RUWAN DARE....9--10

808 31 0
                                    

_*RUWAN DARE....*_🌷
  _a true life story_

_*By ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_

  _*Page 9~10*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Ahankali aka fara shirin bikin sallah, tini su SUHAILA suka karb'o d'inkunansu na sallah dan wannan karon har kala set shida dady yamasu na kayan sallah ga mak'udan kud'i daya basu suyi dik abinda sukeso,,,.....

Saura kwana uku sallah dady yabama ya musty da ya hameed mota da mak'udan kud'i yace sudauki su SUHAILA suje central market su siyo takalma da jakukuna da sarka da awarwo dadai sauran kayan kyalli na y'ay'a mata, haka kuwa akayi su SUHAILA sai murna ake ana tsalle, haka suka shirya kowa da kowa harda yusrah da ake goyo saida momy tashiryamata tace itama aje da'ita a zab'ar mata nata kayan k'awar,,,.....

Tin 10am suka iso kasuwa amma har kusan 1pm basu gama siyayya ba sai yawo suke acikin kasuwa shago shago, saida su yaya musty sukace wallahi zasu tafi su barsu sannanfa dole suka fito kowa da k'atuwar leda acike sannan suka wucewa,,,......

Ranar daren sallah kuwa tin 10am suka fara aiki, k'aton sa dady ya yankamasu aka rabawa mak'ota rabi rabin kuma aka fara gyaransa, sai kusan 5pm sannan suka kammala komai na aiki nan sukai wanka sannan suka kwanta domin su huta kan lokacin shan ruwa yayi,,,......

Ranar dai basu iyayin bacci ba saida suka tabbatarda anga wata nanfa murna ta kacame acikin gida gobe sallah gobe sallah, haka kuwa washe gari takasance ranar sallah,,,".....

Around 8pm dot kowa ya shirya cikin shiga irinta alfarma nan sababbin driver's d'in dady suka fito da sababbin motocin dady da escort d'insa, mota d'aya dady yashiga tareda momy da mama da yusrah sai d'aya kuma su SUHAILA sai d'ayar kuma y'ay'a musty ya hameed da yara k'anana, sai kuma sauran motoci uku dasuka masu rakiya saboda yanzu dik inda dady zaije da escort d'insa hatta k'ofar gidan yanzu tsaronta ake saikanemi izini sannan za'a barka kashiga,,,.....

Bayan anyi sallar eid dady yafito suka dinga gaggaisawa da mutane waenda basu sami ganinsaba suka masa Allah kyauta i sanya alkhairi yanzu suka masa, nanfa dady yabude bakin aljihunsa yafara rarraba kud'i ga mutane da tsofaffi, saida suka kai har kusan 10:30 su SUHAILA suka gaji suka k'ufula sannan fa dady yazo suka wuce gida,,,"....

Bayan sundawo gida aka baje babban parlon dady wanda yasha sabon gyara hadda wallpapers ko'ina ansaka masa sababbin kujeri kasancewar komai nagidan saida aka sauyasa aka saka sabo, hatta bed's d'in dakunan su SUHAILA sababbi ne suma kuma ansaka masu wallpaper a d'akinsu, a yau inkagansu abun gwanin birgewa, tindaga kan mimi har izuwa su ya Aysha dasuke manyan yayye a yanzu kaya iri d'aya suka saka, wani tsadajjen sweezzless ne light blue and white colour suka saka kowacce anmata d'inkin sket da riga sai sarkokinsu da awarwaro mai tsadar gaske, sunyi kyau sosai musamman tauraruwar tamu wacca ita dama can koda batai make--up ba tanada kyanta bare kuma gashi tayi, haka tadawo tamkar taurarur zarah acikin sauran taurari dake haske acikin sararin samaniya,,,.....

Abunda dady yafi so kenan yagansa cikin iyalinsa saboda dady dama can irin mutanen nanne masu son su zauna sukad'ai da iyalinsu batareda wani yakusantosu ba dan ko Amina dandai tana jininsa ce, ammafa kuma dikda hakan baihanasa son yawan muamala da mutane ba kawai dai shi yanayin rayuwarsa ne haka, bare kunsanfa d'an boko ne dole yaji irin hakan,,,,.....

Maza ma sudika kaya iri d'aya suka saka kasancewar mata sunfisu yawa, shadda ce gizna mai tsadar gaske hadda dady saidai shi tashi colour daban da tasu, haka suka hadu atare da dady dasu momy sukaci abincin sallah cikin tsintsar farinciki da jindadi, bayan sungama itadai SUHAILA tawuce d'akinsu tai bacci,,,".....

RUWAN DAREWhere stories live. Discover now