PART 2

444 16 3
                                    

Abun gwanin ban tausayi Haka Humaira taita faman tsala ihu Amma Kande ko a jikinta, Dan kuwa haka kawai Allah ya d'aura Mata tsanan 'yar, tunda taga Malam Habu ya fita Dan Nemo mata Madara Kande ta dungurar da ita ta cigaba da abunda takeyi.
  Humaira kuwa Tasha kuka tamkar ranta zai fita Sai faman tura yatsunta take cikin Baki saboda tsananin yunwa.
Dak'yar Malam Habu ya samo tsaftacacciyar Madara wacca bazata cutar da ita ba ya d'auketa ya Bata, sosai Humaira takeshan Madarar Nan tamkar wacca ta shekara bataci abinci ba, Kande tana gefe tana faman ta6e Baki had'e da hararar ta.

Sa'eed ganin Maryam ta shiga Nata part d'in yasashi D'aukar waya Dan Kiran mahaifiyar Hafsa, ringing d'aya zuwa biyu ta d'auka tace "Son ina fatan lafiya k'alau?"

Sa'eed yace "Yanzu Ina zaune Naga Hafsa ta dawo, Kuma na lura Babu ciki a jikinta ina kyautata zaton ta haihu ne taje ta Yar da abunda ta haifa kamar yadda Kika Umarceta"

Tace "Ka tabbata ta haihu?, Kuma bbyn baya gidanka?"

Sa'eed yace "Ah Umma, Dan Naga alama"

Mahaifiyar Hafsa Tace "Shikenan, karka sake kabi ta kanta har sainai maka umarni dakai Mata magana, ka kyaleta karka sake ka nuna Mata tausayi ko kad'an, so nake ta d'and'ana gud'arta tunda taso ta tozarta Family d'inmu akan wani k'aramin daliinta, ka shareta Zan kirata maybe zuwa anjima"

Sa'eed yace "Umma!, Dan Allah a d'aga ma Hafsa k'afa haka man, d'an Adam ajizine, Nina Baki labari nida Naga komai wallahi abun ya dad'e da wucewa a wajena wannan K'addarar rayuwartace, saboda Hafsa nayi Imani bazata iya aikata hakan ba kawai k'addara ne, wallahi ruhinta Yana cikin wani Hali, Umma nasan Hafsa tun kafin ta mallaki hankalin kanta bana tunanin da San ranta hakan ta faru..."

Dakatar dashi ta hanyar cewa "Sa'eed ka kiyayeni wallahi, banaso kana kawomin problems a Wannan lamarin, waya fad'a maka ana shaidar d'an yau?, To ka fita idona na rufe, mu Hafsa zata tozarta ta 6ata Mana sunan Family, ta 6atama mahaifinta siyasarsa, Kai da badan kayi Dace da mace tagari irin Maryam ai da tuni tayi yamad'id'i da wannan lamarin, Amma da yake matar rufin asiri ce wa kata6ajin kaji yace yaji Wannan mummunan aika-aikan da Hafsa tayi, ka barni da ita wallahi sai tasan mu ta tozarta, aini naso ace ka zanemin ita ka canza Mata halitta a lokacin sannan ka had'ata da takardar saki tunda Bata da mutunci, wallahi ka kiyayeni Sa'eed kayi abunda na sakaka, ka manta cewar k'anwar kace Kuma matarka a matsayina na wacca ta ruk'e ka Kuma uwa a gareka, in Kuma ka nunamin ban Isa ba Shikenan"

Sa'eed cikin rashin jin dad'in kalaman Umma yace "Amma Umma..."

Sauri tayi ta katseshi da cewar "Amma me?, Kaga banason dogon magana kayi abunda na sakaka kawai"

Sa'eed yace "Shikenan Umma, saidai Ina tsoron Kar Hafsa wani mummunan Abu ya faru da ita ganin yadda kowa ya juya Mata baya, Kuma ke Kanki kinsan Hafsa akwai hak'uri da zurfin ciki"

Cike dajin haushin maganarsa Tace "Am so what, ta mutu Mana, inta mutu inada asara ne, ai Alhamdulillah tunda ba ita kad'ai gareni ba, Ni wallahi Na fara gajiya da maganarka nidai kayi abunda na sakaka", katse kiran tayi ta zauna jugum tausayin 'yarta ya cika Mata zuciyarta, rabon data sakata a Ido tun Randa mummunan abunda ya faru agareta, ta tuna yadda sukai Mata kaca-kaca ita da yayyinta tare da Allah wadai da rayuwarta, ta tuna lokacin da Hafsa take kuka tana rok'on su su saurareta amma Babu Wanda ya kalli inda take, ranar dukan mutuwa akai Mata, Sa'eed ya gwada cetont duk da shima Yana tsananin jin haushinta a zuciyarsa Amma Umma ta dakatar dashi, lumshe idanuwanta tayi cike da sanyin murya Tace "Ta hakane kawai Sa'eed zaisan nai Masa adalci, tunda nayi-nayi ya rabu da ita Amma yak'i, nasan saboda nine ya kasa hakan, Lallai Sa'eed d'an haalak ne, Allah ya jik'an mahaifiyar ka Hajiya Hauwa Kuma K'anwa gareni, Allah ya albarkaci rayuwarka Dan kuwa ba k'aramin rufa Mana asiri kayi ba, Hafsa ke Kuma Allah yasa ki Gane gaskiyar lamarin na D'aukar mataki da mukai a Kanki Kar kice ba muyi Miki adalci ba", shiru tayi ta kwanta tunanin Hafsa ya mamaye Mata zuciyarta tana tunanin komai ta Haifa oho.

GARARIN RAYUWAWhere stories live. Discover now