PART 10

273 19 3
                                    

Asubar fari Humaira ta tashi saboda sanyin da takeji, tashi tayi Tai alwaka da ragowar ruwanta duk da bashi da yawa Tai sallah, ganin ko kad'an Bai Dace tana yawo Babu Hijab ba tafara dube-dube, ganin labule Mara nauyi Wanda ya d'an Sha datti ta d'auka ta rufe jikinta ta k'ara kutsawa cikin kasuwar, tuni ta fito Titi tana kalle-kalle, ganin mutane sun fara shawagi, ga wata yunwa datakeji, ganin wani gu ana soya waina yasata ta nufa wajan ta raku6e tana had'iyar yawu, can ganin zaman bazai Mata ba yasata zuwa inda matar take, fuskarta abun tausayi Tace "Dan Allah in Miki wanke-wanke ki bani abinci naci?" Ta fad'a muryarta a raunane.

Matar kallanta tayi tsaf Tace "Keko Baiwar Allah daga ina Haka da sassafe?"
Humaira Tace "6acewa nayi Kuma na rasa hanyar gida, in Miki wanke-wanken Zaki bani abinci" ta fad'a cike da k'osawa.

Jinjina Kai tayi Tace "Yanzu dai wanke-wanken Bai Gama had'uwa ba, zauna ki jirani Bari a zuba Miki sai kici zaki fijin dad'in aiki"

Humaira farin ciki ne ya mamaye Mata zuciya ta fara yi Mata godiya, Zama tayi dirsham a k'asa tana jiran ta kawo mata abincin taci.
    Sosai Humaira takecin abinci hannu baka hannu k'warya, har Saida ta tabbatar ta k'oshi, sannan ta koma ta zauna tana jiran Tai Mata wanke-wanken.
Bayan awa biyu zuwa uku Hajiya Atika ta loda Mata uban wanke-wanke, kallan Humaira tayi wacca ta fara gyangyad'i Tace Mata "Tashi kiyi wanke-wanke sun had'u"
  Humaira tana ganin Uban wanke-wanken Nan Saida ta had'iye yawu ji kake "Muk'ut" ba musu ta tashi ta farayi Mata wanke-wanke, sosai Humaira ta jigata, Dak'yar ta samu ta gama wanke-wanken Nan ta zauna a wajan tana jiran na Rana.
Wunin ranar dai Humaira a wajan tayisu, ganin ta cika cikinta yasata tashi ta k'ara kutawa wani wajan, primary ta hango ana k'ok'arin rufeta, ta waiga taga nanne kawai zata kwanta hankalinta kwance, tuni ta sad'ad'a ba tare da Mai gadi ya ganta ba taje can seat d'in baya ta kwanta a benci tare da sauke nannauyiyar ajiyar zuciya, Haka ta kwanta Babu fargaba ko tsoro a tare da ita.
   _*Asuba ta gari Baiwar Allah*_

Hafsa ganin kuka bazai ta6a dawo Mata da 'yarta ba yasata fawwalawa Allah lamarin, ta fara Kai kukanta wajan Ubangiji akan Allah ya tsareta ya kareta a duk inda take, sosai take tausayin 'yarta gashi duk ta rame Yanzu saboda tunanin halin da zata tsinta kanta, Sa'eed kuwa yayi magiya akan tayi hak'uri ta sauraresa Amma Ina tak'i bin ta kansu dagashi har Mamanta saboda kamar sune silan faruwar Wannan abun.

Humaira bud'e fuskarta ta farayin jin kamar hayaniya a makarantar, tana lek'awa ta window taga ana musu assembly, Haka kawai taji sun burgeta "ko menene wannan Kuma oh" cewar Humaira murmushi shinfid'e a fuskarta, k'ara gyara Zama tayi Tanajin yadda suka juye harshensu izuwa na turanci, murmushi tayi ta tsaya tana kallansu, ba tare data ankara ba sai ji wasu Yara sun saka Mata ihu suka wurga waje a guje tare da Kiran headmaster, ai tuni cikin Humaira yayi wata k'ara saboda tsoro sai faman zazzare Ido kawai takeyi, ai bata Gama tsorata ba Saida ya ganshi da bulala, ai tuni ta fara matsar hawaye tare da Basu hak'uri, akan ta tuba bazata k'ara ba.

Headmaster yayi mamakin ganin k'aramar yarinya ta kwana a wajan Nan ba tare da tsoron komai ba, ganin yadda ta rud'e ne yasashi sassauta muryar sa yace "Ke Kuma daga Ina?"

Waige-waige ta farayi ganin yadda student d'in class d'in suka kafeta da idannunsu, cike da matuk'ar tsoro Tace "6acewa nayi, na kasa Gane gida" ta fad'a hawaye na sauka akan kuncinta.

Tuni taba headmaster tausayi, kallanta yayi yace biyoni, ba musu ta bishi a baya yayinda taita faman waige-waige, ganin yadda 'yan class d'in suke Mata dariya, Haka ta bishi, direct staff room yakaita wajan sauran teachers d'in makarantar, kallansu yayi yace "Anan ta kwana, na Tambayeta inane gidansu Tace bazata iya ganewa ba, Yanzu dai menene mafita?"

Wata Malama ce wacca ake kiranta da Malama Zainab Tace "Abu mafi sauk'i a kaita gidan me anguwa ko Mai gari, su zasusan yadda zasuyi da ita"

Kowa Saida yayi amanna da wannan shawarar data bada, ba musu wasu daka cikin Malaman da sukasan gidan Mai anguwar layin, sukace Bari su kaita ai mishi bayani, har sunyi gaba Humaira taja Tanga ta tsaya ta kalli headmaster Tace "Dan Allah Baba inason in runk'a zuwa makarantar Nan bansan komai ba game da Boko, na Arabic matar data ruk'e nice ta koyamin kasancewar masaniya ce"
  Tuni taba Malaman tausayi, headmaster ne yayi gyaran murya yace "Karki damu, duk yadda Mai anguwa ya yanke nida kaina Zan d'inka Miki uniform in sakaki a makaranta mai kyau Mai sauk'in kud'i"

GARARIN RAYUWAWhere stories live. Discover now