RUWAN DARE.....21--22

578 35 8
                                    

_*RUWAN DARE.....*_🌷
  _a true life story_

_*BY ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_

  _*Page 21~22*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Birnin kebbi suka fara sauka gidansu k'awar susi wacca suke school d'aya kuma department d'aya, bayan sungaisa da ummanta sannan suka shiga ciki ta shirya sannan suka hau a dai daita sahu suka wuce Carpe Center,,,....

Sunjima sosai acan saboda akwai mutane sosai dasukazo suma dubatasu danhaka ma saida sukabi layi, sannu ahankali har suka kai sannan aka fara dubawa latipa k'awar susi,,,.....

Alhmdllh tasamu nasara itakam saura su SUHAILA, bayan anduba mata sai aka dubawa SUHAILA, itama cikin nasara tasamu saidai Mark's d'inta bazai kaita U.J 1 a F.B.U.K saidai wata state University dake Aleioro L/government anan cikin kebbi state,
Dikansu basuji dad'in hakan ba musamman susi saboda taso 'yar uwarta tai karatu a babbar jami'ar F.B.U.K saboda tasamu karatu mai kyau, sab'anin ita SUHAILA da damuwarta iya fuska ta tsaya saboda a yanzu bataso tacigaba da karatu a F.B.U.K tafison koda diploma ce tai datasake komawa a can,,,.....

Bayan anduba mata aka dubawa susi sukam dik Alhmdllh dama numbern jamb kawai suke bukata ba Mark's ba, daga nan suka hau motar tasha suka wuce kalgo L/government school dinsu SUHAILA,,,....

12pm suka isa kalgo a bakin hanya aka saukesu kasancewar school d'in ba can cikin kalgo takeba akan hanya take,
Bayan ansaukesu saisuka taka da kafa suka k'arisa School d'in, saida taje suka gaggaisa da k'awayenta sannan suka wuce gunda aka manna masu result dinsu,,.....

Ahankali tafara duba sunanta amma k'irjinta sai dukan dukan tara tara yake saboda tsabar fargaba, can k'asa tahango sunanta sannan tafara duba average d'inta da Mark's d'inda tasamu, abunda idanuwanta yaganemata ne yasakata tafara jin jiri na d'ibanta ma'ana dai sam babu nasara tafadi bataci ba dan abunda ake bukata ga kowane dalibi yasamu wanda zaiwuce U.J shine 2.8 amma ita abunda tasamu 2.2 kunga ko 2.7 bata kaiba bare adan samu ayi gyara,,,.....

Wasu zafafan kwallah ne taji sunfara bin fuskarta waenda batamasan suna zubaba saboda tsabar mamaki da tsintsar tashin hankali, a iya saninta dik wani Question da ake masu takanyi k'ok'arin amsar fiye da rabinsa wani ma dika take amsashi wanda tai yak'inin koda batafi kowa Mark's ba to zata fito acikin y'an sahun farko amma yanzu gashi ko sahun na uku bata aciki bare sahun farko, to ina alk'awarinda Mr. Zam yamata ina alk'awarinda yamata, tabbas yau ta gazgata maganar aunty farida datace Mr. Zam k'arya yake mata kawai yayi amfani da wannan damar ne domin cimma burinsa agareta yau gashi ta tabbatar,
Tana cikin tinani saitaji su susi na kwallah mata kira bata ankaraba kawai taji tai sulu sai k'asa, diiipp kakeji tafadi,,,.....

Sam batasan inda takeba dan ko numfashi batayi ashe sumace tai, farkawarda tai kawai saita ganta akan gadon asibiti lokacin kuma har 11pm tayi, ahankali tafara k'ok'arin tashi a zaune sai mama tazo ta taimaka mata tana fad'in "sannu SUHAILA kin farka ashe to Alhmdllh susi jeki ki kirawo dadyn ku yana waje" cikin sauri kuwa susi tafita takirasa saigashi yashigo tareda doctor,,,....

Sannu suka dinga mata sannan doctor yafara dubata, bayan yagama ne yayiwa su dady bayanin abunda ke damunta, tsabar damuwarda take shigane yasa take ramewa sosai yanzu kuma bugawarda zuciyarta tadingayi sosai shine yasakata faduwa hartagai ga yin suma, sannan yanzu dole adinga bata cikekkiyar kulawa saboda tadaina shiga damuwa, kamar tadinga yawan fara'a dai, wannan shine abunda zaisa tagujewa kamuwa da cutar ciwon zuciya, godiya dady yamasa sannan yarubuta injections d'inda zaamata dakuma medicine's d'inda za'a siyo tadinga sha, daganan yamasu sallama yawuce,,,....

RUWAN DAREWhere stories live. Discover now