RUWAN DARE.....17--18

658 37 14
                                    

_*RUWAN DARE.....*_🌷
  _a true life story_

_*BY ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_

  _*Page 17~18*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Muryarsa tajiyo yafara magana kamar haka "Inafatar baki manta da zancenda mukaiba inafatar kuma kin shirya amsar tayin soyayyata" wani irin nannauyan ajiyan zuciya tasauke sannan ta tashi tsamm tafita daga cikin masjid d'in saboda bataso kowa yaji,,,.....

Saida tadan yi nisa da masjid d'in sannan tanemi wani gu tazauna tareda share kwallanda suka zubomata tace masa "shikenan na amince" tana gama fadar haka saita kashe wayar tafashe da wani irin matsanancin kuka tana shesheka, kuka tai sosai ganin babu mai rarrashinta yasa ta tashi taje tawanke fuskarta a pampo sannan takoma masjid tacigaba da karatunta,
Saidai karatun take amma sam hankalinta baya gun talula sosai acikin zurfin tinani, tinanin take "anya kuwa batai kuskure ba wajen amincewa Mr. Zam da buk'atarsa,  anya kuwa tayiwa IMRAN adalci, anya kuwa tayiwa kanta adalci" can kuma sai wata zuciyar tace "to ai wannan itace kadai mafita agareki SUHAILA, daki rasa cimma burin ki kuma daki rasa k'imarki da darajarki data iyayenki ai gwanda ki amince tinda soyayyace kawai ta d'an lokaci tinda k'ila ma bazakiyi shekara d'aya a school d'in batareda aure ba to miye abun damuwa aciki"  rumaisa ce d'aya daga cikin class mate d'inta ta tab'ata ganin takurawa waje d'aya ido tana kallo wanda hakan ya tabbatar masu da ba karatu takeba tinani take,,,.....

Murmushi tamata sai rumaisa tace "SUHAILA lafiyanki kuwa tin d'azu ana magana kinyi shuru" d'an dukarda kanta tai tareda dafe kan da hanu d'aya sannan tace "wallahi kainane yake d'an man ciwo, barama naje nasha magani" nan sukamata sannu sannan tawuce tabarsu,,,".....

Around 5pm tana zaune acikin toilet tana wanke under were's d'inta kasancewar toilet d'in yanada d'an girma, wayarta ce a gefe tanashan k'ira'ar asshekh usman BK saitaji message tashigo wayarta,
Har tai kamar bazata dubaba saikuma tad'auki wayar taduba, nunbern Mr. Zam ce kasancewar batai saving d'in numbern ba shys batafito da sunaba amma dai ta gane numbern,,,.....

Ahankali tabude message d'in tafara karantawa "kishirya da misalin 8pm zanzo nadaukeki mufita shak'atawa, inafatar bazaki b'ata man lokaci ba idan nazo" diiimmm.....!!! taji k'irjinta yabuga saitai saurin fad'in "innalillahi wainna ilaihi rajiun" acikin zuciyarta, shuru tai tarasa wace amsa zata mayarmasa wacca zata hana wannan fitar saboda itadai bata saba da fita yawo da saurayiba koda IMRAN kuwa bare kuma har da dare bama da rana ba, tana cikin tinani saikawai tayanke hukuncin kiransa a waya danhaka tafara danna masa kira,,,....

Ringing d'aya ana biyu kuwa yadaga ba jiran komai ko sallama bataiba tacemasa "Sir dan Allah kayi hakuri wallahi bazan iya fita da dare ba bansaba kuma inatsoron kar aunty farida tagano tafad'a a gida, dady zai dakeni kuma zaiyi fushi dani, momy da mama ma zasuyi fushi dani Dan Allah Sir kayi hakuri please...!!!" takarisa cikin magiya har kwallah saida suka zubomata,
Shikuwa yariga daya bushe fitilansa inma zatafi haka yimasa magiya bazai hanasa aikata abunda yakeso da'ita ba, saboda haka yacemata "ke banason shashanci wallahi ai ke bakaramar yarinya bace da har idan zaki fita sai wani yasan inda zakije, nadai fadamaki kishirya 8pm dot zanzo nadaukeki kuma banason African time" yana gama fadar haka yakashe wayar, bin wayar kawai tai da kallo kamin tafashe da kuka saikuma tai saurin saka hanunta ta toshe bakinta kar farida tajiyota,,,....

  ___________________

Around 7:45pm bayan tai wanka tai sallar isha saita zauna akan gadonta tana tinanin ya zatayi tafita batareda farida tasani ba kuma ma har tafiya mai nisa tinda yace yawon shak'atawa, can tana cikin tinani saita tino da dabara donhaka tafara shirinta, riga da sket ne tasaka nawani material mai shegen kyau pink, blue and white colour sai Stone's dake mammanne ajikinsa, d'inkin yamata kyau sosai abunka da mai diri sai d'inkin yakamata tam saidai kayan basuda d'an kwali danhaka tasaka hijab d'inta mai tsayi amma baikai har k'asa ba,,...

RUWAN DAREWhere stories live. Discover now