Part 11

817 43 0
                                    

💠💠💠💠💠

*BAMBANCIN AL'ADU.....* 💥

🌚🌚
💥

*©® 2018.*

*$tσrч____wríttєn.*
*вч*
_★нawwa м.υ {$mαѕhєr}.★_
*~___________________~*
★★★ ★ ★★★
___________________________
___________________________
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
SMASHER AND HUBBEEY NOVEL'S GROUP@web.facebook.com

*вíѕmíllαhír-rαhmαnír-rαhєєm.*
_________________________
_________________________

*SADAUKARWA:-*_Ga mahaifina *LATE ALHAJI MUHAMMAD USMAN KUMO.* Allah чα ѕαdαr dα rαhαmαrѕα gαrєkα tαrє dα ѕαurαn αl'ummαr muѕulmí...ameen 😭._

*TUKUICI:*

*HASSAN ATK.*
*HUSSAIN ATK.*
_AND_
*KING BOY ISAH. 👑*


⏩2⃣1⃣


________Sakinta suka yi duka suka koma gefe,kawunansu a k'asa saboda cika umarni,kamar daga sama ta ganta cikin cage gefe kuma mutanen ne tsaye cikin wani irin sauti taji an fara magana da wata irin murya da take amsa kuwwa
_"Laifi na farko da wannan mata ta aikata,tabbas laifi ne daya gawurta,domin kuwa ta kasance mai sab'awa mijinta,ta inda a halin da ake ciki yanzunma bata shiri da shi,baya da wannan sam bata iya tausasa masa kalamai,duk abunda yazo mata fad'arsa take a gare shi ba tare da tunanin ya dace tayi hakan ko bai dace ba..._
_Laifinta na biyu-ta kasance mai yanke hukunci cikin zalunci...ko kad'an wannan mata bata kasance cikin mutane adalaiba, akan wannan laifin nema suka samu sab'ani da mijinta..._
_Laifi na uku-ta kasance bata tausasawa yara,ko kad'an bata kasance daga cikin mutane masu tausayi da jin k'an na k'asa da ita ba..._
_Laifinta na gaba-ta kasance bata aldalci a tsakanin y'ay'anta, kamar yadda Annabin rahama (S.A.W) ya nusar damu akan adalci a tsakanin y'ay'a.."_

Jikinta ne ya hau rawa ganin yadda mutanen ke jifanta da muggan kallo,muryar shugaban ce ta sata kallon gefen da yake inda yake fad'in
_"Lallai ne wannan mata ta cancanci hukunci mai tsauri,amma kafin nan ku hura wuta ku cillata ciki saboda ko a lahira ita ce makomar azzalumai kuma fajirai...."_

"Wayyooo! Allah na shiga uku, dan Allah kuyi hak'uri wollahi na tuba...zan gyara.....ku kyale ni na tafi..na daina daga yau...!"
Kalmomin dake fita daga bakinta kenan tana ihu,bakinta duk sai jini yake fiddawa yayinda take ta faman taune harshenta kan tsabar rok'on da take musu zuciyarta cike da tsoron yanayin da suke ciki,gagarumar wuta aka had'a acikin ramin dake gabanta,har lokacin bata daina fad'in abunda take fad'a ba tun farkon.
_"Lokacin da zaki tuba ya tsere miki saboda ubangiji ya baki dama na tuba,kika k'i bi ki kayi fatali da damarki,a yanzun lokacin mune mu hukuntaki,mu wakilai ne daga cikin jinsin al-janu muna zuwa ne domin hukunta irinki marasa adalci,kafin kuma kije ki tarar da azabar ubangijinmu....Ku jefata wannan shi ne k'arshenki kuma makomarki ko a lahira da ita za'a miki azaba.."_

Dai² sun d'agata suka hullata cikin ramin,bata kaiga sauka cikin raminba amma hucin wutar har ya iso mata,tayi wani razanannen k'ara daya haddasa mata farkawa a baccin,jikinta duk ya jik'e da gumi,kafin wani lokaci d'akin har ya fara had'a mutane,masu neman ba'asin faruwar hakan,juyawa kawai mom keyi tana kallon mutanen gurin tana raba idanu,amma sam ta kasa magana,ganin haka yasa duka mutanen suka shiga fashewa wasu na fad'in
"Allah ya kyauta,sharrin mafarki ne kawai ta had'u da shi..."

Bayan kowa ya fice a d'akin ne,mom ta kalli d'akin nata,tabbas wannan mafarki ya tsoratar da ita ba kad'anba,tunaninta bai wuce ta gano mai hakan yake nufi ba, amma duk iya hasashenta bata iya gane komai daga mafarkin nataba,komawa tayi ta kwanta sai dai me,nan baccin yayi k'aura a idonta,yadda taga rana haka take zaune idanunta sun soye....

BAMBANCIN AL'ADU.! (COMPLETED)✔Where stories live. Discover now