RUWAN DARE.....27--28

660 30 6
                                    

_*RUWAN DARE.....*_🌷
  _a true life story_

_*BY ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_

  _*Page 27~28*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Tinda tashiga motar tagaidashi batasake kallon inda yakeba saima juya fuskarta tai tana kallon gabanta, shikuwa sai kallonta yake time by time yana murmushi,,,....

Kasa hak'uri dai yai saiyamata magana "my beauty Queen kinyi kyau wlh, u look so cute my angel"  murmushi tai wanda yake k'ara bayyanarda kyanta a fili tace "Uhm nagode"  saiyacigaba da magana "tin ranarda na sanyaki a idanuwana naji k'aunarki ta soki gadon zuciyata, naji kin kwanta man a rai, naji inason nakasance atare dake, beauty queen matuk'ar kika bani had'in kai kika amince dani nikuma namaki alk'awari zan maidaki tamkar sarauniya acikin mata, zan maidaki kidawo tamkar baturiyar asali farar fata, wannan kyan naki da kyakkyawar surar nan taki zan maidata tadawo tamkar ta mage, SUHAILA kibani had'in kai nasanyaki acikin daularda baki taba tsintsar kanki aciki ba"  itadai shuru kawai tai tana sauraronsa harya gama sannan tace,.

"Indai soyayyata kake buk'ata nadad'e da baka ita na dad'e da amincewa da tayin soyayyarka, saboda haka kadaina rok'ona haka ya'isa tinda dai kasami abunda kake buk'ata"  shuru yai yana kallonta saboda yafahimci sam bata fahimci inda shi yadosa ba, a yanayinta ma ya tabbatarmasa da SUHAILA she's too young, k'aramar yarinya ce barikince kawai tashigo amma badan tasan kanta ba, fahimtar haka yasa yashare zancen a zuciyarsa yana fadin "hhhh irin wannan kalar nakeso wacca ni zan koyamata komai nad'ora abata kan hanya",,,.....

Da wannan tinanin suka isa a bakin wani katafaren hotel mai shegen kyan gaske, bayan gateman yawangare masa gate yashiga tareda kwasan gaisuwa sannan yai parking na motarsa yafita yabarta zaune aciki, zagayowa yai yabude mata murfi tareda fadin "my beauty queen zaki iya fitowa" ahankali kuwa tasakko santaleliyar k'afarta tafito yanamata murmushi itama tana mayarmasa sannan yarufe motar yamata key,,,.....

Atare suka jera suna tafiya idan ka hangosu zakace jikarsa ce ita saboda yanda tsufa ya bayyanarmasa dikda kuwa yanacikin wadata kuma yana kula da kansa ta hanyar kyale kyale na zamani irin na samari,
Kamar ance ta daga kanta aikuwa tana dagawa saitaga sunanda aka rubuta akan k'ofar shiga ciki nantake kirjinta yafara dukan tara tara saboda tinda uwarta ta haifeta bata taba zuwa hotel ba saida tahangesa daga and nesa kan hanya amma bata taba shiga ba,,,".....

Bayan sunshiga ciki saiya biya kudi sannan yai cike ciken wasu takardu sannan aka basa Key's din room dinda zasu zauna, bayan angama komai sannan yariko hanunta suka wuce,.
Room no.131 shine wanda zasu zauna aciki donhaka kai tsaye sama suka haura izuwa room din,,....

Bayan sun isa sannan yasaka Key's yabude k'ofar suka shiga, daki daya ne wanda yake dauke da gado daya da toilet da dan karamin fridge sai yan sauran tarkacen kayan d'aki, kan wata kujera tasamu ta zauna tareda rungume hannayenta, shima kan kujerar ya zauna a kusa daita yana kallonta yana murmushi,
Cikin murmushi yace "to my beauty me zamu fara wanka ko cin abinci?" kallonsa tai da mamaki sannan tace "Nifa nadauka wani gu daban zamuje like wurin hutawa musha ice cream sannan muje super market da dai sauransu, saikuma naga kazo damu nan"  murmushi yamata kawai baice komaiba saiya mike tsaye yaje ya danna wata kararrawa sannan yashige toilet abunsa, kamar 15mnts da danna kararrawa saitaji anfara norking din k'ofa, tsoro ne yakamata danhaka takasa tashi tabude k'ofar jikinta sai kyarma yake, cigaba akai da norking amma takasa tashi tabude k'ofar, ana cikin haka saigashi yafito daga toilet din d'aure da towel a k'ugunsa gakuma wani k'arami a hanunsa yana tsane jikinsa dashi, shi yaje yabude k'ofar saitaga wani yaro yashigo ya ajiye faranti cike da abinci kala kala,,,....

RUWAN DAREWhere stories live. Discover now