_*RUWAN DARE.....*_🌷
_a true life story__*BY ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183__*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_
_*Page 23~24*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Sannu ahankali SUHAILA tafara rayuwar makaranta saidai wannan karon kam batai saurin sabawa da room mate d'inta ba sab'anin wancan lokacin da tai saurin sabo da antynta farida,
Kimanin satinta d'aya kacal suka fara karatu gadam gadam kasancewar wannan karon u.j.1 ne shys karatun yasha bambam dana da dayake matric ne,,,....Gaba d'aya ta mayarda hankalinta akan karatu baruwanta dawani malami ko wasu k'awaye dataje class bayan gaisuwa ba abunda ke had'ata da kowa saikuwa in anbasu assignment ko presentation shine kawai ke had'ata da mutane,,,,.....
Yanayin basirarda Allah yamata da farinjini acikin al'umma shys nantake tashiga ran mutane musamman y'an uwanta student gakuma taimakonda takeyiwa waenda basuda iliminda yakai nata, kamar d'an lesson haka kokuma su cimmata a hostel tadinga koyardasu abunda basu ganeba, nantake kowa yai na am da'ita akan tazama class monitor nasu, malamai ma sunyi na am dahakan saboda kowa yasan SUHAILA nada baiwa wacca bakowanne dalibi keda ita ba, hakan yasa suka mata suna da gifted dan ko malami idan baiyi da gaskeba zata iya kaishi bango da tambayoyi kuma kai bazaka taba iya kadataba wajen yimata tambayoyi batareda tabaka amsoshinsu ba,,,....
'yammata dayawa nakawomata gayyatar kawance amma ba wacca takula karatunta kawai take, hakama samarin school d'in y'an 200level da y'an 400level, wasuma suce suyi soyayya wasu kuma kawance wasu kuma wai dagaske suke sonta suna sone su aureta, itakuwa dikansu kallon mayaudara take masu saboda a yanzu dik maza kallo d'aya take masu ma'ana mayaudara kuma maciya amana, wannan dalilin yasa take masu wulakanci dik wanda yakawomata farmakin so nantake take watsesa tai gaba abunta,,,,......
Saidaifa dawata a k'asa saboda Mr. Zam baifice arayuwar SUHAILA gaba d'aya ba, acikin kusantarta dayai yabarmata wani rikitaccen al'amari wanda yafara aiki akanta yanzu, a dik lokacinda ta kwanta bacci saitai farmakin gatanan wani namiji yana kusantarta, bayan ta farka kuma sai wata iriyar matsananciyar sha'awa ta rufeta,,,.....
Wannan bakon al'amarin shine yake damunta saboda tinda take bata taba fad'awa irinsaba buk'atar namiji acikin gaggawa dakuma jin matsananciyar sha'awa tana fizganta, saidai har yanzu takasa fad'awa kowa saboda tana tsoro, haka takeshan fama taita matse matsen cinyoyi tana hard'e k'afafuwa tana furzarda numfashi tareda sauke nannauyan ajiyan zuciya,,,....
Tarasa ya zatayi saboda matsalar tana damunta,
Ahaka suka cigaba da karatu batareda tasanarda kowa ba, room mate d'inta kuwa nusiba abunda ke had'asu kawai bacci saboda batacika zamaba, wani lokacin idan tafita tin 8am sai lokacin rufe gate yayi take ganin tadawo wata dalleliyar mota ce zata mayar da'ita, ko ayanayin shigarta dataga tanayi tasan ba kalar mu'amalarta bace shys bata kulata sosai daga gaisuwa saiko inzataci abinci takan kirata suci atare sai kuma 'yar fira wacca bawani dadewa sukeba,,,,.....Kamar kullum yauma zaune take akan floor d'in wani clss around 6pm kasancewar yau weekend ne tagaji da zama acikin d'aki shine tafito tadan sha iska tinda bakowa tasaniba, kallon yanayin school d'in take yanda 'yammata ke shigarsu irinta arna waisu adole weekend ne dole sushakata kuma awaje ba acikin hostel ba, wata wandon jeans ne matsattse sai y'ar riga wacca ko dogon motsi tai za'a iya hango cibiyarta sai d'an mayafi asaka a rufe suma shima transparent ne bakomai yarufe ba, wata kuma d'an sket ne tasaka wanda yamatseta ya bayyanarda al'aurarta a fili sai 'yar riga mitsitsiya sai y'ar hula, wata kuma sket da riga ne tasaka na atamfa amma d'inkin yamatseta sosai sai d'an mayafi wanda dashi gwanda ma babu,,,.....