_*RUWAN DARE....*_🌷
_a true life story__*By ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183__*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_
_*Page 3~4*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Sannu ahankali mai a dai--daita sahun yake tafiya dasu har suka iso gidan yaya hafsat nan suka sakko sannan suka bud'e k'ofar shiga suka k'arasa daga ciki,,,.....
Cikin sallama suka shiga parlor amma basuga kowaba danhaka SUHAILA tafara kwallawa ya hafsat kira "yaya hafsat....ya hafsat" ya hafsat dake cikin kitchen jin kiranda ake kwala mata yasa tafito tana fad'in "Na am gani anan" k'arasowa tai cikin parlon saitagansu zaune mimi harta kwanta kan kujera, cikin girmamawa SUHAILA tace "yaya hafsat barka da wuni" cikin fara'a da sakin fuska da farincikin ganin y'an uwanta ta zauna akan d'ayar kujera tana fad'in "barka dai y'ammatan momy kune afate ashe" SUHAILA tace Eh, nan sukafara fira irinta yaya da k'anwarta,,.....
Suna cikin fira SUHAILA tace "ya hafsat inasu Nasreen hala naji gidan tsiit" dariya tai tace "dadyn su yafita dasu sunje sugaida hajiyar sa sannan sudan zaga dangi kinsan idan muntafi kuma sai anganmu" SUHAILA tai dariya tace "hakane kam gwanda idan kunzo kud'an dinga shiga dangi kuna gaggaisawa da iyaye da yayye da kannai",,,,......
Kitchen ya hafsat takoma tanacewa SUHAILA "zo kitayani aiki dama inaneman wanda zai tayani mai aikina itama tawuce k'auyensu taga iyayenta kan mutashi wucewa" ba musu kuwa SUHAILA ta tashi tacire hijab d'inta tabi bayanta suka k'arasa aikin atare, suna cikin aiki sai SUHAILA tace "yaya dady fa siyasa zai fara harma yacike form ya biya kud'i" tai maganar cikin dariya, cikin mamaki hafsat tace "siyasa fa kikace" SUHAILA tace "kwarai kuwa wallahi muma d'azu mama ke fad'amana kinsan halin dady baya saurin fadar abu sai komai ya kamkama" hafsat tace "kai amma wallahi nai farinciki sosai Allah ubangiji yabasu nasara yakuma tsare manashi daga sharrin mak'iya da mahassada" suka amsa da ameen hafsat tace "ashe bikinku bikin dad'i za'ayi idan lokaci yai koda bikinku zaizo Naira ta zaunawa dady yak'ara zama hamshak'i zakuji dad'i yara sa'arku tafi tamu" dariya SUHAILA ta kyalkyale daita tana fad'in "kai ya hafsat bakida dama wallahi ai kan ayi namu nasu yaya Aysha za'afara kinga kuwa sune zasu fara jin dad'i kan lokaci yazo" itama cikin dariya tace "hakane kam amma ai kilama saikunfisu, yawwa wai nikam ina Mu'allim dinki habibin Ya Shaikh Imran angon SUHAILA",,,.....
Murmushi SUHAILA tai cikin yanayin kunya sannan tace "yanzu dazamo gidanki muka hadu dashi shima yatara mana abun hawa kuma yabiya mana kud'i"........"Allah sarki Allah yabar dank'on k'auna, gaskiya SUHAILA kinyi dacen miji wallahi gashi malami kuma ustazu gashi kuma yanada aikinsa gakuma tarin k'aunarda yake nunamaki dama dik wani wanda yake d'an uwanki gashi da tsintsar ladabi wallahi idan yaganni har k'asa yake durk'usawa yagaidani, dan Allah SUHAILA kizamemasa y'a kimasa biyayya kinji ko" tai murmushi tace "to insha Allah zanyi ya hafsat" tai murmushi tace "Allah yak'ara had'a kawunanku" suka amsa da ameeen,,,....
Saida sukai sallan azahar sukaci abinci sannan sukamata sallama suka wuce gida kasancewar 3pm suke zuwa islamiyya,,,.....
Koda suka isa gida saisuka tadda k'ofar gidan cike da manya manyan motoci dalla dalla na alfarma wasu anmanna masu hotunan yan takara na jam'iyar APC mai tambarin tsintsiya,,,.....
_*SHIN WACECE ITA.......?*_
SUHAILA AHMAD ZURU shine cikakken sunanta haifaffiyar k'asar Kebbi state acikin k'aramar hukumar ZURU,,,.....
SUHAILA kyakkyawace sosai dan dik acikin y'an gidansu tafi kowa kyau dikda suduka y'an gidansu kamanninsu d'aya saidai wasu farare wasu kuma bak'ak'e ammadai daka gansu kasan jini d'aya ne, mahaifinsu Barrister AHMAD JOSEPH da matansa biyu hajiya safina da hajiya Hauwa'u, SUHAILA su bakwai ne agun mahaifiyarsu hajiya safina, sai hajiya hauwa'u itama tanada yaya bakwai kasancewar kusan atattare suke haihuwa shiyasa mafi yawan yayansu suke tasowa kamar tagwaye bibbiyu ko uku uku,,,.....