120to125

467 11 0
                                    

👩‍❤‍💋‍👩AMINIYA TA CE👩‍❤‍💋‍👩

       💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA 💁💁

Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
   1⃣2⃣0⃣to1⃣2⃣5⃣

Mysha ta tashi da sauri tabar wajan, ganin haka Zeena yasa itama tace ma adeel ta koshi, yace ki kara ci kad'an, tace no, ka barshi jin ihun Mysha sukayi, da sauri adeel yayi d'akin, yana fadin lafiya Mysha mai nene, tace ciki na, yace mai ya sameki tace murd'a min yake, yace tashi muje asibiti, tace bazan iya ba ka taimaka min, yace ina zuwa yana fita tayi dariya tare da fadin yau kwanan kine Zeena amma ni zan amshe, Jim kadan sai gashi da Zeena din sun shigo, ta kuma langwabe wa, adeel yace Zeena ta dauki ahmad ta kaishi d'akinta ta amsa da toh, ta daukeshi ta kaishi, shi kuma adeel ya dauki Mysha yayi mota da ita, kai tsaye asibiti suka nufa, an duba ta, aka bata magani suka dawo gida wajan karfe goma da wani abu, a lokacin Zeena harta fara bacci, taji kaman ana taba ta, da sauri ta tashi taga adeel tace har kun dawo ya jikin nata, ya amsa da sauki sannan ya dauki ahmad, ya fita, tunda ya fita bai dawo ba, daka yazo zai fita Mysha taita nishi, ganin haka saiya dawo ya zauna da ita, ita kuma Zeena baccin ta tayi abunta, sai wajan asuba tayi bacci sannan ya fita masallaci, yayi sallah, bayan ya dawo ya duba ta yaga tana ta bacci, kai tsaye d'akin Zeena ya nufa, yaga tana sallah,ya zauna akan gado, harta idar bata tashi ba taci gaba da zama akan dadduman, ganin bata da niyan tashi yasa yazo inda take ya zauna a 'kasa ya kamo hannunta da take wasa dashi, yace Zeena kiyi hakuri kin jini shuru sai yanzu ta samu tayi bacci, tace babu komai ta tashi ta haye gado, ganin haka shima ya haye gadon ya janyota jikin shi,ya manneta kaman zata gudu, da haka bacci ya dauke shi, ganin yayi bacci yasa ta zame jikinta cikin nashi ta nufi kitchen don ta had'a breakfast, ta had'a farfesun fresh fish, tayi sandwich da tea ta jera kan dinning ta koma dakinta taga har yanzu yana bacci, ta fad'a toilet tayi wanka ta shirya cikin wasu kananan kaya Riga da wando tayi kyau sosai duk da batayi makeup ba,ta fashe jikinta da turare sai kamshi ke tashi, ta koma falo dinta ta zauna tana kallo, sai wajan 10 ya farka yaga bata kusa ya shiga toilet shima ya fito ya shirya, ya ganta a falo tana kallo wani sonta yake shigar shi, musamman shigan da tayi wanda ya rud'a shi, tabbas Zeena ta hadu, jin kaman ana kallon ta yasa ta waigo, suka had'a ido ya sakar mata murmushi tayi sauri tayi kasa dakai, ya matso kusa da ita tare da janyota jikin shi, suna shakan numfashin juna, ta kasa ko motsi, yasa hannunshi ya d'ago mata kai, ya kafeta da ido itama ta kasa, 'kasa da kanta jin bakinshi tayi cikin nata sun dauki lokaci cikin haka kafin ya sake ta, ta fara mayar da numfashi ta kasa ko tashi dan gaba daya ya kashe mata jiki, jin hannunshi tayi cikin kirjinta tare da kara rungumota, ganin dagaske yake yasa tace breakfast is ready, yayi dan murmushi ya matsa kusa da kunne ta, yace kece abinci na, ta dan tureshi ya kuma yin dariya ganin yanda take daure fuska, yace Zeena ina sonki, nan taji gabanta yana bugu da sauri ta tashi tayi bedroom dinta nan ta saki kuka, jin ta dade bata fito ba, yasa ya bita yaga tana kuka yace lafiya kuwa Zeena tayi shiru babu amsa, ya matsa kusa da ita tare da fad'in ban San kukan ki Zeena plz, nan ta kuma jin wani hawayen sau da yawa adeel yana mata abubuwa shigen na afraz, dakyar ya samu tayi shuru, suka fita falo don yin breakfast,baiga Mysha ba yasan tana bacci har yanzu dan haka baiko leka d'akinta ba suka fara yin breakfast.

Mysha itama tuntuni ta farka taga adeel baya wajan tayi dan tsaki yanzu saida yaje d'akin waccen mayyar, wani bakin ciki taji yana damun ta, yanzu duk abunda na shirya a banza tayi tsaki ta tashi, ta fito falo taga Zeena da adeel suna cin abinci suna fira cikin Jin dadi, nan ranta ya kuma baci ji take kaman ta shage Zeena dan takaici, adeel yace Mysha har kin tashi ta amsa da eh, nan Zeena tace ya jikin, tace da sauki kiyi hakuri naso in taso in taya ki aiki, bacci yaci karfina, adeel yace keda baki da lafiya Mysha ina ke ina tayata aiki, Zeena tace lallai Mysha ke daban kike, nan Zeena ta dan fahimci wani abu, anya ciwon Mysha ba karya bane kuwa, inma karya tayi tama kanta, amma zan nuna mata tayi kuskure, Mysha ce ta katse ta tare da fad'in ahmad jiya baiyi miki kuka ba, Zeena tace a'a aini yara suna sona, Mysha ta turo baki tare da fadin Allah sarki, Zeena ta kalli adeel wanda bini2 idonshi na kanta, tace ya kamata inje inga su twins, nayi missing dinsu, adeel yaji dadin wannan maganan dan dama yana neman dama ne da zasu fita shida Zeena, yace ok dama zan fita yanzu ki shirya sai in kaiki, jin haka Mysha tayi caraf tace nima bari in shirya muje tare, yace no keda baki da lafiya ina ke ina fita, tace na warke ai, yace kiyi hakuri ki zauna kar kije abun ya kuma tashi, haka ta hakura dan babu yanda ta iya, don idan ta matsa zai gane karya takeyi, Zeena ta tashi taje ta shirya cikin wani atamfa dinkin riga da skirt ya mata kyau sosai, tasa gyale kalan kayan, ta fito falo, adeel ya kalleta yace ta koma tasa hijab indai tana so ta fita, nan taji wani hawaye na shirin zuba daka idonta, da sauri ta koma tasa hijab, suka fita, Mysha kaman zata fashe dan bakin ciki, tace kuje Ku dawo zan nuna miki naki kadan ne Zeena.

Hotel ya nufa da ita, bayan sun shiga yace ta fito su shiga, bata musa ba ta fito, yaje yayi komai da komai ita bata san mai yake yiba, dan tana zaune nesa da inda yake, yazo yace suje ta bishi,  wani d'aki suka shiga taga ya zauna akan gadon d'akin sai a sannan tace mishi mai suka zoyi nan, ya tashi yazo kusa da ita ya fara cire mata hijab din jikinta,ganin haka gabanta ya fara fad'i, harya cire hijab din, ya cire mata rigan jikinta, tace adeel M.....  Kafin ta karasa abunda take son cewa yasa bakinshi cikin nata, nima ganin haka na fita na basu waje,

Mysha tunda suka fita take ta zarya ta kira adeel bai dauka ba, tayi tsaki yanzu hala suna can tare suna cin Amana na, wani haushin Zeena take ji, gashi plan dina na jiya bai yiba, tunda ya koma d'akinta ya kwanta, tayi dan dariya tare da fadin Zeena sai nasa adeel ya wulakanta ki, da kanshi zai koreki,.

Zeena tana toilet tana wanka tare da hawaye, shi kuma adeel yana kwance kan gado cikin nishad'i, tabbas mata suna suka tara kuma ko wace mace tana da nata baiwar da Allah ya mata, har Zeena ta fito ta ganshi a kan gado suka had'a ido tayi sauri tayi kasa dakai wani irin kun yanshi, take ji, yayi murmushi ya matso kusa da ita, yayi hugging dinta, tare da fad'a mata I luv u Zeena, you are my happiness, jin tayi shuru yace bari insa miki kaya ta saki kuka yace mai nene, tace bana so zansa dakai na, yayi dariya ta diba kayanta tayi toilet, ya bita da kallo yana dariya harta fito fuskanta a daure yace mai nene kuma, tace kayana duk ya yamutse, taya zani gidan mum a haka, yace ai yau babu zuwa gidan mum gida zamu koma, tace plz ka kaini, yace a haka, tayi shuru can tace toh ka kaini gida in canza kaya sai muje, yayi dariya tare da fadin zan dauko miki twins in Kawo miki su, ba karamin dadi taji ba, suka koma gida, sunga Mysha a falo tama Zeena kallon sama da kasa, tare da aiyana wa a ranta, anya ba wani waje sukaje ba, dubi yanda adeel yake ta wani zumudi sannan bada wannan kayan ya fita ba, ita kuma Zeena kayanta ya yamutse ta kasa, nan taji kirjinta yana buga mata, ta daure tace har kun dawo nasha aiko dasu twins din zaku dawo, Zeena ta fahimci tana so tasan daka inda suke ne, tace eyya ai bamu samu munje ba, munje wani waje ne, nan Mysha ta kumbura, adeel yabar wajan yayi gefen Zeena ganin haka Mysha ta taso taje gaban Zeena tace ina kukaje, Zeena ba tare da tsoro ba tace hotel muka je, dan bama son takura, wani kululun abu ne ya tsaya mata a wuya, ta cakumi wuyan Zeena.

Maryam obam✍✍

AMINIYA TA CEWhere stories live. Discover now