85to90

472 6 0
                                    

👩‍❤‍💋‍👩AMINIYA TA CE👩‍❤‍💋‍👩

       💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA 💁💁

Dedicated this page to my fans  😘💃🏻
         8⃣5⃣to9⃣0⃣

Shima komai nashi ya tsaya, ganin haka ta fara girgiza shi, tana fadin afraz, dr ya shigo da sauri yace Su bashi waje, nan ya fara yan dube2 amma ina rai yayi halinshi, Zeena ta bude kofan ta shigo da sauri itama mum ta biyo ta, tace Dr ya tashi, dr yace sai dai kuyi hakuri Allah ya mishi rasuwa, Zeena ta saki dariya tare da fadin no afraz bazai mutu ba, ta matsa kusa dashi tana fadin afraz ka tashi ka karyata wannan Dr din, nasan ba zaka mutu ka barni ba, get up afraz, taja hannunshi taga yayi nauyi, ta saki ya fadi sharaf, ta saki kuka afraz why mai yasa ka tafi a lokacin da nake bukatan ka, afraz saida sonka yamin yawa sannan zaka tafi ka barni, ka tashi your unborn child is waiting for you, ba haka mukai dakai ba afraz ka tashi ta fara girgiza shi, mum dinshi ita Suman tsaye tayi ta kasa ko motsi, a dai2 lokacin dad dinshi shima ya shigo cikin rudewa ganin afraz din yasa ya tabbatar ya rasu, hawaye ke zuba a idonshi, ya matsa kusa da matarshi wanda ko digon hawaye yaki ya zubo mata a ido, gaba daya ta shiga cikin d'imuwa, Zeena ta taso da sauri tace dad kace ya tashi, yace Zeena kiyi hakuri afraz bazai tashi ba, addu'a kawai zamu mai, tace dad afraz ya mutu dagaske, yace eh Zeena ta fara baya2 tana fadin no no he will not die and leave me lokaci daya jiri ya dauketa ta fadi kasa, da sauri dad din afraz ya fita ya kira Dr, nan da nan aka fara dubata, shi kuma afraz aka daukeshi akai gida dashi da safe za'a kaishi gidanshi na gaskiya, labarin mutuwan ya baza ko ina, su abda suma sun zo asibitin, ita zauna da Zeena ummi kuma tana gidansu afraz din, kwata2 hawaye yaki zuba a idon mum sai zuciyanta dake faman buga mata, ummi tana ta mata maganan da zata danji sanyi, kiyi hakuri duk mai rai mamaci ne, kar ki zama mai butulci a lokacin da Allah zai baki shi bai fad'a miki ba, har kika sameshi kika nuna farin cikin ki, yanzu Allah ya dauki kayanshi sai ki zama mai hakuri duk son da kike mai Allah yafi sonshi, sai a sannan kukan yazo mata tace shine daya dan dana haifa yau na rasa shi, don me bazan damu ba, afraz shine komai nawa shine kwai na dana mallaka yau na rasa shi, mutuwa mai yasa baki daukeni ba, ummi ta to she mata baki, tare da fadin kar kima Allah butulci karki manta rayuwa akwai mutuwa kuma koda afraz bai mutu yanzu ba zai mutu wata rana, ki zama mai hakuri da dan gana, a yanzu babu abun da afraz yake so sai addu'a wannan kukan bashi da amfani, tayi shuru tare da fadin haka ne, ta tashi da sauri ta nufi dakinta sai gata da alkur'ani ta matsa kusa da inda aka ajiye afraz din ta fara karatu tana kuka,

Zeena wajan karfe hudu ta farka, ta bude idonta tare da fadin afraz ta tashi zaune, taga ansa mata drive, ta tsige abun ta tashi da sauri, jin kaman motsi yasa abda ta farka taga Zeena na kokarin bud'e kofa da sauri ta tashi tace Zeena ina zaki, tace abda ina afraz, tayi shuru, tace abda dagaske afraz ya rasu, abda tace Zeena kizo ki zauna, tace no ta bude kofa ta fita abda ta rufa mata baya tana kiranta ganin bata da niyan tsayawa yasa ta koma da sauri ta dauki jakanta ta fito bata ga Zeena din ba, da sauri ta shiga motarta, tayi waje ta hangota tace ta shigo suje, babu musu ta shiga, gidan su afraz din suma suka nufa, sun shiga falon gidan sunga ummi da mum suna ta karatu gefe kuma afraz ne kwance an rufe shi, da sauri ta karasa wajanshi ta bude shi, taga fuskanshi kaman mai yin bacci, tace afraz mai yasa kamin haka ka tashi in fad'ama abun da kake so kaji, afraz ina sonka ina sonka afraz, baby dinka yana son ya rayu dakai plz ka tashi kar ka maida baby dinka maraya, ummi ta matso kusa da ita, tace Zeena ta rungume ta, tana kuka ummi afraz ya tafi ya barni, saida nace karya fita ummi amma yaki, inda bai fita ba da hakan bai faruba, ummi tace Zeena kiyi shuru ki daina fadin haka koda bai fita ba indai kwananshi ya kare bazai kara koda kwana daya ba, tace ummi bazan iya rayuwa ba tare da afraz ba ummi ina sonshi ummi mai yasa haka yake faruwa a kaina, ta kuma sakin kuka, ummi tace ta daina kuka tamai addu'a ne, ta matsa kusa dashi tana tamai addu'a tana kuka, duk wanda yake wajan saida ya tausaya mata.

Mutane sun taru a kofar gidansu afraz din sosai daka gari2 mutane keta zuwa, anyi mishi wanka an mai sutura dama an barshi sai wajan 8:30 za'a kaishi gidanshi na gaskiya hakan ko akayi, a lokacin da aka dauko shi Zeena kuka take kaman ranta zai fita, ta kankame gawan, dakyar aka banbare ta, aka wuce dashi, rayuwa kenan, afraz yayi mutane sosai, Allah yasa mu cika da imani,

Ana ta zuwa musu gaisuwa kota ina, Zeena kwata2 taki cin komai, anyi2 taki ci, saida mum din afraz tazo da kanta sannan ta yarda taci, shima ita take bata a baki, ci kawai take amma bata jin dadin komai, inta kalla cikin ta saita fashe da kuka, tana fadin afraz ka tafi baka ga baby dinmu ba.

A yau akayi addu'an uku, mutane kowa ya watse, an barsu su kadai, ciki harda ummi wanda tun da akayi rasuwan itama tana gidan ita da abda, yanzu daka Zeena sai mum din marigayi afraz da dad dinshi, suka rage a gidan sai masu yi musu hidima, Zeena duk ta rame tayi baki kullum tana cikin hawaye, mum taita bata baki akan tayi hakuri ta rage damuwa ba ita daya bace, inta kiyin shuru saita ce mata da afraz yana nan ba zaiji dadin wannan kukan ba, inta ji hakan sai tayi shuru.

Wata ranan juma'a da yamma Zeena tana zaune tana karatun alkur'ani mum ta shigo d'akin ta zauna a gefe, Zeena ta saki kara tare da fadin ciki na, mum tace Zeena sannu tashi muje asibiti, ta kira daya daka cikin masu aikin gidan suka kama Zeena din aka sata a mota sukai asibiti da ita, tana ta faman fadin ciki na, nan da nan akai labour room da ita, mum ta kira ummi ta fada mata bata dade ba tazo, tare da abda, sun dauki wajan awa uku amma shiru babu labari sai azaba da Zeena din kesha, akace dole sai an mata operation domin ba zata iya haiyuwa da kanta ba, suka ce sun yarda ayi, nan da nan likitoci sukayi kanta aka fara aiki, su ummi babu abun da ake sai addu'a, wajan karfe goma da wani abu Dr ya fito yana murmushi tare da fadin congratulations an sami twins, baby girl nd baby boy, mum ta d'aga hannu tana ma Allah godiya, suka cewa Dr din zasu iya shiga yace eh, da sauri suka nufi dakin, Zeena tana kwance yaran na gefe, babu abun da take sai hawaye, mum ta dauki yaran duka yaran kaman afraz kaman an tsaga kara, kaman yayi yawa sosai, mum itama ta fara hawayen tace Allah sarki afraz, Allah yaji qanka, ummi tace Zeena ki daina wannan kukan, tace ummi naso afraz yaga wannan ranan inga wani irin murna zaiyi, ya dade yana burin zuwan wannan ranan, ta kuma zubo da wani hawayen wani son yaran taji yana shiganta tare da tausaya musu.

NOTE: masu cewa afraz bai kamata ya mutu ba, inya mutu novel din ya baci, kufa tuna Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, kuma karku manta duk mai rai mamaci ne. Rayuwa akwai mutuwa akwai tsufa kar ko da yaushe mu dinga mantawa da mutuwa, duk da novel ne wannan ya kamata mu dinga sawa akwai mutuwa a ciki ba kullum ace sun kasance tare cikin jin dadi da kwanciyan hankali ba, indai akace kullum haka ne Ya zama babu amfani rubuta littafi tunda ana mantawa da mutuwa ya zama shirme, sau da yawa ina rubuta akan abun da yake faruwa ne, Allah yasa mu dace

Maryam obam✍✍✍

AMINIYA TA CEWhere stories live. Discover now