45to50

538 11 0
                                    

👩‍❤‍💋‍👩AMINIYA TA CE👩‍❤‍💋‍👩

       💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA 💁💁

Dedicated this page to yasmin darling 😘💃🏻
          4⃣6⃣to5⃣0⃣

Yayi tsaki tare da buga sitiyarin motarshi, yaja motar ya wuce, washe gari tun 7 ya fito, Ya nufi gidan da Zeena ta shiga, Ya zauna a mota har wajan 11 baiga kowa ya fito daka gidan ba, wajan 12 zaheer ya fito ya shiga mota ya wuce, abun ya kuma daure mishi kai, Ya dai yanke shawaran bari ya shiga gidan ya gani, Ya fito ya nufi kofan gidan, yayi nocking, a lokacin Zeena tana falo din, tana kallo, tasa wata top mai budaddan hannu ruwan yellow da skin tie, tace yes coming, jin kaman muryan Zeena yasa yaji dadi, Ya bude kofan ya shiga, bata waigo ba, balle taga wanda ya shigo, Ya kafeta da ido, tare da wani shaukin sonta da yake kuma shigarshi, jin kaman ana kallon ta, yasa ta waiga, da sauri ta tashi tare da fadin afraz, abun daya faru da ita lokacin da taje gidansu Mysha ta tuna, anya banga afraz ba lokacin ba kuwa, kodai shi ya kaini asibiti da nayi accident, kai anya bashi bane, domin in shine zai dawo duba ni, inma bai dawo ba ummi zata fad'a min, ya kafeta da ido, ganin irin kallon da yake mata yasa ta daure fuska, tare da fadin mai ya Kawo ka nan, mai kake so?  Yace Zeena ke nake so, ta d'aga mai hannu alaman yayi shuru, tace afraz plz ka fita, yace haba Zeena wlh sonki yamin yawa, plz ki tausaya min, ta kuma daure fuska tace afraz na fada Maka tun tuni bana sonka, ban son ganinka, koh ana so dole ne, Ya matso kusa da ita yace Zeena plz ki soni, ta bude baki za tayi magana yayi hugging dinta, ta kasa ko magana, sai zuciyanta dake ta buga mata, Ya fara mata magana kaman mai rad'a, Zeena ina sonki ina so ki zama matata, jin haka ta tureshi tare da yin baya, tace afraz I hate you, wlh ko babu maza a duniya gwara in mutu banyi aure ba, tana fadin haka tabar wajan da gudu, ya bita da kallo, dama akwai macen da zata 'kishi, duk kudin da yake dashi, ga kyau, tabbas sai a yanzu afraz yasan ba komai kudi zai iya samo maka ba, fita yayi yabar gidan cikin takaici.

Adeel yana zaune a falo yana kallo amma kwata2 hankalinshi baya wajan kallon, tunanin Zeena yake, Zeena kece komai nawa, bazan iya rayuwa ba tare dake ba, komai zai faru Zeena sai na mallake ki, yayi dan gajeran tsaki, tare da kara tsanan Mysha, jin maganan ta yayi tana fadin haba adeel tun dazu ina magana kayi banza dani, Ya kalleta yace inaji, tace ina so inje gidan mu, Ya sakar mata harara, tare da fadin ai babu ke babu fita, tace haba adeel wai mai yasa kake min haka, kwata2 baka kulani, kullum sai ka zauna kana bata lokacin ka akan tunanin waccen banzan Zeena mai take dashi wanda banda shi, Ya tashi tsaye rai a bace yace lallai Mysha sai yau na kara sanin ko ke wacece, bari kiji Zeena ta fiki kyau ta fiki tarbiya, ta fiki komai ki daina ma yaudaran kanki kina hada kanki da ita, ta fashe da kuka adeel ni fa matarka ce, kake yabon wata a kai na, kake nuna wata ta fini, ya kalleta yayi dan murmushi tare da fadin bazan taba kallonki a matsayin mata ta ba, Mysha yanda kika cuceni kika yaudare ni, kika barni cikin kunci haka zamu zauna ni dake, har Zeena ta kammala karatun ta in aureta, tace what adeel kasan mai kake fad'a kuwa? Yayi banza da ita ya haura sama ya barta a nan tana rusa kuka, tare da tausayama kanta.

Kullum afraz yana bin skul din su Zeena amma taki kulashi yayi naci yayi mitar amma duk a banza, gashi zasu fara exam a skul, dole ya koma London dan yayi exam, a na gobe zai koma yaje skul din su, a lokacin sun gama lecture ta fito zata koma gida, yau da kanta zata wuce don zaheer akwai inda zashi, ganinta yasa yayi sauri ya fito a mota ya nufeta, ganin yana nufota yasa ta daure fuska, bayan ya karaso ya kafeta da ido tare da fadin haba Zeena ke ko tausayi na, bakya yi, don Allah Zeena kiyi hakuri ki kulani, gobe zan koma nazo in miki sallama, ta kalleshi tace toh a sauka lafiya, taci gaba da tafiya, jin ta bashi amsa duk da cikin tsiwa tamai da gatsali, hakan yamai dadi, yaci gaba da binta Zeena ki taimaka kiban number dinki plz, ta daure fuska tace afraz dan Allah ka daina bina, bana so plz, yace shikenan amma ki bani number dinki, tace bazan iya ba, ganin haka yace toh muje in kaiki, shima tace bata so, daka karshe dai shiya bata tashi number din tare da rokonta ta kirashi, ta amsa da toh yana barin wajan ta yarda katin tare dayin tsaki.

Afraz ya koma London, sun fara exam amma kwata2 bai San abunda yake rubutawa ba, kullum da Zeena yake kwana yake tashi, yana mamakin irin azababban son da yake mata, amma yakan danganta abun da sakayya Allah ya mata akan abunda ya mata, yakan kara tausayin kanshi ya tabbata Zeena idan tasan shi ya mata fyade bazata taba kallonshi ba, yanzu Yama ya kare balle ace ta sani, ji yayi jikin shi yayi mishi sanyi, wayanshi dake gefe yaji yayi ringing da sauri ya dauka ganin sunan yasa ya dan canza fuska, domin yana tunani ko Zeena ce, Ya dauka tare da fadin hello mum, ta dayan bangaren ta amsa da hi, tare da fadin yakake, son kwana2 bana samin ka a waya ina ka shiga, yace mum naje Japan ne, tace Japan mai kaje yi? Yayi dan shuru can dai yace mum wlh ina sonta mum plz mum ki neman min auran ta, tace son wa kake so haka, yace mum Zeena, ta nanata sunan Zeena, a ina take yace a Abuja amma tana nan Japan tana karatu, tayi dariya tace toh kun dai daita ne, yace no mum bata sona, mum in ban sameta ba komai zai iya faruwa dani, jin irin yanda tilon d'anta wanda ta mallaka shi daya a duniya, yake magana hankalinta ya tashi, tace son karka damu koma yar gidan wanene ita zan nema Maka auranta, jin haka yace mum kin min alkawari, tace yes my son, kama fara Kiran kanka da mijin Zeena, yayi yar wata kara tare da fadin I love you mum, tayi dariya sannan sukayi sallama, ranan afraz ya kasance cikin nishad'i domin komai yake so iyayenshi suna bashi, gani yake kaman ma ya mallaki Zeena din.

Yau Sunday Zeena tana gida babu skul, tana kwance a d'akinta tana kallon sama, babu abunda take tunani sai adeel, ta rasa mai yasa kullum sonshi yake kara karuwa a ranta, duk kokarin da take don taga ta cireshi cikin ranta amma abun yaki, sai dai a kullum sonshi da yake karuwan mata, wani hawaye ne Ya zubo mata, adeel ina sonka, son da bazan iya musaltawa ba, duk da kunci amanata, ka barni da sonka a tare dani, kana tare da matarka ka manta dani, ta saki kuka mai karfi, taci kukanta babu mai rarrashinta don kanta tayi shuru, wayanta ta dauka ta kira daddy dinta, bugu daya ya dauka, yana jin muryanta yace Zeena kin yi kuka koh, jin tayi shuru ya tabbatar da hakan, yace Zeena har yanzu baki cire wannan abun a ranki ba koh, idan har kina son adeel kuma zaki aureshi ni dakai na zan nema miki auranshi, domin ban son abun da zai saki damuwa, jin haka tace dady a'a ka barshi, bai dace dani ba, inda yana so na da kanshi zai zo ya nemi aurena, mahaifin nata ya tausaya mata, yace Zeena ki dai yi tunani akai, tace toh dady su kayi sallama ta kashe wayan, tare da tunanin maganan da sukayi da daddy dinta, adeel ina sonka amma ka auri AMINIYA TA, wata zuciyan tace mata toh sai me, dan ya aureta, kawai in kina sonshi ki aureshi da wannan tunanin bacci ya dauketa.

Maryam obam ✍✍

AMINIYA TA CEWhere stories live. Discover now