👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA 💁💁Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣0⃣0⃣to1⃣0⃣5⃣A lokacin da ummi ta koma gida tama dady magana akan a daura auren nan da sati biyu, in yaso saita tare daka baya, dady yace akan wani dalili kuma, bayan an tsaida rana kuma yanzu a canza, ummi tayi shuru bata kuma cewa komai ba, jin haka dady yace akwai wani matsala ne, tace a'a babu, naga kaman ansa lokacin ne yayi yawa, dady yayi shuru can yace ai kaman yanzu ne, zaki ga yayi, abda ta shigo falon da fara'a a fuskanta, ummi tace anyi nasara kenan, tayi dariya tare da fadin eh ummi, ta mika ma ummi takardan tace lallai abu yayi kyau, dady tace mai nene, ummi tace waec din tane, yace har ya fito, yanzu sai shirin zuwa high instuition kenan, tace eh dady, tana dariya, nan suka zauna suna ta fira cikin sha'awa,.
Tunda ummi tazo gidan tama Zeena magana, babu wanda ya kuma mata maganan auren, hakan ya mata dadi dan tana ganin kaman an fasa ne, ita kwata2 yanzu adeel baya cikin tsarinta, domin kuwa ba zata iya kishi da Mysha ba, domin yanda taga Mysha a saudiya ta musu, Ina ga in sun hada miji, wani hawaye ya zubo mata tare da fadin afraz ka tafi ka barni gashi yanzu ina cikin kunci, babu mai rarrashi na, Ina ma kana nan da duk haka bai faru ba, mutuwa ta rabani dakai masoyi na, a lokacin da nake son kasancewa dakai, lokacin da nake bukatanka, ta kuma zubo da wani hawayen afraz ka tafi ka barni da sonka, a raina, naso ace tare muka mutu, duk wannan maganan da takeyi a fili take, mum ta shigo d'akin taji duk abunda take fad'a, taji tausayin Zeena din sosai, ta matsa kusa da ita, tace Zeena ki daina fadin haka, afraz ya tafi yabar miki yaranshi Zeena ki daina sa wannan abun a ranki, afraz addu'a yake bukata, sannan kuma yaranshi duk da basu sanshi ba, ki fad'a musu waye babansu su taso suna mai addu'a indai kikayi haka kin mai babban gata, kuma kin nuna mishi dagaske kina sonshi, ta kuma fashewa da kuka ta rungumi mum din,.
Yau an tashi garin Abuja ana zafi, Zeena tama twins wanka tasa musu kaya mara nauyi, tana zaune taji zafin itama ya isheta duk da a.c a kunne yake, ta tashi ta sami mum tace zata wajan ummi, mum da fara'a tace kai yau wani rana, tunda afraz ya rasu sau biyu taje gidansu, itama tayi murmushi, mum tace ai kin kyauta Zeena amma zama waje daya babu dadi, shi yake sama mutum yaita tunani, tace hakane, tace ma mum ta wuce ganin zata fita twins suka bita da gudu, suka makale ta, abun ya bata dariya tace ku koma ku taya mum fira, suka ki sakinta, mum tace haba ya zaku min haka, dawa zaku barni a gida, kuzo muje muma anjima zamu fita, ganin mum zata zo inda suke suka sa kuka, mum tace kuyi shuru tare zaku, jin haka sukayi shuru suna dariya, suka fita suna ma mum bye2, tace zaku dawo ai ku sameni,
Kai tsaye gidansu Zeena ta nufa, bayan tayi parking ta shiga, taga motar dady a gidan alaman yana gida kenan, sun shiga falon gidan da gudu abda tazo ta kamo hannun twins, tana fadin what a surprise yanzu nake son kiranki ince zanzo sai gaku, Zeena tace kedai abda kin iya tsara zance, tayi dariya tare da fadin ki tambayi dady kiji, a gabanshi na fada, jin haka dady yace to ai tunda tazo shikenan, nan ta gaida dady ya amsa cikin fara'a ya kira jikokin shi, suka zo wajan shi yana musu wasa, ummi tace ma afraz yazo ya noke alaman a'a, tace au niko to yau babu auren na sallameka, dady yayi dariya yace kishin ne ya motsa kinga amarya tazo ko, sukayi dariya, Zeena da abda suka shige ciki,
Bayan sun shiga Zeena take tambayan abda akan maganan bikin da ake shirin yi, yana nan ko an fasa, abda da mamaki tace a fasa kuma, aike zaki fi kowa sani ai, tunda kuna waya da adeel din, ni nasha mako kinzo mu tattauna akan bikin ne, Zeena ta sakar mata harara tare da fadin sai ki tattauna dashi ai, abda tace mai yayi zafi kuma, Zeena tace abda Kin San wani abu, kin dai San yanda abubuwa suka faru a baya toh ina so kiban shawara, ada naso adeel Mysha ta aure shi, daka baya na gano, abunda yasa ya aureta, a lokacin Allah yasa bani zai aura ba, nima na auri afraz bana sonshi amma daka baya Allah ya dauramin sonshi, har ya rasu ya barni da mugun sonshi a raina, wanda a yanzu nake kallon bazan iya kallon wani namiji da sunan so ba, ko aure ba, gashi su ummi sun tsaida ranan aurena da adeel, abda bazan iya kishi da Mysha ba, taya zan rusa wannan auren, abda tace haba Zeena ban taba tunanin haka daka gareki ba, dady yasan ba zaki bashi kunya ba shiyasa ya amsa musu, kuma bros zaheer ya fada mishi kina son adeel, shi yasa ma harya amsa maganan auren kuma dady yayi hakan ne dan ya faranta miki, bama haka ba idan kince baki son auren haka zaki bar yaranki babu uba, ai ya kamata yau ace sun taso da wanda zasu dinga kira da mahaifinsu,kuma na tabbata yanda adeel yake sonki zai rike miki yaranki, tace abda banki taki ba adeel fah mijin Mysha ne AMINIYA TA, abda tace to sai me dan mijin tane, idan ita bata ji kunyan aurenshi ba, taci amana toh kece zaki ji kunyan aurenshi, aiba zamanta zaki yiba, Zeena tayi shuru tabbas maganan abda hakane kuma gaskiya ta fad'a, toh amma yanzu taya zata kalli adeel a matsayin mijinta, harta iya zaman aure dashi, wata zuciyan tace don yaranki zakiyi, sai wajan 5 Zeena suka koma gida, da gudu twins suka shiga suka fad'a kan mum dake zaune a falo tace oyoyo, suka saki dariya da murna na ganin mum, nan suka nuna mata kudin da dady ya basu,tace to su bama mamansu ta ajiye musu, suka nufi Zeena suka bata, nan suka zauna suna ta fira da mum,
Bikin yana ta gabatowa, ita Zeena harga Allah bata murna da auren, dan tana ganin kaman taci amanan afraz idan ta sake wani auren, gashi a yanzu babu daman tace ta fasa domin bikin baifi sati daya ba, ga adeel tunda yazo mata gaisuwa bai kara zuwa wajanta ba, sai dai twins da yake aiko ma da kaya, kala2 hakan yana mata dadi sosai, tana zaune a waje kan kujera ta gaban swimming pool dan zafin yau yayi yawa, aka bude gate din gidan aka shigo, motar tayi packing ta bayanta, ya fito yazo inda take yace barka da hutawa, ta waiga taga adeel, ta amsa babu yabo babu fallasa, ganin hakan yasa ya sami karfin giwa, yace Zeena nazo muyi magana ne, bata amsa Shiba, shima hakan bai dameshi ba, yaci gaba da magana, Ina so inji mai kike bukata, ta dan tabe baki tare da fadin bana bukatar komai, yace ok babu damuwa ya ciro kudi yan dubu daya2 ya bata bandir biyar yace ga wannan ki saima su twins sweet, tace no ka barshi an gode, ya danji wani iri, amma sai yace ai bake naba ba, so baki da right din da zaki ce a barshi, tace amma ai...... Ya katse ta tare da fadin na wuce.........
Maryam obam✍✍