55to60

598 21 0
                                    

👩‍❤‍💋‍👩AMINIYA TA CE👩‍❤‍💋‍👩

       💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA 💁💁

Dedicated this page to sayyada darling 😘💃🏻
          5⃣6⃣to6⃣0⃣

Mahaifin afraz bayan ya shiga d'aki ya dauki waya ya kira mahaifin Zeena, a lokacin mahaifin Zeena yana zaune a bedroom dinshi yana kallon news, yaji karan wayanshi, Ya dauko ganin sunan mai Kiran yasa ya dauka da sauri tare da fadin ranka ya dade barka da dare, mahaifin afraz ya amsa da yauwa, bayan sun gaisa mahaifin afraz yace mai gobe kana gida, Ya amsa da eh ranka ya dade, yace insha Allah gobe zanzo da yamma, mahaifin Zeena yace ranka ya dade lafiya dai koh, yace eh lafiya, mahaifin Zeena yace aida ka bari ni nazo da kaina, yace a'a karka damu zanzo da kaina, yace toh ranka ya dade sai na jika, sukayi sallama, bayan ya kashe Wayan yace lafiya kuwa alhaji umar na sidi yake son gani na, mahaifin afraz yana daya daka cikin manyan mutane a Nigeria, bama Nigeria ba kawai duk Africa, babu inda zaije yace yana son abu ba'ayi mishi ba, baya ga siyasa da yayi shi babban dan kasuwa ne, ranan mahaifin Zeena da tunanin zuwan alh umar na sidi yayi bacci.

Zeena na kwance karar wayanta ne ya tashe ta, ta dauka tare da fadin hello cikin muryan bacci, jin muryan adeel yasa ta watsake, yace Zeena badai ni na tashe ki ba, tace a'a dama yanzu nake son in tashi, jin kaman ta dan sake, yasa yaji dadi, tare da fad'a mata yana so yazo Japan akwai maganan da yake so suyi, tace no adeel plz karka zo ka zauna kawai, yace Zeena kin San yanda nayi missing dinki kuwa? Tayi shuru yaci gaba da fadin da kin San yanda nayi missing dinki da baki cemin haka ba, Zeena na tabbata kema kina kewa na, tayi shuru dai bata kulashi ba, shi daya yake ta maganan shi, yace Zeena plz kimin magana, tace ina jinka, ta rasa mai yasa ta kasa fushi da adeel har take sauraranshi, ganin kaman bata son magana yasa yace gobe yana nan tafe, bai jira mai zata fad'a ba ya kashe wayan, wani farin ciki taji,tare da son ganin adeel, domin itama tana son ganinshi, lokaci daya kuma ta canza fuska, tare da tuna abun da ya faru, adeel kamin nisa yanzu ka auri AMINIYA TA, bazan iya auranka ba, tayi shuru na wajan minti biyar, can tayi tsaki tare da shirin zuwa skul.

Wajan karfe biyar mahaifin afraz yazo gidansu Zeena,tare da wani abokinshi aka saukesu a falon baki, sannan aka cika su da kayan ciye2, bayan sun gaisa cikin girmamawa, mahaifin afraz yace alh abubakar, nazo neman alfarma ne, Ina nema ma d'ana afraz auran yarka Zeena, mahaifin Zeena yace haba ranka ya dade ai kai ka wuce wannan, na bama danka auran Zeena, sukayi godiya sannan abokin mahaifin afraz yace a yanke musu sadaki su biya mahaifin Zeena yace Su bada dubu hamsin, nan da nan yaje mota ya dauko wani akwati da kudi cike a ciki, yace ga wannan 50million ne ni na kara akan sadakin, sukayi godiya sannan mahaifin afraz ya kuma neman alfarma akan yana son a daura auren nan da sati biyu, mahaifin Zeena yace babu matsala, sukayi sallama suka wuce.

A lokacin da dadyn Zeena ya shiga gida, Yama mahaifiyar Zeena din bayani kuma hakan ya mata dadi, domin tana ganin idan tayi aure hakan zai sa ta cire adeel a ranta, sannan tace kar'a fad'ama Zeena din maganan auran, domin karta sama kanta damuwa, tunda ta kusa zuwa in ta dawo sai mu mata bayani, daddyn Zeena ya yarda da shawaran matar tashi.

Adeel ya sauka a kasar Japan, kasancewan yana da address din gidansu Zeena din, Ya nufi gidan amma yayi rashin sa'a tana skul, yace bari yaje ya dawo, hotel ya nuna ya fada toilet yayi wanka, yasa kananan kaya, sannan ya fashe jikinshi da turare, Ya zauna tare da jiran anjima kadan yayi ya koma gidansu Zeena din, sai murmushi yake shi daya.

A lokacin da Zeena ta dawo fatima ta fad'a mata anzo nemanta bata nan, bata damu da ko waye ba, tace ok, ta nufi dakinta tayi wanka, tasa wata doguwan riga, ta dauki littafinta ta nufi bukka, don karatu gobe zasu fara exam, littafin dai yana hannunta kuma inka ganta zaka rantse shi take karantawa, amma tunani take, ganin adeel tayi ta gabanta yana murmushi sai taga kaman gizo, yake mata, tasa hannunta tare da taba fuskanshi, taga bai bace , ta tabbata dai shi dinne, tayi sauri ta cire hannunta, tare da fadin adeel yaushe Kazo? Yayi murmushi tare da fadin tun dazu, ya kura mata ido, yaga ta kara girma da kyau wani sonta ne yake kara shigarshi, itama ta nata ban garan, wani sonshi ne yake kuma shiganta, dukansu sunyi shuru suna kallon Juna, ya katse shurun tare da fadin Zeena kina sona kuwa kaman yanda nake sonki, jin haka yasa ta fashe mishi da kuka, hankalinshi yayi mugun tashi, yace Zeena plz kibar wannan kukan kar ki sani cikin damuwa, tace adeel mai yasa ka gujeni, a lokacin da nake bukatan ka, sannan kuma yanzu ka dawo zaka kara yaudara na, yayi sauri ya rufe mata baki da hannunshi yace Zeena ban yaudareki ba, Zeena kece macen dana fara so, kuma har yanzu banga wacce nake so ba sai ke, Zeena Mysha ce ta rabamu akan selfishness nata nan ya bata labarin yanda sukayi da Mysha, tayi shuru babu abunda take sai hawaye, ta kasa furta komai, ganin haka shima yayi shuru yana kallonta, ganin yanda take kuka bazai iya jure ganin kukan ba, Ya matsa kusa da ita, Ya fara share mata hawayen, tare da fadin plz kibar wannan kukan, jin haka tayi shuru, wani sonshi taji ya kuma karuwa a ranta tare da tausaya mishi, tabbas  komai Ya faru laifina ne, inda ban Kawo maganan karatu ba da yanxu munyi aure, da hakan bai faru ba, a yanzu ta yarda bazata iya auran ko wani namiji ba inba adeel ba, domin shi daya take so, shima yana sonta, a ranan Zeena ta sake da adeel kuma tace mishi a shirye take data aureshi, hakan yamai dadi, sannan tace karya sake ya saki Mysha domin tana sonshi kuma komai tayi sonshi yasa tayi hakan, yace babu komai duk abunda tace shi zaiyi, daka karshe yayi mata sallama ya wuce masaukin shi, ranan su duka sun kwana cikin farin ciki.

Maryam obam✍✍✍

AMINIYA TA CEWhere stories live. Discover now