Part 14

762 40 0
                                    

💠💠💠💠💠

*BAMBANCIN AL'ADU.....* 💥

🌚🌚
💥

*©® 2018.*

*$tσrч____wríttєn.*
*вч*
_★нawwa м.υ {$mαѕhєr}.★_
*~___________________~*
★★★ ★ ★★★
___________________________
___________________________
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/

*вíѕmíllαhír-rαhmαnír-rαhєєm.*
_________________________
_________________________

*SADAUKARWA:-*_Ga mahaifina *LATE ALHAJI MUHAMMAD USMAN KUMO.* Allah чα ѕαdαr dα rαhαmαrѕα gαrєkα tαrє dα ѕαurαn αl'ummαr muѕulmí...ameen 😭._

*TUKUICI:*

*HASSAN ATK.*
*HUSSAIN ATK.*
_AND_
*KING BOY ISAH. 👑*


⏩2⃣7⃣


_______K'wak'walwarta tuni ta tafi yajin aiki na wucin gadin son tunawa da al'amuran da suka gabata,ta jima tana tunanin yadda abubuwan suka dunga faruwa,kafin daga bisani ta sauke wani wawan ajiyan zuciya,a hankali ta kalli wajen sai dai wayam babu kowa sai ita kad'ai,a hakanli ta tashi ta zauna saman gadon ta dafe fuskarta da hannayenta duka biyu,abubuwan duk data aikata sai yanzun ne take ganin rashin dacewar yin hakan,sam a matsayinta na uwa kuma kaka ga yaran da basu jiba bare su gani bai kyautu ace haka tabi dasu ba,sai yanzun take ganin son zuciyar data aikata wanda hausawa kance "Son zuciya b'acinta",irin maganganun da dad ke yawan yi mata a lokacin da yadda sukaita samun sab'ani akan hakan babu wanda bata tuna ba,har ta kaiga kawowa k'arshen tunaninta da inda dad ya sake aure kawo yau kuma da maganar al'ameen ta tsaya mata a k'ahon zuciyarta,wasu sabbin hawayen ta sake sharewa cikin murya irinta mutumin da yayi laushi ta furta
"Astagfirullah..! wa'atubu ilaik..Allah kasa wannan shi ne zai zamo k'arshen duk wata matsala dani na haifar da ita a gidan nan,Allah ka yafemin kuskuren dana aikata,tabbas a matsayina na uwa bai kyautu na aikata haka ba,Allah ka gafartamin zunubaina ba kuma dan halina ba,sai don tawasulli da nayi da kyawawan sunayenka,Allah na gode maka daka bani ikon ganin lokacin da zan gyara kuskurena tun ina da rai ban kaiga kushewa ba.."
Maganganu haka mom taita fad'insu a fili wad'anda ke nuni da tabbas mom en ta saduda ta kuma bi Allah da manzonsa,jin kanta ya fara mata ciwo saboda tsananin tunanikan da take yi a y'an kwanakin yasa ta kwanciya,babu jimawa bacci ya d'auketa...

Tunda Annah ta rakasu ta tsaya nan waje kamar tasan zasu gudo,duk maganar da mom suka yi da Al'ameen en babu wanda bata jiba,kuma tabbas maganar bata mata dad'i ba,musamman amsar da Al'ameen en ya bada,ko ba komai ai itan kakace a wajensa mahaifiyar ubansa bai kamata ace yaro k'arami ya iya fad'in hakan ba,dole ne ta gyara masa kalamansa kada wata rana ya fad'awa wani a waje tunda aka fara haka da shi a cikin gida,idan har wata rana ya fad'a a wani wajen aka ji tofa tabbas su za'a zaga,da wannan k'udirin tayi niyyar barin wajen sai kuma Allah yasa taji alamun bud'e k'ofa,kallonsu tayi ta had'e fuskarta alamun babu wasa,hanya ta nuna musu ba tare da tayi magana ba,sum² suka wuce musamman Al'ameen da yake sauke kai k'asa ganin irin kallon da yaga Annah nayi masa ya tabbatar masa da yayi laifi ba k'arami ba,suna shiga bedroom en ko yaga ta rufe k'ofa tana nufoshi,ja baya ya fara yana fad'in
"Please Annah Allah ban k'ara yin laifi..Kiyi hak'uri pleaseeee..!"

Harara ta b'alla masa tana fizgo shi daga jikin gadon,kunnensa ta kama sosai
"Wato kasanma kayi laifi ko..? Me kace d'azun da mom na maka magana...."

"Allah baran sake ba,kiyi hak'uri.."
Hannunsa rik'e da nata data kama masa kunne,sai ihun zafi yake
"Idan ka kuskura na sake jin ka fad'awa wanima ba itaba Allah zan cire maka kunne ne,kuma daga ranar nima babu ruwana da kai ka ji ni ko..?"
Saurin amsa mata yai "Allah baran kumaba,dan Allah kiyi hak'uri.."
Sakinsa tayi tana fad'in "Maza b'acemin anan,kuma ka tabbata kaje ka bata hak'uri idan kana so nima na hak'ura.."
Juyawa yayi da sauri ya fice saboda son farantawa Annah,duk da kasancewarsa yaro yasan mai yi masa (rayuwar yarinta kenan tabbas tana da hatsari kada ka sakankance kana zaluntar yaro da tunanin baya ganewa,wallahi duk yana haddace komai a k'wak'walwarsa,lokaci kad'an idan ya fara amayar maka da abunda kake masa,zaka sha mamaki dan ba zato bare tsammani zaka ji maganganun a dai² lokacin da hakan zai faru,Allah yasa mu gane)..

BAMBANCIN AL'ADU.! (COMPLETED)✔Where stories live. Discover now