RUWAN DARE.....31--32

1.5K 29 2
                                    

_*RUWAN DARE.....*_🌷
  _a true life story_

_*BY ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_

_*Page 31~32*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Ahankali da y'an kud'inda take dasu a account tai provision d'in komawa school, saidai harta kammala bawanda yacemata um bare um um,,.....

Ganin haka yasa tasami mama a bed room d'inta domin tamata magana, zaune take mama akan bed d'inta tana linke kayan yusrah da'aka wanke,,,....

Cikin sallama tak'ariso tazauna tareda gaishe da mama ta amsa sannan tad'anyi shuru nawasu sakonni,
Can tad'ago takalli mama sannan tace "am mama dama inaso ne namaki magana akan batun komawana school saboda hutunmu yak'are tin last 2weeks, to banji kunce komaiba shine naje nayi provision da kud'inda ke acikin account dina".....

Shuru mama tai tana k'are mata kallo cikin mamaki sannan tace "wai SUHAILA lafiya kike kuwa, wai kodai jinnu sun shafeki ne tafiyarki school dinnan?" itama mamaki ne yakamata tace "mama bann...banfahimci abunda kike nufi ba",,....

Ajiyan zuciya mama tasauke kamin tace "kije gun mahaifinki kimasa maganar ni dai baruwana ba hanuna kuma ba k'afana" daga haka ta tashi tafice abunta, kallo SUHAILA tabita dashi tama rasa mezatace, tab'e bakinta tai tareda d'aga k'afata irin ko ajinka d'innan,,,.....

               *****  *****

Bayan kwana hud'u SUHAILA tasake jin shuru bawanda yamata zancen komawarta school gashi nasifa tadawo sai kwala mata kira take a waya tadawo haka gashi Mr. Habib d'inta sai damunta nasifa yake wai yai missing d'in beauty queen dinshi,,,.....

Ganin haka yasa washe gari ranar Monday tashirya domin komawa school, cikin rantsattsiyar atamfarta mint green colour mai ratsin fari tashirya sannan tasaka hijab iya guiwarta wanda bama dan yazamemata dole tasakaba a yanzu da bazata sakashi ba, bayan tagama shirinta gaba d'aya sannan taje takira driver yazo ya kwashi kayanta yakai yasaka a mota,,,.....

Sai bayan tagama komai sannan taje gun mama tamata bankwana, mamaki ne tsintsa ya bayyana a fuskar mama saboda sam bataji dady yayiwa SUHAILA izinin ta takoma school ba, to saidai batasaniba ko k'ila taje tamasa magana yamata izini,
Fatan alkhairi tamata tareda kyakkyawar adduah sannan tafita, kasancewar dady da momy basa nan sun fita tin 8 da susi hakan yasa batareda wani d'ar ko tsoro ba tafice abunta,,,.....

Sai bayan sunkusa k'arisawa garin Aleiro L/government sannan tarubuta text taturawa dady cewar takoma school domin tacigaba da karatunta,,,....

Suna isa takira nasifa tashaida mata taiso school, aikuwa da gudu nasifa tazo suka rungume juna cikin farinciki sannan suka kwashe kayan SUHAILA suka shiga dasu ciki sannan SUHAILA tabama driver kud'i har 5k yaita mata godiya sannan yajuya yakoma gida,,,.....

SUHAILA k'in fad'awa nasifa labarin cikinta tai har tai kwana uku da dawowa, a kwana na hud'u ne Mr. Habib yakirata cewar yadawo yana garin, farinciki da murna ne suka mamayeta aikuwa nantake tafara shirya kanta domin tarban masoyinta,,,....

Itadai nasifa kallonta kawai take tanacin gayu sai goge nan take tana gyara can, ganindai abun yai yawane yasa ta tambayeta silar yin wannan gayun, dariya SUHAILA tai sannan tace,..

"masoyina ne yadawo d'azu yakirani yaceman yana garin, kinga kuwa ai dole namasa shiri na musamman domin tarbansa" dariya nasifa tai tace "Ah dole kimasa shiri na musamman, kice dai kakarmu ta yanke sak'a acikin week d'innan",,....

Dariya SUHAILA tai tace "kai sister bakida dama fa" itama tai dariya sannan tacigaba da shirinta,,,...

Around 9pm dot Mr. Habib yafaka motarsa a harabar school d'in, bayan yaiso ne yakirata yashaidamata gashi yaiso, aikuwa cikin sauri SUHAILA tayiwa nasifa sallama tafito, tana k'arisowa gun motarsa tabud'e murfin gaba tashiga,,,....

RUWAN DAREWhere stories live. Discover now