1to5

3.2K 114 1
                                    

👩‍❤‍💋‍👩AMINIYA TA CE👩‍❤‍💋‍👩

       💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA 💁💁
(Mrs nura kuriga)😘🌹

Dedicated this page to fatima zarah💃🏻
             1⃣to5⃣

Da sunan Allah mai rahma mai jin qai, da ya sake bani dama na sake rubuta wani sabon littafi, Ina rokan Allah daya bani ikon kammalawa dan alfarman annabi Muhammad (s a w)

"Zeena ce zaune a class tayi uban tagumi, ta rasa maike mata dadi, mlmn maths nata musu bayani amma bata ma San yana yiba, kaman daka sama taji ana kiranta da sauri ta d'ago kai, ta saki murmushi da kara, suka rungume juna ita da Mysha, Zeena tace haba friend why are you late today,I though you are not coming today, Mysha tayi murmushi tace sorry Zeena na raka daddy airport ne daka nan driver ya Kawo ni, mlmn maths ne Ya katse su tare da fadin Zeena nd Mysha keep quick please, kasan cewan makarantan kudi ne, ba'a takura ma yaran sannan teachers din kaman tsoran student din suke, domin skul din sai dan wane da wane, kowa na tsoran ya bata ma student rai, kar allura ta janyo garma, Zeena tace sorry sir, yaji gaba da gudanar dasu, har ya fita, wani ya shigo, har aka fita break, Zeena suka je, yin break suna tafiya suna fira har suka karasa restaurant din skul din, ga snacks nan kala2 sai wanda kaga daman ci, Zeena ta dauko musu ice cream Mysha kuma ta dauko, cookies suka nufi kan wani table suka ajiye kayan sannan suka zauna, suna ci suna fira, Mysha tace Zeena kin San wani Abu kuwa? Zeena tace a'a sai kin fada, Mysha taci gaba da cewa daddy dazu muna hanya zan raka shi airport yake cewa wai ina Gama secondary skul zai min aure, Zeena ta zaro ido tace what? Sai kace a zamanin da, may be he is joking, mysha tace no Zeena he is not joking, Ya dade yana yin wannan maganan, kuma daddy inya fada Abu toh he is serious, Zeena tayi shuru tare da tausayin kawar tata, can tace toh ke Mysha bakya kula kowa, yanzu wa zaki aura, Mysha tace nima abunda nake tunani kenan, yasa koda yaushe nake jin wani iri idan na tuna bani da saurayi wanda nake so, Zeena tace toh ke yanzu mai zaki fada ma daddy dinki inya tambayeki akan wanda zaki aura, Mysha tace nima ban San amsa din ba, ke gwara ke ko yanzu akace ki fito dashi zaki Kawo shi, duk da ban taba ganinshi ba, har yanzu, Zeena tayi murmushi taji an Kawo zan cen prince dinta, Mysha tace wannan murmushin fah,  a dai2 lokacin wani yaro mai suna afraz yazo kusa dasu ya kafa ma Zeena ido kaman tsohon maye yace sannunku  yan mata, Mysha ce ta amsa, yace ya naji kunyi shuru, yaci gaba da fadin Zeena wai mai yasa koda yaushe indai kika ganni saiki canza fuska, ki duba duk skul din nan ko wace yarinya so take yau ace ina kulata, amma ke na rasa dalili da yasa bakya so inzo inda kike, Ya kalli Mysha yace please Mysha am I not handsome, Mysha tace you are, infact ma babu macen da zata ganka bata kuma kallonka ba, yayi murmushin jin dadi yace thank, sannan ya kalli Zeena wanda ranta ya Gama baci da Mysha yanda take wasa shi, ta mike da nufin ta wuce, ganin haka yasha gabanta, Ya tare ta, tare da fadin Zeena you better stop this nonsense, how dare you ina magana kina wani tashi zaki wuce, duk wanda suke wajan hankalinsu ya dawo garesu, ta kalleshi ido cikin ido tace you have to know 1 thing I really hate you, I hate everything about you, infact ma bana son ganinka, tsayawa yayi yana kallonta da mamaki, dama zaiga irin wannan ranan har mace ta tsaya tana gaya mishi magana duk yanda yake da kyau ga kudi ga aji, yan mata suke rubi binshi, amma yau y'a mace take wulakanta shi, a gaban mutane, ihun da akeyi a wajan yasa ya dawo daka tunanin daya fada, a dai2 lokacin Zeena ta wuce Mysha ta rufa mata baya, yayin da afraz yaji kafanshi yayi mishi nauyi wani irin kunya ya rufe shi, amma haka ya fita, kai tsaye wajan motanshi yayi yashiga ya tada ta, Ya fita daka skul din,Sheraton hotel ya nufa ya kama d'aki, Ya kwanta idonshi yayi ja babu abunda yake tunani sai abunda Zeena ta mishi, Ya kasa komai Ya tashi dakyar yaje motanshi ya dauko kwalban codein ya kwankwade, sannan ya samu bacci ya dauke shi, a lokacin da Zeena da Mysha suka nufi class, Mysha tace Zeena kin San mai kikayi kuwa?  Zeena cikin tsiwa tace mai nayi, tell me, Mysha tace Kin San afraz kuwa kin San waye shi kuwa, Zeena tace ban sani ba ban kuma fatan in sani, plz indai kin San maganan shi zaki min, plz leave me alone, jin haka Mysha tayi shuru, amma a cikin xuciyanta tana tsoran abunda afraz zai mata domin hatsabibi ne, gashi ta wulakanta shi gaban mutane, skul din duk an baza labarin, a lokacin da aka tashi Mysha tabi Zeena dan ta ajiye ta a gida, yau bada matan ta tazo ba, kasancewan ta raka daddy dinta airport, dukansu babu mai magana, can Zeena tace Mysha mai yasa kikayi shuru baki cewa komai, Mysha tayi Dan murmushin yake tace mai zance Zeena wlh ina tsoran afraz, ban San mai zaiyi ba, Zeena tayi dan murmushi tace plz Mysha kinga ni harna manta shidin banza wlh bai isa yamin komai ba, nafi karfinshi, ita dai Mysha jinta kawai take, domin afraz bama a skul dinsu ba, kaf garin Abuja dakyar ne kaji wajan da ba'a sanshi ba, baya ji gashi idan yana son abu, ko miye sai yasan yanda ya mallake shi, kota halin 'ka' ka wannan kenan da haka har suka karasa gidansu Mysha ta ajiye ta, ta wuce gida,

Wacece Zeena?

Zeenat abubakar yan asalin garin katsina ne, su uku iyayensu suka mallaka, akwai yayanta adeel wanda yake karatu a kasar Japan sai ita dake aji hudu a famaks sai kanwarta mai suna aysha, suna kiranta da abda, sun taso cikin gata duk da irin gatan da suke ciki suna karatun islamiya kuma sun San addini dai2 gwargwado, mahaifinsu senator ne sau biyar yana ci saboda mutum ne mai rikon Amana kuma dadtijo ne, duk irin kudin da Allah ya mishi bai bar yayanshi sun lallace ba, yana tsaye akan iyalinshi, mutum ne mai son yaga yara sunyi ilimi sai yasa Zeena bata tunanin aure duk da, tana da saurayi wanda yake matukar sonta itama tana sonshi amma baya kasan nan yana China yana kula ma mahaifinshi da wasu aiyuka wajan shekara biyu, kullum suna makale a waya kaf gidansu babu wanda bai San zaheer ba, Zeena mutane da yawa suna mata kallon miskilanci don bata cika son yima mutane magana ba, in kaga ta kula ka toh babban dalili ne, sabanin kanwarta Mysha mai son magana, har wasu na mamakin kaman can nasu, sun hadu da Mysha a skul suka kulla kawance har suka hada iyayensu kawance.

Maryam obam✍✍

AMINIYA TA CEWhere stories live. Discover now