RUWAN DARE.....25--26

658 42 3
                                    

_*RUWAN DARE.....*_🌷
  _a true life story_

_*BY ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_

  _*Page 25~26*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Suna isa tafad'a kan gado tafara rera kuka tamkar k'aramar yarinya, nasifa matsowa tai kusa da'ita sannan takai hannayenta ta tallafo fuskarta da tai faca faca da kwallah dogon hancin nan yayi jazir dashi hakama y'an lab'banta sunyi jazir abunka da farar fata kamar Aufana 😜 Lolz,,,.....

Cikin muryar tausayi tashare mata kwallah sannan tafara mata magana "am sorry sister ki yafeman nakaiki inda baki saba zuwa ba ko am sorry forgive me please" d'agowa da fuskarta tai tana kallonta da dara daran idanuwanta waenda suka saiya kala izuwa ja saboda kukanda tai, girgizamata kai take tana fad'in "kokadan sister bake kika b'ata man raiba dikda dai banji dad'in inda kika kainiba kuma bantaba tinanin Allah zaikai kafana canba kuma banji dad'in kaini can da kikaiba amma sam wannan bashine yasakani nake kuka ba" saikuma tai shuru,,,.....

Cikin mamaki fuskarta d'auke da mamaki tace "to menene yasakaki kuka?" kallonta tai sannan tajuya mata baya idanuwanta na zubda kwallan bak'in ciki tace "wannan abune daya faru kusan shekara d'aya yanzu kuma zan iya kiransa da k'addara haka kuma sirrina ne wanda bakowa zan iya fad'awa shiba" b'ata fuska nasifa tai sannan ta tadawo dai dai fuskarta suna fuskantar juna tamkar zata zubda kwallah tace "yanzu nafahimci matsayinda kika ajiyeni SUHAILA, kina nufin kenan ni ban cancanci naji sirrinki ba kokuma banacikin waenda zaki iya fad'awa sirrinki, shikenan bakomai saidai ni kisani tamkar y'ar uwarta ta jini nadaukeki dikda kuwa kink'i ki saki jikinki dani kuma dikda bawani dad'ewa da sanin juna ba mukayi amma nidai tamkar y'ar uwata uwa d'aya uba d'aya nadaukeki"  saita juya fuskarta alamar ranta ya baci sosai,,,,......

A rayuwar SUHAILA dakuma yanayin mu'amalarta sam bata kaunar ran wani yabaci saboda ita bata kaunar tabatawa wani rai, hakan yasa nantake taji ba dad'i nantake kuma taji zuciyarta ta amince da nasifa dikda talura halayyarsu ba d'aya ba amma dai zata d'auketa amatsayi 'yar uwa tinda yanzu batasan kowa ba a school d'in sai ita gashi atare suke rayuwa a d'aki d'aya corse dinsu ne kawai ba d'aya ba, matsowa tai kusa da'ita tareda dafa shoulder d'inta tace "kiyi hakuri sister bahaka bane nima wlh tamkar 'yar uwata haka nakejinki, wannan abun da naboyeshi nakasa fad'awa kowa shi abune daya shafi rayuwata wanda bakowa yasaniba harma da iyayena sai mutum d'aya wacca itama dolece tasaka harta sani"  saikuma tai shuru,,,....

Hmm.....!!! ta sauke nannauyan ajiyan zuciya sannan tacigaba "saikuma ke yanzu dazan fad'awa kema kuma inason dan Allah kirik'eman alk'awari karki taba bayyana wannan sirrin nawa"....

Murmushi nasifa tai sannan takad'a mata kai tareda fad'in "I promise to u insha Allah bawanda zaiji my sister" murmushin jin dad'i tai sannan tacigaba,
"kamin nafara karatu anan saida nafara matric a F.U.B.K dake kalgo l/government, kuma abunda yafaru dani acan ne yafaru dani" nantakwashe labarin komai tabata har izuwa faduwarta a exam sannan tadora da "tinda nabar School d'in bansake ganin Mr. Zam a idona ba sai yau dana gansa a wannan wajen dakika kaini, ganinsa danayine yatina man da wannan bak'in cikin daya kunsaman yabarni dashi wanda har nabar duniya bazan taba mantawa dashiba, Ibrahim muazzam yacuceni ya b'ata man rayuwa yarabani da abunda kowacce mace take tinkaho dashi dake alfahari dashi wato budurci, dad'i da k'ari kuma tin bayanda wannan abun yafaru dani banajin wata matsala a tattare dani sai yanzu, kusan kullum nakwanta bacci sainayi mafarkin ga wani nan yana kusantata ma'ana yana saduwa dani, nashiga damuwa sosai saboda a yanzu ina buk'atar namiji sosai a kusa dani gashi kuma IMRAN yagujeni yanzu ko nemana yadainayi kuma idan nakirasa bana samunsa, inason karatuna nasifa kuma inason IMRAN sonda bazan taba yiwa wani d'a namijiba a rayuwata, narasa yanda zanyi da rayuwata gashi kuma nakasa sanarda iyayena halinda nake ciki"....

RUWAN DAREWhere stories live. Discover now