RUWAN DARE.....Complete

1.2K 42 19
                                    

_*RUWAN DARE.....*_🌷
  _a true life story_

_*BY ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_

  _*Page 35~36*_

🌷 _*END*_🌷

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Sannu ahankali suka fara test wanda wannan lokacin kuma yai dai--dai da fara siyasar dady ta biyu ta shekarar 2019 domin neman cigaba da mulki akaro na biyu,,,.....

Kamar kullum yauma Nazir ne yazo ya d'auketa yafita daita, yauma kangon gidansa yakaita sukaita holewarsu suna shanawa abunsu kasancewar kuma weekend ne,,,....

Sai washe gari ranar sunday sannan yamaidata school,,,"......

     ______________________

Shak'uwa mai k'arfi tashiga a tsakanin SUHAILA da Nazir dan tinda ya d'andani zumarta yakasa rabuwa daita, dikda kuwa bawani abun kirki yake sakamata dashi ba dan saidaima ita tabashi acikin kud'inda ke shigowa dik month a account d'inta daga gun mazanda take mu'amala dasu,,,....

Nazir tamkar ya asirce SUHAILA saboda yanda take masa, dik abunda yace yanaso agunta to yagama samu haka kuma dik abunda yace tamasa ba musu takeyin saurin yimasa batareda musu ko gardama ba,,,......

Hakan yasa Abdul yak'ara samun wadataccen wulak'anci agunta saboda yanzu ko 15mnts bata iyayi tana fira dashi matuk'ar Nazir yana kusa daita sai tadinga masa magana in harshness, a wayace kawai sukeyi acikin isasshen lokaci,,,.....

Sannu ahankali dady suka fara gudanarda siyasarsu acikin hope da cikekken kwarin guiwar cin nasara insha Allah,,,...

Sannu ahankali suka kammala zana test suka fara zana jarabawa amma SUHAILA ko ajikinta don baruwanta da karatu bare tasaka abun a ranta wai tadinga yin shirin exam don takanyi ma kwana d'aya, biyu bata school,,,.....

    
Yau takasance Wednesday zaune take acikin room d'insu ita da nasifa, nasifa linke kayanta take da akayo mata wanki daga cikin gari itakuma SUHAILA tana a kwance tana game da galleliyar wayarta,,,.....

Kamar wacca aka tsakara kawai saita mike tsaye tasaka takalmanta takama hanyar fita, kallonta nasifa tai tace "ina zakije SUHAILA?" batareda tawaigo kota tsayaba tace "yoto dama dole ne saikinsan dik inda zanje saikace wacca aka saka tai gadina" tana maganar ne tana ficewa daga d'akin,,,....

Kallo kawai nasifa tabita dashi saboda tinda sukai waccan fad'an lokacinda SUHAILA tai ciki na biyu tin lokacin tadaina bata girma yanda taga dama haka take mata saboda yanzu gani take tafita zama fitacciya acikin bariki,,,....

Kai tsaye d'akinsu murja walie tawuce, koda taje kuwa saita taddasu kowacce kwance akan bed d'inta suna karatu, cikin sallama da faraa tashiga suka d'ago suma cikin faraa suka amsa mata sallamar sannan tazauna kan bed d'in ummy sambo kasancewar shine farko na murja yana daga can kusa da window,,,....

Murja ce tace "Ah yau SUHAILA acikin room dinmu abunda kikai kusan wata shida bakiyiba, wai kodai wani abu kikazo nema ne dan har yanzu ban yarda dacewa haka kawai kikashigo ba" dariya tai wacca take k'ara mata kyau sannan tace,...

"Ah habadai bahaka bane wallahi commitment ne sukaman yawa shys wlh, amma yaudai haka kawai nazo muyi fira" ummy tace "hmm wane commitment kuma bawani commitment wlh wahalalliyar hanyarda kuka d'ora kanku akaice dai take wahalardaku" kallonta murja tai tareda d'an kashemata ido alamar tai shuru tadaina wannan maganar, hakan yasa tai shuru amma badan tana tsoron yintaba,,,....

D'an murmushin gefen leb'e SUHAILA tai batareda tasake cewa komai ba, murja walie ce tafara janta fira harta sake sukacigaba da firar,,,....

Can suna cikin fira saita dubi ummy tace "wallahi ummy da'ace inada yanda zanyi nahana kaina cigaba da wannan sana'ar da nayi, ahalin yanzu sam bazan iya daina mualama da mazaba koda kuwa nace zanyi hakan saina kasa, a yanzu hk ma ina fuskantar wata matsala wlh",,....

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 11, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RUWAN DAREWhere stories live. Discover now