👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA 💁💁Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣3⃣5⃣to1⃣4⃣0⃣Adeel yayi sauri ya janyo ta, Zeena wanda tayi Suman tsaye dan tsoro, tace ka sake ni, yau sai anyi ta, ta kare, ta kuma zabura zata nufi Zeena, ganin haka Zeena ta matsa da sauri tayi baya, shi kuma ya kuma janyo ta, tare da marinta har sau biyu yace kije na sakeki saki daya,nan komai nata ya tsaya, da mamaki ta kalle shi, tace adeel saki, nika saka takan wannan banzan, ya kalleta yace wannan ya rage naki ya kama hannun Zeena sukai ciki, suka barta a nan, bayan sun shiga Zeena harda sama d'akin key tayi adeel yayi murmushi, dan tana ganin Mysha Zata iya shigowa ciki, adeel ya zauna akan gadon d'akin ya daura hannu akan kanshi, duk sai yaba Zeena tausayi, ta matsa kusa dashi tace adeel gaskiya banji dadin abun da kayi ba, yasa mata hannu a baki alaman tayi shuru,yace Zeena wani kalan adalci ne banma Mysha amma duk bata gani, ban taba cin amanarta ba ran girkin ta, amma ita bata da wani Abu kullum sai zargi, na rasa wannan irin halin nata, Ina zama da ita ne saboda ke da kuma yarona, amma yanzu na gaji gwara ta wuce, dan wata rana zata iyayi miki komai karta je ta kashe min baby, Zeena tayi shuru bata ce komai ba, ganin haka yasa yace ki daina tunani kar kisa baby dina cikin damuwa shima, tayi dan murmushin yake,ita harga Allah bata ji dadin sakin daya ma Mysha ba.
Mysha ta nufa d'akin ta, tana ta rusa kuka, tare dajin haushin Zeena, tace Zeena saboda ke adeel ya sake ni, yanda ya sake ni kema haka saiya sake ki, dan bazan barki ba, ta diba wasu daka kayanta tasa a akwati tayi gidansu ita da ahmad, tana shiga taga mamanta da gudu ta fad'a kanta tana kuka, mahaifiyar ta duk ta rude tana tambaya lafiya, mai ya faru, tace mum adeel ya sake ni, maman tace what saki, tace eh mum, tace kiyi shuru ki daina kuka bari in kira dady dinki, maman ta tashi ta nufi d'akin dad din Mysha din, Jim kadan sai gasu tare sun fito, mahaifin ta, yace maiya faru, nan ta fad'a mishi karya da gaskiya ranshi ya baci yace tayi shuru taje d'aki zai nemi adeel din, maman tace neman shi akan me mai za'a mai kawai ka barshi, yace ai ba'a haka dole shima inji ta bakinshi wannan shine adalci, tace wani adalci bayan ya wulakanta mana y'a harda saki kuma, ni na yarda da y'ata ba zata min karya ba, yace hakane amma koma dai miye dole inji ta bakin shi, yana fad'in haka ya koma d'aki, ranan Mysha kasa bacci tayi sai aikin kuka, tabbas tana son adeel irin son da ba zata iya musultawa ba, Zeena kece silan komai saboda ke ya sake ni, tayi murmushi tare da fad'in adeel dole in koma gidanka ko dan darajan dana,.
Zeena tana falo tayi uban tagumi kaman wacce aka ma mutuwa, adeel ya fito daga d'aki yaga yanda ta zabga tagumi, ya karasa gareta tare da cire mata hannun, yace tunanin mai kikeyi haka Zeena, tayi dan nishi sannan tace adeel dan Allah kayi hakuri ka dawo da Mysha, jin haka yasa ya daure fuska tare da fadin indai kika ci gaba da fad'a min wannan maganan zaki ga fushi na, tace adeel nasan bata kyauta ba am.... Ya d'aga mata hannu tare da fadin ni na fita, ta bishi da kallo cikin takaici, ita dai tana so ya dawo da Mysha dan tasan Mysha tana son adeel sosai kuma sonshi yasa take duk abunda take yi, haka ranan Zeena ta zauna cikin tunani.
Mysha duk irin gatan da mum dinta take mata, bata jin dadin zaman gidan, ita burinta yau ace ta koma gidan adeel, domin inta tuna yana tare da Zeena wani bakin ciki take ji, tare da tsananta, Zeena na rasa dame kika fini da yasa komai nake so sai kin raba ni dashi, kowa ke yake so, miye banda shi wanda ke kike dashi, kukan ahmad ne yasa tayi sauri ta dauke shi, tana jijjiga shi,
Mahaifin Mysha ya kira adeel, akan maiya had'a shi da Mysha nan ya fada mishi irin abubuwan da take mai, ran mahaifin nata ya baci sosai, yace ma adeel ya gode saiya neme shi sukayi sallama, yana zuwa gida ya kira Mysha ita ma mamanta ta fito, nan ya zayyane mata abun da Mysha tayi, itama taji mamaki tace Mysha ce take hakan, gaban Mysha sai fad'i yake dan tasan yau ta bani, mahaifin nata yace kin kyauta tunda zaman gida kika zaba saiki zauna, kin samu yaro mai hakuri kinje kina mai abunda kika ga dama, inda wani ne daya dade da koranki ko kuma ya miki dukan tsiya, tunda baki da kirki daka yau zan kafa miki doka bake ba fita, ki zauna a gida tunda shi kike so mutuniyar banza, mamanta tace Mysha ina kika koyo wannan bakin halin wanda ban sanki dashi ba, ke kin taba ganin inama babanki haka, babu abunda Mysha take sai kuka, domin tasan tunda dad dinta yayi fushi da ita, tasan yanzu bata ba wani jin dadi, dad dinta yace ta tashi ta basu waje, ta tashi da gudu tayi d'aki tana aikin kuka,
Bikin zaheer ya matso anata shirye2, dakyar adeel ya bar Zeena taje gida tayi sati daya, anata shagalin biki gidansu Zeena ya cika da mutane sosai, an daura auren zaheer da amaryan shi Zaynab yar garin adamawa, washe garin daurin dauren zasu koma Japan domin ya samu aiki a can haka ko akayi ango da amarya suka wuce yan biki kowa ya watse, adeel ya kira Zeena yace yaushe zaki dawo, tace nan da 2week dan na gaji da hidiman biki, Ina so in dan huta, ya kashe Wayan Jim kadan ya kuma kira yace fito ina kofar gidanku, yana gama fadin haka ya kashe Wayan,sai gata ta fito ta zagaya ta shiga cikin motan tana shiga yaja suka wuce, tace ya zaka wuce dani banyi ma ummi sallama ba, yace ki kirata a waya, tun daka lokacin bata kuma cewa komai ba har suka isa gida, ranan Zeena tasan mijinta yayi kewanta kaman itama yanda tayi,
Mysha ce zaune ahmad nata wasa ta rame da danyi duhu, kullum tana cikin tunani ga iyayenta sun daina sakan mata sosai, mu samman ma dady dinta, gashi bata fita ko ina, inta kira adeel baya dauka, sai dai ta mai text tana bashi hakuri akan ya maidata, shima babu reply, sai a yanzu take nadaman abunda tayi, wani hawaye ya xubo mata, adeel sanka da kuma kishinka yasa nayi duk wa innan abubuwan, gashi yanzu ya tashi a banza tunda ka sakeni, lokaci daya taji tana nadaman abunda tayi, domin tasan nata kishin ya wuce musali,cikin wannan halin mum dinta ta sameta a ciki, ta tausaya ma yar tata, tace Mysha ki daina wannan kukan domin bashi da amfani, kuma komai Ya faru ke kika jama kanki, tace mum wlh ina son adeel dan Allah mum kisa dady ya mishi magana ya mayar dani, mamanta tayi shuru, tace Mysha dad dinki yayi fushi sosai dakyar in zaima adeel magana amma zan jaraba bashi hakuri.
Cikin Zeena yakai wata7 tana samun kulawa wajan adeel, kullum yana nuna mata so da kauna, itama tana iya kokarin ta wajan nuna mishi kulawa, suna zaune a falo wayanta yayi ringing ta dauka taga number ne, ta kara a kunne jin muryan Mysha tayi tana kuka, tace Zeena dan Allah kiyi hakuri akan abunda na miki, Zeena tace babu komai, sannan tace dan Allah kisa adeel ya dawo dani, wlh Zeena Allah ya jarabce ni da sonshi, Zeena tayi dan murmushi wanda bai kai ciki ba, tace zan mai magana duk yanda mukai zaki jini, ta kashe Wayan sannan ta kalli adeel wanda ya bata rai, tace lafiya kuwa naga ka daure fuska, yace banso kimin maganan Mysha plz, tace haba adeel karfa ka manta akwai yaro a tsakaninku ko danshi ya kamata kayi hakuri ka dawo da ita, yace Zeena bazan iya dawowa da Mysha ba, domin Mysha ba macen aure bace, Zeena tayi kaman za tayi kuka tace adeel ka dawo da ita saboda Allah, badan halinta ba, kuma na tabbata tayi nadama tunda harta kirani tana kuka akan inyi hakuri akan abunda tamin, nan yayi shuru dakyar Zeena ta samu ta shawo kanshi ya yarda,..
Adeel da Mysha sun dawo matsayin mata da miji Mysha ta canza kaman ba ita ba, komai ita take ma Zeena tace bata so tana komai tunda ba ita kadai bace, adeel har dan kiba yayi saboda yanzu ya sami kwanciyan hankali a gidanshi,
Adeel shi ya dauke biya masu twins karatu yana musu hidima kaman yaran daya haifa, Zeena kullum tana kara godewa Allah akan baiwar da yayi mata, ita da Mysha sun fara business Ana Kawo musu kaya daka waje suna sai dawa, Mysha da Zeena Ana zaune Ana fira, Zeena taji kaman ana tsungulinta a mara, tun tana ji kadan harta fara ji sosai, nan ta saki kara Mysha tayi sauri ta riketa tana fadin Zeena lafiya maike damun ki, tace Marana, dakyar Mysha tasa ta a mota sukai asibiti suna zuwa akace haiyuwa ne, akai labour room da ita ko minti talatin ba ayi ba ta haifa yarta mace, sai a sannan Mysha ta kira adeel take fad'a mai, zo kuga murna nan da nan yazo asibitin, yaga yar kaman Zeena sai dai ta dauko kalan hancin shi, yarinyan kyakyawa,
Zeena da baby dinta suna samun kula wajan Mysha sosai, ranan suna yar taci sunan ummi habiba, suke kiranta da ma-ma, mum tasai ma yarinyan kaya da yawa, haka itama ummi, ga wanda Mysha itama tayi, abda itama tayi aure ta auri wani saurayinta wanda suke san juna sosai, a dubai zata zauna saboda karatun ta.
BAYAN SHEKARA BIYAR
Zeena zaune da yaranta su uku, ma-ma da sadeeq sai anan, suna ta wasa, Mysha ta shigo ita da yaranta da gudu yaran suka tashi suna tsalle na ganin yan uwansu, Zeena tace har kun dawo kunyi sauri, Mysha tace wlh kuwa duk na gaji, itama yaran Mysha biyu, ahmad da saudat, nan yaran sukai waje suna wasa, ita kuma da Mysha suna ta hira, har adeel ya dawo, shima ya zauna anayi dashi, yace yanzu dai kun daina bani kulawa aure zan kara, jin haka Zeena ta tamke fuska, Mysha tace ai babu wacce ta isa ta shigo wannan gidan, yace haka kika ce, zaku gani ai jin haka Zeena tabar wajan, Mysha ta saki dariya tare da fadin sai kaje kaba aminiyata hakuri, yayi dariya shima sannan ya tashi ya nufi d'akin Zeena din, tana ganin shi ta kawar dakai gefe, yayi dariya yace haba amarya ta, jin haka ta saki kuka tana fadin ni ka daina cemin amarya wanda zaka aura ita zaka kira da haka, yayi dariya tare da fadin kece amarya ta, tunda na sameki na cire ko wace mace a raina, taji dadin abun da yace, yace ashe dai ana kishi na, ta rufe fuskanta da hannu, yayi dariya nan suka fada faranta ma juna nima dai a nan zan tsaya.
ALHAMDULILLAHZaku iya samun novels dina a grp dina :maryam obam novels
Maryam obam ✍✍