20to25

769 34 0
                                    

👩‍❤‍💋‍👩AMINIYA TA CE👩‍❤‍💋‍👩

       💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA 💁💁

Dedicated this page to waleeda luv😘
           2⃣1⃣to2⃣5⃣

"wasa2 yau wajan wata daya adeel yana fushi da ita, ga Mysha ta rasa gane kanta, ta gefe daya kuma gashi zasu fara exam duk tunani ya mata yawa, ga afraz irin abubuwan da yake mata yayi yawa,

Zeena ta kalli Mysha tace muje study room muyi karatu, Mysha ta dan yamutsa fuska tace no kije kaina yana min ciwo, Zeena tayi dan sororo tana kallon ta, tace muje kisha magani mana, tace ki barni plz Zeena am ok, ganin haka Zeena ta fita, ta nufi study room din tare da tunanin maike damun Mysha kwana2, a lokacin data karasa taga afraz a kofan study room din, shida wasu abokan shi, ta daure fuska ta nufi ciki, shima bai kulata ba, hakan ya mata dadi, inta tuna ya kusa barin skul dinma sai taji wani farin ciki.

Mysha ce zaune a cikin Millennium Park, tana jiran adeel, tana shan drink, bata wani dade ba, yazo, bayan ya zauna ya kalleta babu yabo babu fallasa, yace Mysha lfya kika kirani nan, ko Zeena ta amince ne, ta dan yamutsa fuska jin an kira sunan Zeena, tace nop dama ina son magana dakai ne, yace ok ina sauraranki, ta dan saki murmushi tace adeel kai yanzu kana ganin zaka tsaya jiran Zeena har sai ta kammala karatun ta? Ya danyi shuru can yace bazan iya ba wlh Mysha alhaji na ya dameni yanzu ma yaban nanda wata daya in Kawo mata koya aura min duk wacce yaga dama, plz Mysha kima Zeena magana ko zata tausaya min wlh ina son Zeena kullum da tunaninta nake kwana nake tashi, Mysha tace indai Zeena ce ba zata amince dakai ba, tana da kafiya, babu yanda banyi da itaba amma taki yarda, sai yasa na kiraki in shawarceka, yace ina jinki, tace adeel nima mahaifina yace ina gama secondary school zaimin aure, yace gwd haka yana dakyau ai domin shine ya dace da y'a mace, gidan mijinta, tace haka ne, toh amma akwai matsala yace name kenan, tace bani da saurayi wanda nake so, yace aiya Allah ya baki, tayi dan murmushi tare da kara make murya tace adeel mai zai hana ka nemi aure na, yace what Kin San mai kike fada kuwa Mysha, tace eh na sani adeel, kaga kai an baka 1month ni kuma yanzu gobe zamu fara exam na zuwa ss2, anan kuma zanyi waec, nasan kana San Zeena ita kuma tana da burin karatu mai zurfi kafin aure, kaga nima ina da burin karatun amma dady na yace a d'aki na zanyi, kaga inka aure ni, zamu taimaki juna, zanyi karatu na, idan Zeena itama ta gama saika sakeni ka aureta, yayi shuru can yace sorry Mysha I can't do it, Ya tashi yabar wajan,  tayi tsaki tare da fadin wlh adeel kota wani hali saina zama matarka, taji wani tsanan Zeena a ranta.

Su Zeena an fara exam yanzu ba kaman da ba Mysha an dan sake ma Zeena kadan, afraz an bar skul suma sun kusa fara waec,sai dai yakan dan zo jefi2,

Wayan Mysha kema ringing tayi tsaki ganin sunan adeel yasa tayi sauri ta dauka tare da fadin hello, bai jira ta gama fadin abunda zata ceba, yace ina kofar gidanku, tayi sauri ta tashi ta dauki gyale ta fita, ta sameshi cikin mota ta bude ta shiga, da murmushi a fuskanta, Ya kalleta yace Mysha na amince da kudirinki zan aureki amma zan sakeki bayan Zeena ta Gama karatu, don ita nake so, I tace zabi na, tayi dan murmushi tace babu komai, amma da sharadi yace name, tace karka fadama Zeena yanda mukayi, yace babu komai. Sukayi sallama ya wuce, ta shiga gida tana murna ta sami adeel, tace ai adeel kaida Zeena har abada tayi wani dariya wanda ita tasan mai take nufi.

Yau Zeena tayi mamakin canjin Mysha ganin haka yasa take fada mata adeel ya daina kulata, Mysha tace ki shareshi kema tunda ba'a dole, Zeena tace baki San yanda nake son adeel ba Mysha wlh ina son adeel fiye da komai, duk na rame ko abinci bana iya samun ci in koshi saboda tunanin shi, yaki yamin uzuri, wlh Mysha ban so inyi aure ban kammala karatu ba, domin bazan iya ba mijina kulawan daya dace ba, ga karatu ga hidiman mijina, kinga inna Gama karatun in mukayi aure zai samu kulawa sosai, Mysha tayi shuru amma ji takeyi kaman ta shake Zeena dan haushi, tace Zeena tunda kin dage karatu zakiyi sai kiyi ni bari inje inada abunyi.

Maryam obam ✍✍

AMINIYA TA CEWhere stories live. Discover now