_*RUWAN DARE....*_🌷
_a true life story__*By ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183__*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_
_*Page 5~6*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Sannu ahankali siyasa sai gudana takeyi zab'e kuma sai k'aratowa yake, Alhmdllh kuma dadyn SUHAILA sai nasarori yake samu acikin tafiyarsa ta siyasa,,,.....
Yau takasance Monday bayan su SUHAILA sundawo daga school taje tasami mama a d'akinta, cikin sallama tashiga mama ta amsa mata sallamar sannan tazauna tareda gaisheda mama, cikin sakin fuska mama ta amsa tareda fad'in "SUHAILA andawo daga School" tace "Eh mama" mama tace "to sannunku da dawowa abincinku yana kitchen kuyi sauri kuci kuyi sallah kuyi shirin tafiya islamiyya ni zan wankemaku uniforms d'inku saboda banason kiyi letti y'ata" tai maganar cikin murmushi tana kallon fuskar SUHAILA,,,.....
SUHAILA tace "to mama" saikuma tad'anyi shuu, ganin haka yasa mama ta tabbatarda akwai abunda SUHAILA kesan fad'amata dan haka tagyara zamanta tajuyo tana fuskantarta cikin sakin fuska tace "y'ata menene mekikeso ne?" d'an murmushin gefen leb'e tai saboda tasan abunda zata fad'a babban abune agunta dama dik wani wanda yake acikin gidan gashi batasan ya iyayen nata zasu d'auki maganar ba saboda wannan maganar itace ta farko wacca tafara fad'arta acikin gidan, dikda sauran yayyenta ma sunso sufurtata amma saboda tsoro da fargaba yasa suka kasa fad'arta sukabarta a tsakaninsu batareda kowa yajita ba,,,......
Saida ta tattaro dikkanin nutsuwarta sannan tafara magana cikin in ina tace "am....am....mama dama....dama....inasone dan Allah mama ki taimakeni" saikuma tai shuu takasa k'arisawa, murmushi mama tai tagyara zamanta sannan tarik'o hanunta tace "y'ata ki kwantarda hankalinki ki fad'aman damuwarki kinji ko" a dik fad'in gidan bawani wanda SUHAILA kefad'awa damuwarta sai mama ko momy data haifeta bata fad'awa damuwarta, ganin haka yasa itakuma mama take k'ok'arin ganin ta warware mata matsalarta a dik lokacinda tazomata da'ita,,,".....
Numfashi ta sauke sannan ta sadda kanta k'asa tace "mama inaso dan Allah kirok'aman dady idan na kammala secondary School dina yabarni nacigaba da karatuna, mama i want to be a medical doctor so please mama kitaimakaman domin ganin nacimma burina, inada burin taimakon al'umma sannan inada burin taimakon y'ay'a mata marasa gata da k'ananun yara, please...!!! Mama help me to achieve my BURI NA" shuru mama tai tana kallon SUHAILA harta k'arasa abunda take fad'a,,,....
Kawarda fuskarta tai daga kallonta sannan tace,...
"SUHAILA kin bijiro da babban al'amari acikin gidannan dikda nasan tabbas ba likita inma akwai abunda yafi likita wahalar karatu to zaki iya karantarsa saboda i know ho is u, but the problem is mahaifinki, kinfi kowa sanin waye shi, sam baya magana biyu sannan kema kinsan bazai taba barinki kije makaratar koleji (University) ba, SUHAILA kiyi gaggawar cire wannan zancen daga zuciyarki saboda kema kinsan ba abubane mai yiwuwaba" kwallah ne taga suna zuba daga idanuwan SUHAILA bakinta har makyarkyata yake saboda k'unar zuci,,,....
Janyota tai ta rungume tafara rarrashi tana fad'in "No no my dear stop crying please, karki saka wannan abun a ranki yazo yadinga damunki a zuciya bakekad'ai bace da akafara yiwa hakan a cikin gidannan so menene nadamuwa, kawai kiyi addu'ar Allah yabaku zaman lafiya ke da IMRAN yak'ara had'a kawunanku a gu d'aya, tarin iliminda Allah yabaki kuma kiyi k'ok'arin zubashi wa 'yay'anda zaku haifa, rufin asirin y'a mace d'akin mijinta bawani karatun boko ba, ita aljannah da lada a ko'ina ana samunta kema kiyi k'ok'ari kinemi taki a gidan mijinki kinji ko y'ata" tagyad'a kai alamar Eh,,,....
Share kwallan da suka b'ata mata fuska tai sannan ta tashi tafice zuwa d'akinsu, tin daga wannan lokacin SUHAILA batasake yin wannan maganarba saidai fa har yanzu wannan burin nata nacigaba da karatu yana nan zaune daram acikin zuciyarta musamman yanzu datake k'ara samun lambobin yabo daga manyan gomnati da malamai,,,....