_*RUWAN DARE.....*_🌷
_a true life story__*BY ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183__*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_
_*Page 13~14*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Ahankali tashiga ciki d'akin taredayin addu'ah, d'akin na mutum biyu ne kamar yanda yake a tsarin makarantar mutum biyu a kowanne d'aki, bed biyu ne sai kitchen wanda yake d'auke da kayan aiki na girki amma ba gas cooker sbd k'aidar school d'in ne ba'a aiki da gas-cooker, wani d'an k'aramin fridge ta hango acikin d'akin wanda yake dai dai rayuwar mutum biyu ko d'aya,
Daga can gefen d'akin tahango wata k'ofa wacca koda bata bud'eba tasan toilet ne, kasamcewar school d'in sabuwa ce dika--dika batafi 3years da bud'awa ba shys komai nata sabo ne saboda school d'in tasaka tsauraran dokoki akan dik d'alibinda yai b'arna koya hallaka kayan school shys kayan basuyi komai ba sunanan da kyansu,,,....Jakarta ta sauke tacire hijab d'inta tafara tsabtace d'akin, dikda kuwa kullum ma'aikata na gyarawa amma hakan bazaihanata sake nata gyaran ba kasancewar SUHAILA akwai tsabta sosai fiye da tinanin mai karatu,,,.....
Ko'ina da ko'ina saida ta tsabtace har toilet saida ta wanke sa tass sannan tashiga tai wanka ta d'auri alwalar sallar la'asar, kasancewar weekend ne may be shys ba mutane sosai a hostel d'in sbd ko d'ayan bed d'inda ke d'akin akwai kaya akansa alamar akwai wata acikin d'akin,,.....
Bayan tai sallah saita sake sabon shiri cikin atamfa green and white colour d'inkin zani da riga da d'an kwali sannan tasaka hijab, takalmanta tasaka tad'auki phone d'inta tafita,,".....
Ahankali tafara zagaya school d'in tana ganin yanayin yanda tsarinta yake, ba mutane sosai sai kwaya--kwaya ne kake gani,.
Tanata tafiya harta kai restaurant d'in school d'in gashi dama tanajin yunwa danhaka kawai tashiga, cikin tsoro tsoro fargaba fargaba tashiga, tana shiga taje gun ma'aikatan wajen tamasu magana irin abincinda takeso sannan taje ta zauna,,,....Batajima sosai da zama ba kuwa aka kawomata, dikda ba mutane sosai acikin wajen amma cikin dar dar takecin abincin, batareda ta koshi ba saboda yanayinda takeji na bak'unta yasa ta tashi taje tabiya kud'in abincin tawuce,
Kai tsaye hostel dinsu tawuce koda taje har room mate d'inta tadawo nan tashiga suka gaisa kowacce tayiwa y'ar uwarta bayaninta, yarinyar tace "ni sunana farida Abbas Abubakar ni yar kano ce amma muna zaune ne a birnin kebbi L/government kefa?" murmushi SUHAILA tai sannan tace "nikuma sunana SUHAILA Ahmad zuru, ni haifaffiyar garin zuru L/government ce kuma y'ar k'asar kebbi State" farida tai murmushi tace "nice to meet u SUHAILA" itama tace "me too dear" sai farida tasake cewa "dafatar zamu zama k'awaye" SUHAILA tad'aga mata kai alamar eh tana murmushi,,,....Ahankali ahankali farida ke jan SUHAILA a jikinta saboda ganinta yarinya mai hankali da nutsuwa saboda ita farida 300level take saboda haka ma SUHAILA ke kiranta da Aunty, komai SUHAILA tai ba dai dai ba takan tsawatar mata sannan tamata gyara,
A cikin y'an kwanaki SUHAILA tafara sabawa da antynta farida komai atare sukeyi hatta girki ma atare sukeyi, wanki kuwa farida ke hadawa tabama innoninda ke kula da gyaran hostel su wanke masu su goge masu tabiyasu hakkinsu, SUHAILA najin dad'in zama da farida sosai saboda farida tamkar k'anwarta ta jini ta d'auki SUHAILA,,,.....__________________
Kimanin satin SUHAILA d'aya da kwana uku da zuwa suka fara lecture donhaka dik wani abu na wasa ta tattarasa ta ajiye tamayarda hankalinta agun karatu gashi tanajin dad'in yanda lecturer's d'in nasu ke koyardasu, basa masu explanation da dogon turancinda bazasu fahimtaba saboda su sababbi ne bamasu fara karatunba tinda yanzu matric ne sukeyi,,,....
Kamar kullum yauma cikin sauri take shirin tafiya class kasancewar 10am zasu shiga lecture bacci ya d'auketa har kusan 9:30am, aunty farida kuma batasan yau tanada lecture d'in safeba shys bata tadata ba kasancewar itama yau batada lecture,
Shigowar fatima k'awar farida ne yatadata daga baccin, koda taduba agogo har 9:24,,,....