RUWAN DARE.....15--16

669 29 3
                                    

_*RUWAN DARE.....*_🌷
  _a true life story_

_*BY ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_

  _*Page 15~16*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Wata iriyar bak'uwar murya taji ta amsa mata sallamar hakan yasa ta tattaro hankalinta gu d'aya domin fahimtar mai muryar,,,....

Batareda wata damuwa ba taji ancigaba da magana kamar haka "wato kedai SUHAILA bakyajin magana ko, a dik lokacinda nanemi dana ganki saikin kwasoman wasu banzayen kawayenki kinzo man dasu to bari kiji as from to day as from to now nakashe hakan dik lokacinda nakiraki kizo kekadai karki kuskura kisake zoman dawani, inafatar kinji abunda nafad'a",,,....

Da farko sam bata gane mai magana ba saida taji abunda yake fad'a sannan ta shaidashi, Mr. Zam ne, cikin rashin sanin abunda zata fad'a kawai saita tsinci kanta da fad'in "ok am so sorry Sir hakan bazata sake faruwa ba insha Allah" a can daga bangarensa wani irin murmushi yai wanda nakasa gane abunda yake nufi sannan yace "good girl, kizo office d'ina ki sameni inaso zanyi wata magana dake" har zatai magana sai kawai taji yakashe wayar sai taciro wayar tareda kura mata dara daran idanuwanta tana kallo,,,.....

Acikin zuciyarta kuwa cike take famm da tarin tambayoyi da tinaninnika barkatai akan Mr. Zam "wai meyasa Mr. Zam keson idan zataje gunsa taje itakad'ai, meyasa yake b'ata fuska yake hard'e rai idan taje gunsa tareda wasu, meyasa yake yawan kallonta idan yashigo class dinsu kokuma idan yanamasu lecture, miye dalilin nemanta dayake?",
Waennan tarin tambayoyin sune keta faman yimata zarya acikin kokon zuciyarta,,...

Ganin lokaci natafiya yasa ta tashi tasaka hijab d'inta tad'auki wayarta tafita,,,....

Cikin sallama taisa office d'insa shikadai ne aciki yana zaune kan kujera yana rike da system d'insa yana sarrafata, saida takusa 5mnts da shigowa sannan yadago tareda amsa sallamarda tai, cikin tsintsar ladabi tagaidashi ya amsa tareda kafeta da mayun idanuwansa,,,....

Ganin irin kallonda yake mata kamar zai cinyeta yasa dikta tsargu, ganin haka yasa yanunamata wata kujera dake kusa dashi kuma tana fuskantarsa yamata alamar ta zauna, ba musu kuwa ta zauna saboda irin kallonda yake mata yasa takejin kafafuwanta sunamata nauyi gwanda ta zauna kada sukasa imata,,,....

Tasowa yai daga kujerarda yake a zaune yatako yazo dab da'ita sannan yazauna akan table d'inda kujerarda take zaune yake dab da'ita, k'afarsa har tafara gogar tata cikin sauri ta matsa da'ita cikin tsoro, yanayin kayanda ke jikinsa yasa batason kallonsa,
Wani matsattsen jeans ne da t-shirt fara, sun bayyanarda kirarsa dan har kan nipples d'insa kana hangowa,,,....

Wani irin murmushi yai ganin yanayinda tashiga na tsoro danhaka yafara mata magana "SUHAILA" yakira sunanta, ahankali ta dago ta kallesa taga har yanzu ita yake kallo saikuma tasake sadda kanta k'asa,
Cigaba yai da magana "a zahirin gaskiya SUHAILA bazan boyemaki ba tin ranarda kika fara zuwa d'aukan lecture a class d'ina naganki naji nakamu da sonki, har izuwa yanzu kullum kaunarki nuk'urk'usata take, SUHAILA ina sonki ina sonki ina kaunarki"  dasauri tad'ago takallesa saikuma tajuyarda fuskarta gefe d'aya batareda tacemasa komaiba,,,"....

Cigaba da magana yai "please SUHAILA ki soni dan Allah wallahi inasonki sosai" mik'ewa tai tsaye cikin b'acin rai tace "kai hakuri sir ni inada wanda nakeso yake sona kuma harma anmana engagement dashi kuma ansaka mana rana" daga haka tai shuru kuma batakoma ta zauna ba, tasowa yai daga inda yake yadawo dab da'ita yana kallonta yace "nasan k'arya kike ba gaskiya kikafada ba" juyowa tai takallesa sannan tace "wallahi Allah na rantse da ubangiji ba k'arya nake ba inada mijina wanda yake sona nima kuma nake sonsa kuma har ansaka man rana dashi" jin dagaske take hakan yasa ransa ya baci ya harzuka saiyace mata "to shikenan naji ammafa kisani bazan hakura dakeba wallahi dole ne ko soyayya kiyi dani yaso daga baya idan shi wancan d'in yatashi sai kije kuyi aurenku ammafa dole ne nima na moreki dole ne na mori wannan kyakkyawar halittar taki",,....

RUWAN DAREWhere stories live. Discover now