70to75

912 33 1
                                    

👩‍❤‍💋‍👩AMINIYA TA CE👩‍❤‍💋‍👩

       💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA 💁💁

Dedicated this page to basma darling 😘💃🏻
          7⃣0⃣to7⃣5⃣

Jin karan kofan d'akin yasa ta fito, tare da rufe kofan ta da key, tayi tsaki yanzu wannan ne miji na, ai wlh ba zaka taba samun abunda kake soba a waje na.

Afraz tunda ya fita daga d'akin ta, gidan ya bari gaba daya, bai dawo ba sai wajan karfe tara, a lokacin tana falon kasa tana kallo har ya shigo bata sani ba, ji tayi an rukota ta baya, ta saki ihu, duk ta tsorata, ta bashi dariya amma saiya dake, ta fara kokarin kwace kanta daka rikon daya mata, ya sake ta, ganin haka yasa ta tashi zata gudu ya kuma kamo ta, tace ka sake ni, yai kaman bai jita ba, ya kuma janyo ta, Ya zaunar da ita kan kafanshi, ta daure fuska, ganin shima ya tamke fuska yasa ta kasa cewa komai, yace kinci abinci, ta daga mai kai alaman eh, ya janyo wani leda, ya bata, bata musa ba ta amsa, ta tashi daga jikinshi tayi sauri tayi sama, ya bita da kallo harta bace sannan ya kauda kanshi, yayi murmushi ya rasa wani irin so yake ma Zeena.

Bayan taje d'aki ta bude ledan taga kaza ne da ice cream da abinci, ta bude kazan taci da ice cream, tayi nak, ta fad'a toilet tayi wanka ta fito tana shafa mai, a lokacin ya shigo d'akin ya kura mata ido, ta waiga ta ganshi ta tashi da sauri tare da fadin miye na shigo min d'aki babu neman izini, yayi dan murmushi tare da fadin nida d'akin matata saina nemi izini, ganin yana matsowa yasa tayi shuru, tana matsawa baya, har ta hade da bango, shima ya karasa ya manneta, suna shakan numfashin juna ganin yanda yake kallonta yasa tayi kasa dakai, wani nugun sha'awanta yake ji, wanda bazai iya hakuri ba a wannan lokacin, daukanta yayi cak, ganin haka ta fara wintsil2 amma ko a jikinshi dakinshi yayi da ita, ya ajiyeta a kan gadon d'akin sannan ya rufe kofan, ganin haka ta fara kuka tare da fadin dan Allah afraz karka min komai kayi hakuri, yace Zeena nifa mijinki ne, kuma ina bukatanki, tace bana so bana sonka dan Allah karka min komai, yace bakya sona koh, tace eh, yace owk shikenan bari in kira daddy dinki saiki fad'a mishi ni kuma saina sauwake miki, jin haka tace karka had'a ni da iyayena bana so, yace toh ki bani hakki na, tun daka lokacin bata kuma magana ba, nima ganin haka na fita daka d'akin, na koma da asuba naga Zeena tana ta kuka shi kuma afraz yana ta rarrashi yana bata hakuri, dakyar ya shawo kanta tayi shuru ya kaita toilet yace ta shiga tayi wanka, ganin kaman bata da niyan shiga ya dauketa yasa ta cikin ruwan zafi, ya kura mata ido wani sonta yake kara shiganshi, ganin kallon da yake mata yasa ta kuma sakin kuka, duk ya rud'e yana tambayanta mai nene, tace ka fita, yayi dariya ya tashi ya fita.

Adeel ya yanke hukuncin komawa China da zama domin bazai iya zama a nja ba, yaga Zeena tare da wani mijin, tunda ya tabbatar tayi aure komai nashi ya canza abu kadan, yaita fad'a akai, ga saurin fushi da yake yi yanzu wanda duk bayayi da, itama Mysha ta samu labarin Zeena tayi aure hakan ya mata dadi domin tana ganin yanzu zata samu mijinta, tayi alkawarin ko zuciyan dutse gareshi saiya sota, wannan kenan.

Zeena inta tuna abun daya faru tsakaninta da afraz sai tai ta kuka, yanzu ya rabata da adeel kenan, yayi nasara akan ta, ta tuna lokacin daya mata alkawari saiya mallake ta, gashi yanzu ya sameta, wani takaici taji tare da bakin ciki, tace afraz zaka iya samu na, amma ba zuciya na ba, bazan taba sonka ba,

Afraz tunda ya sami Zeena duk ya daina harkan mata, domin duk yawon barikin da yayi bai hadu da wacce takai Zeena ba, tunda ya sami Zeena yanzu bashi da wani buri illa ace Zeena ta fara sonshi, shine abunda yake fata.

Yau watan Zeena uku da aure, tana zaune a falo, afraz ya fito, ta kalleshi tace ina son magana dakai, yace inaji, tace inaso inje gida yau  yace ba yanzu zaki fara fita ba, ta dan marairaice tace plz, yace in kina so kije gida sai kin min kiss a baki, jin haka yasa ta daure fuska tare da kau dakai gefe, yace ok ni na fita ganin zai fita yasa ta tashi da sauri ta shiga gabanshi, yaso yayi dariya yanda yaga tazo da gudu amma saiya dake, ta rufe idon ta, yace ai bani zan miki ba, ke zaki min, ta dan turo baki, ganin yana kallonta tace toh ka daina kallo na, Yayi dariya yace in ban kalleki ba taya zaki min, tayi shuru tana kallon kasa yace ni zan fita in ba zakiyi ba, da sauri tayi mishi kiss din sannan ta ruga da gudu, Ya bita da kallo yana dariya, ya koma ya zauna a falo din, Jim kadan ta fito cikin wani material mai kalan c green ya mata kyau sosai, yace Zeena yanzu haka zaki fita babu mayafi, tace toh ba'a mota bane, yace koma a miye ban yadda da hakan ba, ki koma kije kisa hijab muje, kaman za tayi kuka ta koma ta dauko hijab din, yace kinga yanda kikayi kyau kuwa, ta turo baki, suka fita, wani super market suka je, yace suje tayi musu tsaraba suka shiga ta dauka abubuwan d zata dauka ya biya suka wuce, bayan ya sauketa yace wajan 5 zaizo daukanta tace toh, ta shige, masu gadin gidan yasa suka shigar da kayan tsaraban,Ya wuce.

AMINIYA TA CEWhere stories live. Discover now