idonta ta ware tana zare jikinta daga na haidar,harara ta b'allawa al'ameen tana fad'in
"Kajimin yaro da magana,har wani fatarmin yake na sake haihuwa yanzun..."

Kallonta haidar yayi k'asa² hannunsa rik'e da waist enta har lokacin yana fad'in
"Me kike nufine y'an matana...?"

"Haba hayatee yanzun dan Allah ni idan akace maka na sake haihuwa ai kaima kace a'a na huta ko..?"

Kallon rainin wayo ya mata,yana dariya ciki-ciki
"Lallaima baby wato bara ki sake bani baby yanzun ba,sai yaushe kenan..?"
Kallonta ta mayar kan al'ameen daya b'ata fuska,tana fad'in
"Dear maza jeka gurin aunty Zee ina zuwa kaji nayi mantuwa a bedroom..."

"Mami fad'amin na d'auko miki..."
Yaron ya fad'a yana kuma kafeta da kallo
"A'a kai dai jeka abunka baka san inda na ajiyeba,yi sauri kada dad ya bama sahala kayan dad'in nan..."

"Laaa! Mami kin tunaminma barinyi sauri..."

Kallon haidar tayi da yak'i sakinta,tana marairaice masa fuska,gane abunda take nufi yasa shi sakinta yaja hannunta suka fice,al'ameen kam ganin sun fito da iyayen nasa yayi saurin yin gaba da d'an gudunsa,sosai haidar ya matsota yana fad'in
"Allah baby ki shirya daren yau sai na sake baki baby,idan kuma mun riga mun samu zan k'ara masa k'wari ko...?"
Zamewa tayi zata barshi yayi saurin dank'ota yana fad'in
"Ai kam baki isaba yarinya,ni zakima wayo wato.."

"Ni dai dan Allah kayi hak'uri ka barni na huta,dukafa har yanzun babyta bata kai 2 years bafa,amma kake min fatan sake haihuwa,in sha Allah ba yanzunba,ni da sake haihuwa in sha Allah sai nan da kamar 5 years haka,kaga sahala ma lokacin har taimakona zatana yi ko..?"
Cike da murmushi tayi maganar,kuma bil-hak'k'i gaskiyanta ta fad'a,sakin baki haidar yayi yana kallonta,tafiyanma da yake nan yaja ya tsaya yana mata kallon from head to toe
"Hayatee lafiya kakemin wannan kallon...?"

BAMBANCIN AL'ADU.! (COMPLETED)✔Where stories live. Discover now