_*RUWAN DARE......*_🌷
_a true life story__*BY ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183__*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_
_*Page 33~34*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
*****Kimanin kwana shida takwashe tana fama da zazzab'i, idan tasha magani saiya kwanta bayan kwana biyu kuma saiya sake tashi, gashi tanashan wahala sosai,,,.....
A waennan kwanakin dai tafi wahala sosai kasancewar nasifa batanan tanacan wajen yawonta shys batasan ciwon yakaita kwance ba, gashi su murja walie bawani yawan shigowa suke room d'in ba shys suma basusan batada lafiya ba bare suzo su taimaka mata,,,.....
Yauma kamar kullum kwance take sai kwallah ke zuba daga idanuwanta saboda zafin ciwonda takeji gashi kanta sai ciwo yake mata gakuma amanda takeyi wanda shine yake k'ara galabaitar da ita,,,.....
Tana a kwance kawai tasakejin wani amai yazo mata aikuwa ba shiri tamike tsaye takama hanyar toilet, saidai kan tak'arisa har aman yazo yafara zuba acikin d'akin sannan tak'arisa toilet tacigaba da yinsa,
Kamar daga sama saiga nasifa tadawo kasancewar weekend yak'are gobe Monday may be shys tadawo sbd ita dik iskancinta tana kula da karatinta saboda shine jigon dawowarsu k'asar Kebbi state ita da iyayenta,,,.....Tana shigowa saitaga bataga SUHAILA ba, jin kakarin amai daga toilet ya tabbatarmata da itace acikin toilet d'in, ajiye kayanda tashigo dasu tai dasauri tabita acikin toilet d'in,,,"....
Koda taisa kuwa tana zaune dab'as acikin toilet d'in sai kwara amai take tamkar zata amayarda abunda ke cikinta, cikin tausayi ta kamata tariketa tana mata sannu, saida tak'are aman sannan tadibo ruwa tawanke mata jikinta tabata ta kuskure bakinta sannan ta taimaka mata suka fito sannan ta kwanta kan bed d'inta,,,.....
Nasifa kuwa zagewa tai tagyara gunda tai amai acikin d'aki sannan tashiga toilet shima tawankesa tass ta tsabtace koina da koina sannan tafito, bayan tagama saita d'akko wani tirare mai dadin gaske tafeshe d'akin da toilet,,,.....
Tana acikin fesawa sai SUHAILA tarufe hancinta da sauri tana fad'in "haba nasifa wannan wane irin tirarene kika saka mara dad'i mai wari" mamakine ya bayyana tsintsa a fuskar nasifa, SUHAILA itace jigo wajen fad'in nasifa tadinga siyomasu wannan tiraren saboda tanasansa yanada dad'i sosai amma kuma yanzu wai itace mai fad'in bashida dad'i wari yakeda,,,.....
Ajiye tiraren tai sannan tazo ta zauna kusa da SUHAILA, k'ureta tai takafeta tana kallon yanayinta kamin tace "SUHAILA meke damunki ne?" shuru tamata takasayin magana sai rawar sanyi take tana karkarwa,,,....
Sake jefemata tambayar tai "SUHAILA nace meke damunki ne? Kifad'aman abunda ke damunki" ahankali dakyar taiya yaye blanket d'inda take lullub'e dashi iya fuskarta sannan tafara magana,,....
"Wallahi nasifa nima bansan abunda ke damunaba I don't no what's wrong with me, I don't no wallahi kawaida inajin zazzab'i ne gakuma ciwon kai mai tsanani" murmushi nasifa tai sannan tace "Hmm SUHAILA kenan wallahi koda ni ba likita bace amma natabbata ciki ne dake, wallahi SUHAILA kinbani kunya kinbani mamaki, dik ina wayonki da wayewarki da gogewarki dahar zaki bari kiyi cikin shege a bariki, ashe dama baki shirya shiga barikiba kika shigota, hmm kinbani mamaki wallahi",,....
D'agowa tai ta taso tazauna dakyar saboda ciwonda kanta yakemata sosai, dafe kan tai sannan tafara magana "Hmm nasifa kenan, ahalinda nake ciki a yanzu idan har baki taimaka manba kin tausaya man to baidace kizo kitsaya a kaina kina gaggayaman magana san ranki ba, dakike cewa wai nabaki mamaki ina gogewata da wayewata dahar nabari nai ciki, to inaso kitina cewa lokacinda kike d'orani akan mummunar tirbanda kike akai, lokacinda kike kokarin ganin nahau kan bakar hanyarda kike akai, lokacinda kike karantar dani kike koyardani ilimi akan bariki kinmanta baki koyardani idan nashigo bariki karnabari nai ciki ba, lokacinda kike koyardani ilimin bariki baki koyardani ilimin yanda zanyi nahana kaina yin ciki, saboda haka kisani har yanzu kinada sauran aiki dan baki koyardani yanda zan tsare kaina karna dauki ciki ba",,.....