Part 10

849 43 0
                                    

💠💠💠💠💠

*BAMBANCIN AL'ADU.....* 💥

🌚🌚
💥

*©® 2018.*

*$tσrч____wríttєn.*
*вч*
_★нawwa м.υ {$mαѕhєr}.★_
*~___________________~*
★★★ ★ ★★★
___________________________
___________________________
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
SMASHER AND HUBBEEY NOVEL'S GROUP@web.facebook.com

*вíѕmíllαhír-rαhmαnír-rαhєєm.*
_________________________
_May d Almighty Allah see u through,wish u safe nd sound recovery dearie's *ANEESAT ABUBAKAR RIMI (ANEELURV/OUM AYMAN)* nd *RAHAMA MUHAMMAD RUFA'I NALELE (AUNTY'N LURV).*_ 😓😓😓
_________________________

*SADAUKARWA:-*_Ga mahaifina *LATE ALHAJI MUHAMMAD USMAN KUMO.* Allah чα ѕαdαr dα rαhαmαrѕα gαrєkα tαrє dα ѕαurαn αl'ummαr muѕulmí...ameen 😭._

*TUKUICI:*

*HASSAN ATK.*
*HUSSAIN ATK.*
_AND_
*KING BOY ISAH. 👑*


⏩1⃣9⃣


________Idanunta ta shiga murzawa kamar zata masa kuka haka take kallon fuskarsa da damuwa a tattare da ita,sake d'aure fuska yayi yana fad'in
"Malama ki kulamin da Yaro ko kada ki yarmin da shi..."
Saurin tallafoshi tayi sai faman k'ok'arin maida ruwan hawayen dake son sakkowa take,duk abunda take idonsa na kanta,shegen miskilancinsa ne kawai ya motsa yake mata hakan amma bawai dan yana jin dad'in hakanba sai don kawai yana son ya tsoratar da duk wani mai bak'ar niyya akan jaririn nasa ita kuma sai k'ok'arin danne damuwarta take,kallonta ya sake yi ta k'asan ido take kuma sai tausayinta ya kamashi tunawa da bata da kowa sai shi,kuma daga gare shine kad'ai take samun sassaucin damuwanta,tabbas idan ya mata haka bai mata adalci ba kasancewarta k'aramar yarinya ko bayan hakama yau en nefa ta haihu wanda ko cikakkiyar awa biyar da dawowarsu ba'ayiba daga hospital,sake kallonta yayi sai faman runtse idanu take yayin da hawayen dake mak'ale cikinsu suka samu damar zubowa,lips enta take cijewa hawayenta na ci gaba da sauka a haka ta daure tana feeding baby'n duk dan gudun kada ta sake b'ata masa rai,coz zuwa yanzun kam janan ta gama sanin matsayinta a gare shi,a kullum idan ta b'ata masa rai jinta take kamar ba itaba duka haka zata zauna cikin damuwa,ko yaushe bata da burin daya wuce ta faranta masa musamman yanzun da take zuwa islamiyya ta san duk wani hak'k'i nasa da yake rataye akanta,shi yasa a koda yaushe masifar taka tsantsan take da duk wani abu da zai gifta ya kawo musu samun rashin jituwa,tun bama lecture da suke sha a ialamiyya'n duk k'arshen wata,za'a tattara d'aliban makaranta da kuma kai katin gayyata ga wasu islamiyyu'n dake zagaye dasu dan mata su farka daga irin rayuwar da wasu ke shimfid'awa a gidajen aurensu abun ya k'azanta,duk k'arshen wata haka ake gayyato musu manyan malamai da sukayi shura a wannan zamani su fad'akar tare da wa'azantar da mutane dangane da wani mas'alah daya shigema mutane duhu,ta wannan hanyar sosai da yawa daga mahalarta taron suke k'aruwa saboda da yawan masu matasla ko a gidajen aurensu ko tsakaninsu da iyaye had'a da y'an uwa ko abokan zama suna k'ok'arin gyarawa.
A hankali ya had'a jikinsa da nata cikin hanya mafi sauk'i ya shiga lallashinta har ya samu tayi shiru sai ajiyan zuciya da take,haka suka yini ba tare da mom ta lek'o ba,a yayin da duk damuwa ta dad'a shigar Haidar bisa irin wannan halin ko in kula da mom ke nuna masa,lokuta da dama sai yayi tunanin tunkararta da maganar sai kuma ya tuna inda Allah (s.w.t) yake mana gargad'i game da iyaye,wannan dalili shi kad'ai ke dakatar dashi ga batin nufinsa,amma kam tunaninsa na gocewa a duk lokacin da tayi wani abu na badai-daiba dangane dasu,ko a yanzunma tunanin da yake kenan na rashin zuwanta ta duba ko lafiya suke,haka kuma yaci ta sauka daga mugun fushin da take dasu ko dan ganin wannan kyauta da Allah ya basu.
Tun yana sa rai da ganinta har abun yafi k'arfinsa haka ya fawwala lamarin gurin ubangiji da neman taimakonsa bisa wannan al'amari,tabbas yana da yak'inin wata rana Allah zai kawo musu sauk'i a cikin al'amuransu baki d'aya.
Zee kam ranan nan ta wuni ita tayi musu girki,shi ko gogan duk motsin da janan za tayi akan idanunsa dan ya sake kafawa ya tsare yana kuma jira,bacci ta yini tana yi a ranan sai wajejen maghreb sannan ta koma dai² wanda har ta samu daman fita parlour ta zauna suna hira da Zee da auta dake ta faman son d'aukan baby amma fir haidar ya hana,dan cewa yayi itama bata fi a d'auketaba a rarrasheta.
After maghreb dad ya dawo direct apartment ensu haidar yayi dan yana da tabbacin itace kad'ai surukarsa da haidar yake nufi,a parlour ya tadda su duka sun baje sai hira suke,while haidar na saman cuistion ya d'ora k'afafunsa saman d'an k'aramin table d'aya kan d'aya ya hard'e abunsa yana kallon news a AL-JAZEERA,sallaman dad yasa su duka suka maida hankulansu kan hanyan shigowa,tsaye yana murmushi suka hangoshi,a guje auta tayi gurinsa tana rik'e hannunsa,cike da shagwab'a ta soma kaima dad k'aran haidar kan hanata d'aukan baby da yayi,tabbas zatonsa ya zama gaskiya daya kasance baiyi b'atan hanya ba,da matsanancin farin ciki dad ya iso cikin parlour'n ya zauna,d'aya bayan d'aya suka shiga gaida dad cike da girmamawa sai sanya musu albarka yake,ko kafin wani lokaci tuni an d'auko masa jaririn,masha Allah shi ne kalmar data fara futa a bakinsa lokacin da yake kallonsa,yana murmushi yayi masa addu'a,sannan ya kalli haidar da fad'in
"To malam Aliyu Allah ya raya mana takwarana...!"
Kansa ya sunkuyar dan ya san tsokanarsa dad keyi,bayan dad yaga jaririn da girmansa yayi tama janan sannu sannan ya fice a side en nasu.

BAMBANCIN AL'ADU.! (COMPLETED)✔Where stories live. Discover now