Part 2

1.6K 73 2
                                    

💠💠💠💠💠

*BAMBANCIN AL'ADU.....* 💥

🌚🌚
💥

*©® 2018.*

*$tσrч____wríttєn.*
*вч*
_★нawwa м.υ {$mαѕhєr}.★_
*~___________________~*
★★★ ★ ★★★
___________________________
___________________________
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV & GENTLE NOVEL'S GROUP@web.facebook.com

*вíѕmíllαhír-rαhmαnír-rαhєєm.*
_________________________
_________________________

*SADAUKARWA:-*_Ga mahaifina *LATE ALHAJI MUHAMMAD USMAN KUMO.* Allah чα ѕαdαr dα rαhαmαrѕα gαrєkα tαrє dα ѕαurαn αl'ummαr muѕulmí...ameen 😭._

*TUKUICI:*

*HASSAN ATK.*
*HUSSAIN ATK.*
_AND_
*KING BOY ISAH. 👑*


⏩3⃣

________Yanayin daya tunkarota da shi yasa ta dad'a k'ank'ame jikinta tana fasa k'ara data sashi jan brake ba tare da ya samu damar k'arasawa inda take ba.
A hankali ya d'an koma da baya kad'an yana sakin tsaki,a kaikaice ya sake kallonta kafin ya maimaita tambayan nasa
"Ke me kikemin a nan...? kuma uban waye ya aikoki...?"

Zuciyanta na skipping saboda tsoronsa da taji ya kamata lokaci guda,ta kasa bashi amsa tana tunanin ta ina zata fara sanar masa daga inda aka turota,shirun da tayi shi yake k'ara tunzura shi wani haushinta ya k'ara kamashi.
Juyawa yayi ya fice a d'akin dai-dai lokacin da wani yaronsa yake k'ok'arin yin magana a bakin tantin nasa,fitowan nasa yasa secretary en nasa *ISMA'IL* ya sauke kansa k'asa yana fad'in
"Yallab'ai barka da fitowa....."
Ba tare da ya jira ya amsa masa ba yaci gaba da fad'in
"ammm! yallab'ai gaskiya akwai damuwa...Amma idan a cikin maganata da zan fad'a akwai kuskure ayimin afuwa..."
Kallonsa kad'ai *HAIDAR* yayi ba tare da yayi magana ba,shi kansa *ISMA'IL* bai jira amsawar ogan nasa ba ya soma da fad'in
"A gaskiya yallab'ai dama maganata ba kan komai bane face wad'annan y'an matan da aka turo mana..."
Dad'a bud'e ido *HAIDAR* yayi yana kallonsa ta cikin hasken farin watan,shi kuma ya sake d'orawa daga inda ya tsaya
"Tabbas wannan tsari na garin nan mu a gurinmu zamu kalleshi da wata irin fuska,kuma yallab'ai ya kamata ace y'an matan sun koma inda suka fito dan gujewa afkawarmu a halaka..."
Sai a lokacin ya soma fuskantar dalilin daya sa yaga yarinyan a nasa d'akin,siririn tsaki ya saki wanda yasa *ISMA'IL* ya dad'a jin jikinsa yayi sanyi,a nasa tunanin ogan nasa yaji haushin maganar daya masa,duk da bawai yasan halin *HAIDAR* duka ba,amma kam ko a company zai iya shaidarsa kan baya shiga sabgar mata,hasalima zai iya bada shaida akan bai tab'a ganinsa da mace ba,sai daifa hausawa na cewa "ba a yabon d'an kuturu har sai an ga ya tashi da yatsunsa",wannan dalili da kuma shirun da yayi d'azun lokacin da aka kawo su yasa *ISMA'IL* en kasa bambance ainihin halayen nasa.
Dogon numfashi ya sauke sannan ya kalli inda secretary en nasa yake yana fad'in
"Toh! nima dai nayi mamaki dana ga mace cikin d'akina,ni a tunani ma ko aljana ce saboda kuka naji tana yi..."

Da sauri *ISMA'IL* dake duk'e ya d'aga kansa yana fad'in
"Kuka kuma yallab'ai....? Tabbb! gaskiya to yarinyar ta musamman ce,ni kam wacce na tarar ranka shi dad'e abunma bare fad'u ba saboda fitsararta tayi yawa.Koda yake haka halayensu yake ba abun mamaki a nan.."
Da katar da shi *HAIDAR* yayi coz ba kowane magana yake da time en saurare ba,kuma haka k'a'idarsa take ba kowa yake shiga sabgarsa ba
"Ina zuwa ka jirani na fito..."
Yana fad'in haka ya mik'e ya shiga d'akin,a yadda ya barta a haka ya dawo ya tarar da ita kamar mai jin sanyi,kansa ya d'auke daga kallonta da yake a hankali dan ya fuskaci maganarsa na bata tsoro ya furta
"Tashi muje ki koma inda kika fito..."

BAMBANCIN AL'ADU.! (COMPLETED)✔Onde histórias criam vida. Descubra agora