RUWAN DARE.....7--8

811 46 4
                                    

_*RUWAN DARE....*_🌷
  _a true life story_

_*By ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_

  _*Page 7~8*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Rayuwa tacigaba da tafiya inda SUHAILA suke cigaba da zana jarabawa,  IMRAN kuwa tinda tamasa wannan maganar basusake had'uwaba saidai a waya, hakan yabata damar cigaba da nunamasa k'auna saboda ya manta da maganarda tamasa ya d'auka kamar bada wata manufa tamasa wannan tambayarba,,,.....

Yau takasance Wednesday su SUHAILA nagida saboda yau basada exam hakama gobe saidai jibi Friday, zaune suke acikin d'akin momy ita da susi da sadiya fa'iza, ( sadiya da fa'iza sune k'awayen SUHAILA da susi waenda suka tashi atare school dinsu na boko d'aya kuma dik class dinsu d'aya ),,,....

SUHAILA tsaye take tana goye da yusrah daketa faman rigima tana kuka saboda su momy sunfita mak'ota, su susi kuwa a kwance suke kan gado suna latse latsen wayoyinsu, fa'iza ce tad'ago cikin fara'a tace "umm Allah sarki rayuwa kenan wataranama sai a wayi gari ba kai" dariya susi tai tace "hegiya antina da lahira kenan" su SUHAILA ma dariya sukai sai SUHAILA tace "wallahi kuwa shiyasa d'an adam yadinga sara yana duban bakin gatarinsa saboda idan yau kaine gobe bakai bane" fa'iza tace "wallahi yarintarmu ta primary da jss natina yaushene ma muka shiga ss section wai yau mune har muke zana jarabawan k'arshe" dariya sukai suduka susi tace "sady kintina satar madara da cin  bashin mama mai waina ta primary" tana fadar haka suka kwashe da dariya SUHAILA tace "ni da fa'iza mune sarakunan tsoro amma in aka sato mune kan gaba wajen ci" nanma suka k'ara kashewa da dariya,,,.....

Fa'iza ce tace "kai ai wallahi naso ace yanda muka taso dinnan mukai primary atare secondary atare ace har koleji ( University) ma atare zamuyi amma ina dady baya bari" shuruu sukai nantake annurin fuskokinsu ya sauya susi tace "wallahi nima naso hakan fa'iza inaso muma mucigaba da karatu amma dadyn mu bazai bariba shifa bama yason mukammala secondary batareda mun fitarda mazajenda zamu aura ba, ba yanda muka iya haka zamu hakura muyi biyayya kodon samun lada da kyakkyawan k'arshe",,,....

Tini yanayin fuskar SUHAILA yasauya fiye danasu susi, kallon susi tai sannan tace cikin bacin rai "wallahi nikam insha Allah sainacigaba da karatuna" kallon mamaki susi tabita dashi kan tace "SUHAILA mekike nufi kenan, yanzu amatsayinki na malama wacca zata auri malami zaki sab'awa ubangiji saboda kawai DUNIYA, tabdi jam lallai kuwa abunda kike fad'awa mutane karsuyi yau shine kike k'ok'arin aikatawa saboda duniyar banza, karfa ki manta kece kefad'in ayi biyayya ga iyaye aguji sab'a masu to yau kuma kece zaki sab'awa naki kuma akan banzar duniya wacca zaki tafi ki barta, shawarda zan baki kawai shine kibi ahankali wallahi idan dady bai aminceba karki yarda zuciya ta rud'eki duniya ta rud'eki kik'i bin umarninsa",,.....

Itadai SUHAILA kallonta kawai take harta gama maganarta batace uffan ba saima karajin b'acin rai da k'unar zuci takeji, suma su fa'iza shawarwari suka dinga bata da nasihohi akan karta bari zuciya da shaid'an la'anannen Allah yai nasara akanta, daga nan salon fira ta sauya sukacigaba da latse latsen wayarsu, itakam dik ji take komai bayamata dad'i danhaka kawai tafita tabarmasu d'akin saidai ta k'udiri niyar saitaje da kanta tasami dady ta rokesa yabarta tacigaba da karatunta tinda su teacher's dinsu har yanzu basuzo ba,,,,....

     _________________

Alhmdllh yau itace ranarda su SUHAILA suka kammala zana jarabawar WAEC saura NECO, kowannensu kagani sai murna da farinciki yake,, a can nahango su SUHAILA a kusa da office d'in principal suna d'aukan hotuna da wayoyi,,,.....

Sunjima sosai a school d'in suna bikin bidiri daga bisani sukai sallama saikuma Allah yasake had'asu a NECO sannan kowa ya watse,,,,......

            ******  *****

RUWAN DAREWhere stories live. Discover now