51to55

595 24 0
                                    

👩‍❤‍💋‍👩AMINIYA TA CE👩‍❤‍💋‍👩

       💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA 💁💁

Dedicated this page to yasmin darling 😘💃🏻
          5⃣1⃣to5⃣5⃣

"tunda mum din afraz tayi mai magana akan zata neman mai auran Zeena ya cire duk wani fargaba da yake yi akan zai rasa ta, wannan ne Ya bashi da man yin karatu har suka kammala exam dinsu, kuma shine final year dinshi, zai zama cikakken engineer a quantity survey, a ranan daya gama exam din ji yayi kaman yayi tsalle ya gashi a Japan wajan Zeena domin yayi mugun kewanta, shi koda bata kulashi inya ganta ma dadi yake ji, amma dole yayi hakuri gobe tayi, yayi dan gajeran tsaki yaga dare ya mishi nisa ranan, washe gari da asuba ya tashi yayi sallah, sannan aka fara shiri, duk da wajan 10 zasu tashi yana Gama shiri ya nufi airport, Ya zauna kafin lokaci ya cika.

Zeena tana gida yau bata je lecture ba, ta online take dubawa, wayanta dake gefe yayi kara, ta dauka taga abda, tace little sis yakike, abda ta amsa da lfya tare da fadin ya skul, ta amsa da lafiya, wai yaushe zaki zo Zeena, nayi missing dinki, Zeena tayi dariya tace kaman da gaske, abda tayi dariya tace dagaske nake, Zeena tace in mun gama exam zan zo, mun kusa farawa, jin haka abda tayi kara tare da fadin kizo keda bros zaheer, kice na mishi mata, Zeena tayi dariya tare da fadin wa innan kananan kawayen naki, a ciki kika zaban mai, ta dan turo baki kaman Zeena din tana gabanta, tace haba Zeena yanzu fa ina jss3 going to ss1 kinga ai ba za'a kirani da karama ba, Zeena tayi dariya sosai tace abda baki da dama, tace ina ummi abda tace tana kitchen Zeena tace takai mata Wayan, ta amsa da toh, ta nufi kitchen din taba ummi, bayan ta amsa suka gaisa tace ummi daddy ya fada miki wata magana, tace a'a maganan mai nene, tace akan adeel, ummi tace Zeena har yanzu baki cireshi a ranki ba, tayi shiru, ummi taci gaba da fadin ya kamata kima kanki fad'a, kara girma kikeyi Zeena ya kamata kisan abun da zai yiwu da wanda bazai yiwu ba, ki cireshi a ranki ki fara kema rayuwanki, tace toh ummi, tana fadin haka ta kashe Wayan, tabbas abunda ummi ta fad'a haka ne, Ya kamata ta cire adeel a ranta, amma ta yaya hakan zai faru taya zata cireshi, bayan kullum son shi kara karuwa yake a ranta, wani hawaye ya biyo kuncinta, adeel ka cuceni kaida Mysha kuna can kuna jin dadin rayuwanku kun barni cikin kunci da bakin ciki, sonka yamin yawa, mai zanyi sonka ya fita a raina, Allah sarki Zeena rashin masoyi babu dadi.

Afraz an sauka a kasar Japan, wani farin ciki yake ji tare da nishad'i yazo kasar da masoyiyarshi take, kai tsaye hotel ya nufa ya ajiye kayanshi, Ya fad'a toilet yayi wanka, bayan ya fito ya shirya cikin kananan kaya, yayi kyau sosai, kai tsaye gidansu Zeena ya nufa, yayi nocking, aka bashi izinin shiga, fatima ya gani wacce take kula da Zeena, Ya gaidata cikin harshen hausa da mamaki take amsa wa, don a zaton ta baya jin hausa don baiyi kama damai jin hausa ba, zata iya kiranshi da bature ko balarabe, Ya katse ta tare da fadin dan Allah Zeena nake nema, tace tana baya, ta nuna mai hanyan da zaibi, Ya shiga ya ganta cikin wani yar bukka, ta zabga uban tagumi, duk sai yaji wani kala kasancewan ya ganta a haka ya tabbata tana cikin damuwa, Ya matsa kusa da ita, Ya cire mata hannun, ganin afraz yasa tayi saurin tashi tare da fadin maiya Kawo ka nan, yace Zeena dan Allah ki tausayamin wlh Zeena ina sonki, tayi tsaki tare da fadin nace bana sonka wai afraz dole ne, ya kafeta da ido tare da fadin Zeena nasan abun daya faru da kike tunawa wlh Zeena na canza yanzu ba haka nake ba, tayi shuru bata kulashi ba, Ya matsa kusa da ita, tare da daura hannunshi kan kafadan ta, Zeena kece farin ciki na kece komai nawa, ganin bata kulashi ba ya janyota tare da rungumeta, babu abunda kake ji sai saukar numfashin su, sunyi wajan minti uku a haka, yace Zeena plz ki soni kaman yanda nake sonki, taja da baya tare da fadin afraz you will never change, who give you the right to touch me, let me tell you one thing,  niba kalan yan iskan yan matanka din nan bane, so you better respect your self and leave, idonshi ya canza kala, Ya kuma matsawa yana fadin Zeena plz kiyi hakuri ki soni, tace nace bana sonka I hate you, yayi dan murmushi yace Zeena ko kina sona ko baki so na saina aureki kota wani haline, this is a promise, Ya fara tafiya tace afraz ya tsaya ba tare daya waigo ba, tace kace saika aureni koh, to bari kaji dana aureka gwara in mutu, ya waigo tare da matsowa kusa da ita, Ya janyo ta, ganin yanda ya daure fuska yasa ta kasa magana, Ya matsa da bakinshi kusa da nata kaman zaiyi kissing dinta, komai Ya tuna kuma ya fasa ya tureta ya fita, ta fashe da kuka tare da fadin wai mai yake shirin faruwa da ita ne, ta gefe daya ga adeel wanda take mutuwar so, tunanin shi ya hanata komai, ta dayan bangaran kuma afraz wanda yake takura mata, haka ta zauna taci kukanta, ta tashi ta shiga d'akinta.

Tunda wannan abun ya faru bata kara ganin afraz ba, hakan ya mata dadi, shima afraz din a washe garin ranan ya koma Nigeria, domin yaga inya biyema Zeena zai iya rasa ta, iyayenshi sunyi mamakin ganin yanda d'an nasu ya rame lokaci daya, sunyi mai tambayoyi afraz ya taso bai saba da karya ba, komai munin abu indai yayi in suka tambayeshi yana fada musu gaskiya, yace mum Zeena nake so ku nemo min auran ta, dady dinshi yace wannan wani irin sone afraz haka, wannan ne karo na farko daya ma iyayenshi karya tare da boye musu abu, Ya fada musu yanda suka hadu da Zeena amma bai fad'a musu ya mata fyade ba, daddy dinshi yace karka damu yar gidan waye, yace yar gidan senator abubakar daura ce, yace ok shikenan zanje gobe muyi magana dashi, yace thank daddy, Ya tashi yabar wajan cikin murna.

Zeena ta fito daka wanka taji karan wayanta da da sauri ta dauka, taga number ne, ta dannna tare da fadin hello, ta dayan bangaran aka amsa da Zeena, jin muryan tayi ya bugan mata dodon kunne, muryan da take burin ji take son ganin mai muryan, yace Zeena plz kiyi min magana, mai makon magana sai ta fashe da kuka, hankalinshi ba karamin tashi yayi ba, yace Zeena dan Allah ki daina wannan kukan, tace adeel mai yasa ka kirani, yace Zeena na kiraki in fad'a miki har yanzu ina sonki, son da nake miki bazan iya yima ko wace mace ba, plz Zeena ki yarda dani banci amanarki ba, jin haka tace adeel plz ban son wannan maganan, yace shikenan Zeena, amma ina so ki sani ina jiranki har ki gama karatun ki, Zeena ke daya ce macen da nake so kuma nake so in mallaka, kullum da sonki nake kwana nake tashi ta kashe Wayan da sauri, Zeena tayi shuru ta kasa furta ko kallama daya, wai mai yake shirin faruwa ne, Don son adeel tana yi amma mijin AMINIYA TA CE,  hmmmm muje zuwa.

Maryam obam✍✍

AMINIYA TA CEWhere stories live. Discover now