👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA 💁💁Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣1⃣0⃣to1⃣1⃣5⃣Ga kanshi dake ta sara mishi, a falon ya kwanta har bacci ya dauke shi, ita kuma Zeena bayan fitanshi itama kwanciyan tayi abunta, sai wajan asuba ta farka taje toilet tayi alwala tazo tayi sallah, bayan ta idar taji kaman ana mata nocking, taso ta share komai ta tuna kuma ta tashi ta bude kofan, taga adeel ne Ya shigo tare da fadin kinyi sallah, ta d'aga mai kai alaman eh, ya bude daya daka cikin d'akin ya shiga wanda ya ware nashi, bayan ya shiga tayi dan tsaki ta nufi d'akin ta itama,
Mysha tun jiya ta kasa bacci sai aikin kuka, babu abunda take gani sai adeel da Zeena, tana ganinsu a tare a matsayin ma'aurata, tace ni nayi sake ya kamata in dau mataki, tayi dariya tare da fadin Zeena nasan ko ke wacece, nasan yanda zan miki keda kanki zaki bar gidan nan, wannan tunanin da tayi shi yasa bacci ya dauketa
Zeena tunda ta koma bacci sai wajan 10 ta farka, ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin wani doguwar rigan material, duk da batayi makeup ba tayi kyau, ta zauna ta zabga tagumi tace koya twins suke yanzu oho, duk kewarsu ya kamata, ta dauki wayanta ta kira mum, bugu daya ta dauka, Zeena ta gaidata mum ta amsa cikin fara'a, bayan sun gama gaisawa tace ina twins mum tace sun fita da dady yanzu, tace to a gaidasu, mum tasan Zeena kewarsu take domin bata taba tafiya koda na wuni daya bane ba tare dasu ba, tace in sun dawo zata kirata, ta amsa da toh sukayi sallama, a dai2 lokacin adeel ya shigo cikin kananan kaya ya mishi kyau sosai sai kamshi yake tashi, ya kalleta yace an tashi lafiya, ta amsa da lafiya, yace muje muyi breakfast, taji gabanta ya fad'i, don bata san wani irin tarba Mysha zata mata ba, yace let go, tace no bana jin yunwa, ya kafeta da ido ganin irin kallon da yake mata yasa ta daure fuska tare da tashi tasa hijab, yayi dan murmushi yace mai kika ci, ki tashi muje ban San musu, ta mike suka fita tare sun sami Mysha a falo tasa wani top mai hannu daya da 3quater jeans, ta daure fuska kaman bata taba dariya ba, adeel yace Mysha ina breakfast ban gani a dining ba, tace breakfast banyi ba, yace saboda me, tace bashi aka Kawo ni in dinga yiba, ita wanda kaje ka kwana a wajanta ta baka mana, ranshi ya baci sosai amma saiya dake, ya kalli Zeena yace bari in Kawo miki abunda zaki ci, tace no kabarshi kawai, yace akan me kinci wani abu ne, Mysha ta kwashe da dariya tare da fadin yau ina ganin ikon Allah, ganin haka yasa Zeena ta juya tayi dakinta, shima ya bita, bayan sun shiga d'akin ya rasa mai zaice mata, can dai yace kiyi hakuri Zeena bari inje in dawo, ta amsa da toh sannan ya fita, Mysha na falon har yanzu tana ganin shi ta fara bala'i tana fadin an dai zama mijin tace, kana wani binta kana kaudi ko kunya baka ji, yayi banza da ita ya fita, har yaje ya dawo ya sameta a zaune a falon tana kad'a kafa tace Malam nima fa yunwa nake ji, ya mika mata leda daya sannan ya wuce ta bishi da harara, a lokacin daya shiga d'akin Zeena ya ganta a kwance amma idonta biyu, yace ki tashi kici abinci, bata amsa ba amma ta tashi, ya mika mata, ta amsa sannan ya fita, dakinshi ya shiga ya kwanta, ranshi ya baci akan abunda Mysha ta mishi, ina kyaleta ne kawai saboda Zeena, amma duk da hakan zanyi maganin ta, yayi dan tsaki wayanshi dake gefe ya fara kara ya dauka yaga Mysha ce, yayi rejecting Kiran, ta kara kira, da yaga hakan saiya kashe Wayan gaba daya,.
Sai wajan karfe biyu ya fito ya shiga d'akin Zeena, ya ganta tana ta aikin kuka, nan ya zauna yana tambayanta akan mai nene, mai aka mata take kuka ko Mysha ce, ta girgiza mai kai alaman a'a, ya matsa kusa da ita tare da janyota kirjinshi, nan gabanta ya hau bugu, yace kiyi shuru Zeena bana son wannan kukan, ta dan tsagaita da kukan da takeyi, yace ta tashi su shirya suje suyi lunch, tace a'a taci sauran abincin safe, yace ok, ya fara wasa da gashin kanta, wani irin sonta yake shiganshi tare da wani sha'awarta, jin bugun kofa sukayi anayi kaman za'a balla, da sauri ya tashi ya bude kofan yaga Mysha ce tana huci, tace toh Malam saika fito ka nemo min abincin da zanci, yace kina da hankali kuwa Mysha, tace ban sani ba, in banda wulakanci Kazo ka ajiye mutum babu abinci, yace wani kalan abinci ne babu miye babu a gidan Nan, tace ni dafaffe nake so, dan bazan iya girki ba, yace ok ya rufe kofan ya barta a nan waje tana ta bala'i, Zeena tana ta kuka dama abunda take tsoro kenan irin wannan abun, gashi kuma an fara, yace dan Allah Zeena kibar wannan kukan, bata kulashi ba taci gaba da kukan, dakyar ya rarrasheta tayi shuru, tace ya tashi yaje ya siyo mata abincin, yace babu inda zashi tunda akwai abinci a gidan, ganin ta bata rai yasa yace bari yaje, bai sami Mysha a falo ba ya fita,