_*RUWAN DARE....*_🌷
_a true life story__*By ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183__*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_
_*Page 11~12*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Amincewar dady yabama kowa na gidansu SUHAILA mamaki wasu kuma farinciki suke suna fad'in "lallai tabbas SUHAILA 'yar sa'a ce da Saarta tazo duniya" itadai susi bata damuba tasan in Allah yanufi data cigaba da karatu koda a gidan mijinta ne zata cigaba,,,.....
__________________
Rayuwa tacigaba da tafiya inda cikin ikon ubangiji jarabawan su SUHAILA tafito donhaka ta karb'i kud'i gun dady sukaje ita susi dasu fa'iza suka dubo result d'in, woww masha Allah cikin ikon ubangiji kuwa abunda tai zato shine ya faru, sakamakon yai kyau sosai credit 5 A uku sai pass 1, hakama su susi tasu tai kyau amma bakamar ta SUHAILA ba,,,,.....
Cikin farinciki suka dawo gida da murna, da marance bayan dady yadawo daga office sukaje suka kaimasa result d'in, shima yai murna yai farinciki sosai dan hadda kyautar kud'i yamasu saboda farinciki sannan yakarbi result d'in suka fita,,,......
Bayan sunkoma ciki nanta d'auki wayarta takira habibinta kira d'aya ana biyu ya d'aga cikin rangad'a mata sallama "Assalamu Alaiki my Noorul Qalb" wata iriyar murmushi tai mai sauti wacca ta bayyanarda zahirin kyanta afili wishiryarta ta bayyana dimples d'inta ya lotsa tace "waalaikasalam ya HABIBI DA'IMAN, inafatar kawuni cikin k'oshin lafiya da farinciki kamar yanda nima nawuni" gyara kwanciyarsa yai izuwa rub da ciki cikin tsantsar nishad'i yace "Alhmdllh my noor kamar kinsan kina raina inata zamcenki acikin zuciyata saikuma gashi kin kirani yanzu ina jin zazzak'ar muryarki wacca tafi kanari dad'in sauraro",,,,,.....
Wata iriyar yar dariya tai tace "Allah ko" yace "sosai ma kuwa, to ya akayine yau zaki shigo islamiyya?" saitace "amm.....gsky shigowata babu tabbas" dasauri yatashi zaune yace "meyasa ohh....!!! Please inafa kishirwar ganinki wlh i really miss u much wlh" murmushi tai tace "nima haka amma tsabar farincikinda nake ciki yasa k'ila bazaibarni nashigo ba" sake gyara zamansa yai sannan yace "farinciki? farincikin me my noor fad'aman naji menene yasakaki farinciki",,,,......
Pillon dake kusa da'ita ta janyo ta rungume ta langwab'arda kanta izuwa kan shoulder d'inta sannan tace "umm....yau munje munyo printing d'in exam dinmu na NECO kuma result d'in yai kyau sosai harma dady yamun kyauta saboda jin dad'in yanda result d'in yafito"......."Woww am so so happy my noor naji dad'i sosai wlh nai farinciki Allah i sanya alkhairi" cikin jin dad'i da tsintsar farinciki tace "ameeen yh rabbil izzati wal k'uwa, Thanks my habibi nagode sosai",,,.....
Sake kwanciya yai yajanyo pillow ya rungume cikin kasalalliyar murya mai rauni kamar maijin bacci yace "yanzukam angama karatu saura aure ko" wani irin diiimmm......!!! taji k'irjinta yai harsaida takai hanunta ta dafe, sai tai y'ar dariya kawai batareda tace komaiba, cigaba yai da magana "my noor ahalin yanzu ba abunda nake bukata sama danaga na mallakeki a matsayin matata, ahalin yanzu ba abunda yake agabana face auren ki, namaki dikkannin wani tanadi domin jin kinfi kowa Saar miji acikin mata nakuma yi maki shirin tsintsar farinciki da k'auna mai tsabta acikin rayuwar aurenmu, please SUHAILA kema kiman alk'awarin zaki kula dani tamkar yanda uwa ke kula da d'anta" shuru tai tana sauraronsa, yanayin yanda yake maganar cikin murya mai taushi wacca take kashe mata dikkanin wani kuzari na jikinta,,,.....
Ahankali tace cikin kasalalliyar murya "insha Allah IMRAN zaka sameni a yanda kakeda muradin matarka ta kasance, namaka alk'awarin baka cikakkiyar kulawa dakuma mallaka maka tarin soyayyata wacca take a cike da kulawa, zan tarairayeka tamkar kwai tayanda zaka manta da kai marayane zan baka dikkanin farinciki arayuwar aurenmu insha Allah" wani irin sanyi yaji ya ratsa sassan jikinsa harsaida ya sauke nannauyan ajiyan zuciya sannan yai murmushi yace "I really love mu more than yanda kike tinani Allah i nunaman ranarda aka kawoki gidana acikin d'akina amatsayi matata uwar y'ay'ana",,....