RUWAN DARE............1~2

2.9K 93 4
                                    

_*RUWAN DARE....*_🌷
  _a true life story_

_*By ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_

  _*Page 1~2*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

_KEBBI STATE....._
       _*****ZURU L/GOVERNMENT_
Wani kyakkyawan gidane dake cikin wata matsakaiciyar unguwa wacca batada hayaniya da cinkoson mutane sosai acikinta,,,...

Kyawawan yarane acan bayan gidan  suna wasan 'yar gala--gala da 'yar chab'al, daga can gefensu kuma wasu kyawawan 'yammata ne guda biyar suna wankin uniforms masu tarin yawa wanda daka gansu kasan na yara da yawane bana d'aya ko biyu ba,,,.....

Yaran su shida ne mata biyu maza hud'u kowannensu sanye yake da wando da riga dakuma rigar sanyi kasancewar lokacin damina ne anyi ruwa garin yad'au sanyi, y'ammatan ma sanye suke da riga da wando da rigar sanyi,,,".......

Yanayin garin yanada dad'i sosai ba rana ni'ima ta sauka iska mai dad'i sai kad'awa take ko'ina abun gwanin birgewa, y'ammatan sai faman wankinsu suke sunashan Music kuma suna fira, yaran ma wasansu suke abunsu,,,.....

Bayan y'ammatan sungama wankinsu sun shanya kayan sainaga sunbud'e wata k'ofa sun wuce, da'alamu dai k'ofarda zata sadasu da cikin gida ce, suna shiga acikin babban parlon gidan sainahango wasu kyawawan mata guda biyu d'aya fara d'aya kuma chocolate colour, d'aya daga cikin 'yammatan ce naji tace "wash....!!! Momy wallahi wankinnan akwai wahala yakamata asake d'aukar mana masu wanki gaskiya" tai maganar tana zama akan kujera,,,.....

Wacca takira da momy ce naga tad'ago takalleta tareda hararanta sannan tace "Ehh...lallai *SUHAILA* eh lallai kam ai dole a d'aukar maku masu wanki tinda shi wanda zai d'auki masu wankin yadinga biyansu kud'i dik wata baisan zafin kud'iba gashi kuma bai haifi 'yay'anda ke tausayinsa ba ko" shagwab'e fuska tai wacca aka kira da SUHAILA sannan tace "kai momy nifa bahaka nake nufiba",,,.....

Wata uwar harara ta watsa mata sannan tace "yanzu dan Allah yarannan dan bakuda tausayi da irinku a gida sakwa sakwa 'yammata masu jini a jika za'a d'auki wasu masu aiki ai ni a tinanina ko y'an aiki dadyn ku yace zai d'auka zaku hanasa wallahi saboda a gidannan banga abunda bazaku iyayiba saidai idan bakuso yinsaba, saboda haka gwanda ma ku mik'e tsaye dan bazamu sake yin aikin komaiba a gidannan kune zaku dingayi saboda idan kukaje gidajen mazajenku yazamana orlready kun iya baza'a zagemuba"  itadai shuru tai batasake cewa komai ba,,,....

Sauran 'yammatan kuma dariya sukeyi, d'ayar matar ce tana dariya itama tace "y'ata SUHAILA kyalesu kinji dadyn ku yakusa zama chairman na ZURU L/GOVERNMENT insha Allah in Allah yasa yaci wannan kujerar aikin komai bazaki sake yiba a gidannan kinji y'ata"  jin abunda tafad'a yasa da SUHAILA da sauran 'yammatan suka mayarda kallonsu izuwa gareta cikin tsintsar mamaki har suna had'a baki wajen furta "CHAIRMAN MAMA",,,....

Ganin yanda sukai maganar ne yak'ara bata dariya tace "tabbas insha Allah" SUHAILA tace "mama yaushe akai wannan abun amma bamusaniba" wacca ta kira da mama tace "wallahi muma b'oye mana yai sai yanzune yake fad'amana kunsan halin dadyn ku bakomai ne yake saurin fad'a da wuri ba" wani irin murmushin farin ciki SUHAILA tai tace "kai amma wallahi nai farinciki mama Allah yabasu nasara" atare suduka suka karb'a da ameen cikin tsintsar farinciki,,,"....

D'aya daga cikin 'yammatan tace "ashe munkusa zama 'yay'an y'an siyasa muma za'afara d'okin ganinmu a fili kamar y'an film" tai maganar tana dariya suma din dariyar suke,,,....

Momy ce tace "to oya atashi zuwa aiki  kowacce tazab'i abunda zatai ai saurin ak'are dawuri" nantake kowacce tafara zab'an abunda zatai SUHAILA tace "nidai momy ni zan gyara bedroom d'in mama da namu bedroom d'in" tace "ok to ayi sauri kuma ayi aiki mai kyau fa kunsan banason aiki mara kyau sharp--sharp ai agama ko baiyi kyauba, No banaso a kwantarda hankali ai mai kyau kunji ko tinda aikin ba sabon abubane agareku" suka amsa da to sannan kowacce tawuce zuwa aikinta,,,"....

D'aya daga cikin y'ammatan ce ke gyaran babban parlor, tana cikin gyara saiga yaran sunshigo, dasauri ta dakatardasu cikin fad'a tace "kai...kai...malamai ku dakata ku koma waje har nagama gyara sannan kushigo kunga yanzuma moping nake kuma baisha iskaba bai busheba dakun shigo lallacewa zaiyi" wacca take babba acikin yaran ce tace "kai ya Aysha ni wallahi k'ishi nakeji" wata uwar harara ta dalla mata sannan tace "to wallahi bazaki bi ananba kije a pampom waje kisha ruwan mana dole sai ruwan fridge ne kad'ai ruwan sha a gidannan",,,.....

Bubbuga k'afafuwa yarinyar tafara tafara kuka tana fadin "wallahi ni bazansha ruwan pampom waje ba" ganin wacca takira da ya Aysha d'in bazata barta tashiga ba yasa tafara kwallah kira izuwa cikin gida "ya Zainab....yaya zainab" wacca takira da zainab ta amsa da "na am mimi menene" cikin shagwab'a tace "dan Allah kicewa ya Aysha tabari mushigo wallahi kishirwa nakeji kuma tahanamu shigowa" dariya wacca aka kira Zainab tai sannan tace "kuzagayo ta k'ofar baya moping take yanzu" badan sunsoba yaran suna k'unk'uni suka wuce,,,.....

Sai kusan 1:00pm sannan suka kammala aikinsu nan sukai wanka sannan kowacce ta zauna tana latse latse waya, SUHAILA ce tace "ya Aysha please kutashi muje gidan ya hafsat kunga tinda sukazo sau d'aya kawai mukaje gidanta" hafsat tace "ni dai gaskiya bazaniba bacci nakeso nai",,,....

Bataso hakaba danhaka tajuya ga d'aya daga cikinsu tace "Susi tashi muje dan Allah" itama cikin d'an b'ata fuska tace "Sister wallahi nagaji sosai kije kawai" harara kawai ta watsa mata batasake cemata komaiba tad'auki k'aton hijab d'inta har k'asa yake tasaka tad'auki phone d'inta tafita,,,"....

Kai tsaye d'akin momy tawuce tanemi izinin fita, momy kuwa bata hanataba saidai tace dole taje da d'aya daga cikin kannenta saboda bataso suna fita yawo sukad'ai, SUHAIL batai musu ba saboda itama bason fita itakad'ai takeba danhaka tace mimi tasaka hijab d'inta suje,,,...

Tafiya take acikin nustuwa da tsintsar kunya irinta y'a mace hanunta sakad'e dana k'anwarta mimi, tafiyar kuma akan gefen titi ba a tsakiyar titi ba, sunfito layinsu har sun d'auki hanyar babban titi ko zasu sami abun hawa saboda su layinsu masu abin hawa basu cika shiga cikinsa ba ana wahalan samun abun hawa a layin shiyasa dole saisun fito har babban titi suke samun abun hawa gashi kuma akwai nisa sosai tsakanin layinsu da babban titi,,,,....

Suna a tsaye suna jiran a dai--daita sahu sai SUHAILA taji daddad'an k'amshi wanda ko a mafarki tajisa tasan ko nawaye, ahankali ta lumshe fararan idanuwanta tareda jan numfashi, daddad'an iskanda ke kad'awa ya hard'e da daddad'an k'amshin tiraren nantake saisuka bada wani yanayi mai sanyin dad'i,,,....

Mimi ce tai dariya sannan tace "Assalamu Alaikum ya mu'allim" shima cikin fara'a yace "waalaikisalam ya binti Ahmad" SUHAILA kuwa ahankali tajuyo tareda sakarmasa wani ni'imtaccen murmushi sannan tace "Barka da warhaka ya malami na" shima cikin murmushin yace "Barka dai binti Ahmad fatan dik kuna lafiya" tace "lafiya k'alau Alhmdllh"......"to masha Allah, ina zakuje haka" cikin yanayin kunya tace "umm zamuje gidan yaya hafsat ne" k'in tafiya yai saida ya nemamasu a dai--daita sahu suka hau kuma yabiya mai a dai--daita sahun kud'insa nan SUHAILA tamasa godiya sai yace mata "SUHAILA kidaina man godiya ga dik abunda namaki soyayya da k'auna itace takawo hakan, a guna dolene kuma wajibine nai hidima agareki saboda nanda wani lokaci kad'an hidimarki dama komai naki zai dawo agareni so kinga gwanda nafara yi tin yanzu saboda nafiki lada acikin zaman aurenmu",,,....

Dariya tai harsaida fararan hak'oranta da suka bayyana tace "ok kenandai wayou ne kakeman aikuwa bazan bari kafini lada ba nima zan k'irk'iro wata hanyar sakankamaka fiye da abunda kakeman"  dariya yai tareda fadin "asauka lafiya ya mu'allima" tai murmushi tareda d'aga masa hanu alamar bye bye, shima d'in bye bye d'in yamasu suka wuce.......

_*SHIN WACECE ITA.....?*_

_Kubiyoni sannu a hankali domin jin gundarin labarin_

#/Vote
#/Share
#/Comment

'''AUFANA for life '''

RUWAN DAREWhere stories live. Discover now