RUWAN DARE....29--30

633 29 16
                                    

_*RUWAN DARE.....*_🌷
  _a true life story_

_*BY ~ AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*_

_*Page 29~30*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Dawowar SUHAILA gida wannan karon kam tasauya zane saboda abubuwa da dama sun bayyana agareta waenda suka fara bawa mama mamaki amma saitai shuru tazubawa y'ar tata ido,,,.....

    _____________________

Kimanin kwana shida da dawowarta amma har yanzu bata sauyaba, yawan bacci ga amai datakeyi a b'oye gakuma tashin zuciya datake fama dashi saikuma uwa uba wani irin haske datai wanda batadashi a da saikuma cikar k'irji datai wanda ba mama ba har momy saida sukai mamakinsa saidai sam hankalin momy baikawomata abunda mama ke tinani ba, ita kanta SUHAILA abun yafara bata tsoro saboda bata tab'a yin irin wannan zazzab'in ba,,,,.....

Zaune suke acikin katafaren parlon momy suduka harda susi su mimi ne kawai basa acikin parlon suna can parkon dady suna kallon MBC 3, itakuwa kwance take kamar kullum amma ba bacci takeba batadai jin dadin jikin natane,,"....

Kallonta mama tai sannan tace "wai SUHAILA lafiya kike kuwa? naga tinda kika dawo kullum a kwance kike dan aikace aikacenda kikema idan kunzo hutu yanzu kindaina sannan kullum so silent nake ganinki meke damunki ne?"..

Dagowa tai ta kalli mama sannan tace "nima wallahi ban saniba haka kawai nakeji banajin dadi amma but i don't no what's wrong with me...."  ido mama tak'uramata tana k'are mata kallo kamin ta d'auke idanuwanta a kanta,,,....

Momy ce tace "nima dai nakula da rashin walwalarta idan bakida lafiya ne kiyi magana man saikuje aibiti adubaki aga abunda ke damunki" mama tace "I think ai haka za'ayi asibitin kawai zanje daita"

Itadai sauraronsu kawai take batasake cewa komai ba,...

Around 8pm suna kwance akan bed din mama ita da mimi yusrah nagefe tana wasa da teddy saiga mama tashigo, kallon mimi tai tace,
"ke tashi kije parlor zanyi magana da yayarki ne" sai mimi ta tashi tafita itakuma ta zauna a kusa da SUHAILA data tashi zaune,,....

Kallonta mama tai cikin nutsuwa da da hikima irinta masu shekaru sannan tace "SUHAILA kifad'aman meke damunki ne, kidaina b'oyon ciwo a jikinki karkije yamaki illa, sanin bawani wanda kike fad'awa damuwarki sai ni yasa nazo neman sanin abunda ke damunki"
kallon mama take cikin nutsuwa harta gama sannan tace,,....

"Tabbas hakane mama kekad'ai ce nake iya fad'awa damuwata amma wallahi ba abunda ke damuna, zazzab'i ne kawai kuma tin a school nafarashi danasha magani saiya kwanta after 2days kuma saiya sake dawowa"....

Murmushi mama tai tashafa fuskar SUHAILA tace "to shkn gobe ki shirya muje hospital kiga doctor yadubaman lafiyarki yarinyata" itama murmushi tai sannan tad'auki yusrah y'ar yaye suka fita saboda yanzu a hanun momy take itace ta yayeta,,,".....

Around 1am kwance take kanta yana kallon sama, takasayin bacci tinani take wanda takasa gane kansa, shin meke damunta? Wane irin ciwo ne ke damunta? Waennan dama wasu tinaninnikan sune kemata yawo acikin brain d'inta har suka hanamata yin bacci, nantake kuma saita tsinci kanta da fargaban zuwa hospital gobe gakuma damuwar rashin habibinta wanda yaguje asanadin shigarta koleji ( University ),,...

Dakyar tinani yabarta bacci barawo yai awon gaba daita batareda tasani ba,,....

Washe gari tin 8am suka shirya saboda mama nason suga likita dawuri sudawo gida danhaka shape shape suka shirya, hijab SUHAILA tasaka wanda taji kanta a bambarakwai saboda dadewarda tai bata had'u dashiba,,,....

RUWAN DAREWhere stories live. Discover now