Part 5

1.1K 70 0
                                    

💠💠💠💠💠

*BAMBANCIN AL'ADU.....* 💥

🌚🌚
💥

*©® 2018.*

*$tσrч____wríttєn.*
*вч*
_★нawwa м.υ {$mαѕhєr}.★_
*~___________________~*
★★★ ★ ★★★
___________________________
___________________________
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
SMASHER AND HUBBEEY NOVEL'S GROUP@web.facebook.com

*вíѕmíllαhír-rαhmαnír-rαhєєm.*
_________________________
_________________________

*SADAUKARWA:-*_Ga mahaifina *LATE ALHAJI MUHAMMAD USMAN KUMO.* Allah чα ѕαdαr dα rαhαmαrѕα gαrєkα tαrє dα ѕαurαn αl'ummαr muѕulmí...ameen 😭._

*TUKUICI:*

*HASSAN ATK.*
*HUSSAIN ATK.*
_AND_
*KING BOY ISAH. 👑*


⏩1⃣1⃣


________Huci kawai mom keyi bayan ta k'are wayan,ita kad'ai sai ta kalli k'ofan da suka bi ta buga uban tsaki,abun duniya duk ya taru ya mata yawa,yatsarta tasa abaki ta cije had'e da yin k'wafa a fili kuma ta furta
"Wato ni za ayiwa wannan kitimurmurar....Dama Alhaji yasan haka yarinyar nan take shi ne suka had'a kai da d'an uwansa da kuma d'ansu a cuce ni haka ina ji ina gani kuma babu wani abu da nayi,wollahi bare tab'a sab'uwa ba wai bindiga a ruwa,dole nema nabi duk hanyar da zanbi na ganin na raba *HAIDAR* da wannan yarinyar mai zubin aljanu...Koda zan rasa komai nawa saina cimma burina....!"
_Tashin hankali kenan wanda ba a sa masa rana inji malam bahaushe..Allah ya bawa mai rabo sa'a mom ke da y'an koranki,muje dai zuwa...Wai mahaukaci ya hau kura...🏃_

Bayan fitarsu *HAIDAR* kasa magana yayi saboda yadda mom ta d'auki zafi akan maganar auren nan ya wuce misali,kallon *JANAN* yayi da duk jikinta yake a matuk'ar sanyaye,kallon fuskarta kad'ai ya isa mutum ya gane kad'an take jira tasa kuka binsa kawai take,duk inda yayi nan itama take yi a haka suka isa apartment en nasu coz yanzun ya tashi daga nasa shi d'aya 😜 inji my hulbateey fa amma ni babu ruwana,ita ya fara bawa hanya ta wuce sannan yabi bayanta,a parlour saman cuistion ta zauna a d'an d'osane kamar wata bak'uwa ko mai tsoron wani abu da zai cutar da ita,saman 3seater ya kwanta idanunsa a rufe saboda a wannan lokacin jinsa yake kamar mutum mutumi,hawaye ne suka fara sauka a saman fuskarta cike da damuwa ga missing Annah da take,ita sai yanzunma duk ta fara jin tsoron biyo mutumin da bata sani ba kuma basu da alak'a ta kusa ko ta nesa akan tsoron wani hukuncin da za'a mata,kukanta ne ya k'ara k'arfi lokacin data tuna yadda suka yi da mom ensa yanzun,yanzun ne taji kalaman mom sun fara sukanta har cikin ruhinta,sautin kukanta ne ya soma fita lokacin data tuna da komaifa zai iya faruwa da ita tunda yanzun gashi ita kad'ai ce bare a cikinsu kuma bata da kowa,d'an waigowa yayi side en da take zaune abunda kunnensa yaji masa shi idanunsa suka gani,a hankali ya mik'e ya zauna,shi duk ya rasama da wanne zai ji,kukan da take zai tsaya rarrashinta ko kuwa damuwar da mom ta haddasa masa yanzun idanunsa a kanta ya furta
"Zo nan..!"

A hankali ta d'ago kanta tana kallon gefen da yake,ita tamayi tunanin bacci yake data ga ya kwanta kuma yayi shiru bai kulata ba shiyasa ma taji ta sake shiga damuwa,k'in motsawa tayi a gurin har sai da ya sake maimaitawa,ganin bata da niyyan tashi yasa ya d'an had'e fuskarsa yana fad'in
"Bafa na son maimaita magana,idan na fad'a bana sakewa...Nd kada ki sake haka ya sake faruwa daga yanzun.."
Bakinta ta d'an kyab'e tana hararan gefe kamar shiya mata laifin,cikin nutsuwa ta mik'e tana nufan gurinsa kanta a k'asa,hannunta ya rik'o ya zaunar da ita gefensa,ba tare daya kalleta ba ya furta
"Wai ke wace irun mutum ce kullum kiyi kuka shi ne abunda yafi damunki..Ko wani abu na damunki ne...?"

BAMBANCIN AL'ADU.! (COMPLETED)✔Where stories live. Discover now