PART 14

233 12 0
                                    

Hafiz a tsorace ya girgiza ta Amma Ina Bata motsi, ganin har yanzu kumfa na fita ta bakinta yasasu k'ara tsorata gashi komai nata ya tsaya cak, Mai Gari ne yayi k'arfin halin cema Hafiz "Maza jeka kiramin Liman wannan abun kamar sammu ne"
  Hafiz cike da tashin hankali yace "Baba kamar fa ta mutu fa, komai nata ya tsaya cak"
Mai Gari yace "Kayi abunda na sakaka tun kafin ka salwantar Mata da Nata ran, kace ya taho cikin gaggawa"
Tuni Hafiz ya saketa ya tafi cikin sassarfa, yayinda Mai Gari Yana zaune yana tattofa Mata addu'o'i, ba'a d'auki lokaci ba saiga Liman da Hafiz, ai tunda Liman yaga Humaira yace ayi gaggawar Kiran sarkin Aljanu, kafin kace mene sai ga sarkin Aljanu ya bayyana, sarkin Aljanu Bai tsaya sauraransu ba ya fara aikinsa, kafin kace mene Humaira ta fara wani irin ihu tana kururuwa tare da fizge-fizge, sai wata irin mik'a takeyi, tana wuru-wuru da Idanu, kowa na wajan Saida sukaja da baya Banda Sarkin Aljanu, sosai yayi iya bakin k'ok'arin sa, wajan ya samu ya fafata da mugayan Aljanun da aka turo matasu dansu halakata, Dak'yar ya samu nasara akansu saidai Abu d'aya ne ya gagaresa taimaka Mata shine jinta, yadda sukayi nasarar kurmantar da ita, duk da yayi alwashin taimakon ta ta ko wani irin Hali.
   Ganin Humaira ta samu bacci yasashi kallan Mai Gari yace "Wannan fa?"
Mai Gari gyara malun-malunsa yayi yace "d'iyata ce"
Ajiyar zuciya sarkin Aljanu ya sauke yace "Tabbas tana cikin matsala ba k'arama ba, Dan a halin yanzu kasheta akaso ayi sai Allah bai nufa ba kasancewar tana da addini a kuma tsarki shiyasa sihirin bayyi tasiri akanta ba, Amma a kowani lokaci zasu iya shammatarta dan suga sun hallakata, sunzo su kasheta ko kuma su 6ata Mata rayuwarta su hanata ji su hanata gani, saidai Allah ya taimaketa tayi nasarar Hana rufewar idonta saboda addu'ar datayi a lokacin, Amma a zahirin gaskiya bazata k'ara jiba, bance har abada ba watak'il wataran taji idan Allah ya nufa, Amma a gaskiya Wanda yayi aikin a kanta shu'umin Bokane mashahurine, Yanzu idan ta tashi zatayi maganarta sak tamkar da, saidai idan Kun maida matane itace bazata jiku ba"

Babu abunda kakeji sai "Innalillahi wa Inna illayyir raju'un" hankalinsu gabaki d'aya a tashe yake musamman ma Hafiz, cikin rud'u da tashin hankali Hafiz yace "Amma tayaya?, Alhalin Bata da kowa, waye ya saka Mata Ido har haka fisabilillahi, kamar ta yanzu an nakasa mata rayuwa, Mai tayi musu haka?, Yarinyar da batasan dad'in uba ba bare na mahaifiya, yarinyar data taso cikin *GARARI A RAYUWATA* amma Yanzu azo ana bibiyarta za'a hallakata, su waye wa 'yannan?"
Ya fad'a Yana Hura iska tare da naushin iska, Mai Gari shima duniyar tunanin daya afka kenan, Habiba hawaye nabin fuskarta tace "Allah ya saka Miki Humaira, zuciyarki fes take Amma wasu suna Bibiyar rayuwarki ta hanyar sharri, da yardar Allah koma waye sai asirinsu ya tonu kuma ta Allah ba tasu ba...."
Cikin Jimami Mama Tace "Tabbas akwai wani 6oyayyan al'amari a tattare da ita"
Hayak'i Sarkin Aljanu ya bata akan a runk'a yi Mata turare, yayinda ya had'a Mata magungunan sammu Dana Aljanu, Nan sukayi sallama da Mai Gari harda Liman suka tafi tare dayi musu Allah ya k'ara sauk'i.
  Mai Gari, Mama, Hafiz, Habiba jugum sukayi suna kallon Humaira yayinda gabaki d'aya zuciyoyinsu tausayinta ne fal cikin ransu.
  Bayan a wanni kad'an saiga Humaira ta farayin mik'a had'e da addu'a a bakinta.
Ganin ba kowa kusa da ita yasata tashi Dan gabatar da sallahr azhar, direct wajan famfo ta nufa tana mamakin maiya gajiyar da ita har haka, Dan jikinta ba k'aramin tsami yayi Mata ba, ganin Habiba tsaye kanta yasata yin murmushi Tace "Aunty Habiba Ina kikaje?"
Habiba shiru tayi tana kallan ikon Allah, yanzu dai Humaira zatayi magana saidai itace bazataji ba, ajiyar zuciya Habiba ta sauke ta zo kusa da Humaira tana mata nuni da zataci abinci, Humaira dariya tayi Tace "Ikon Allah yau Kuma maganar kurmaye zakimin?"
Habiba hawayan fuskarta ne suka sauko Tace "Ko kad'an Humaira ba Haka nake nufi ba"
Humaira canza fuska tayi ganin Habiba tayi motsi da bakinta Amma Kuma bataji abunda Tace Mata ba, cikin rashin fahimta Tace "Aunty Habiba Naga bakinki yayi motsi Amma kuma banji me kike cewa ba"

Sai a lokacin Habiba ta gasgata zancan Sarkin Aljanu, ta bud'e Baki zatayi magana Kenan taji muryar Hafiz Yana cewa "Ki kyaleta Karki Mata magana, kije kiyi abunda ya Dace, Baba zai Mata bayani yadda yaka Mata, ba musu Habiba tabar wajan tana Mai tausayin Humaira, yayinda Humaira Tana kallansu suna motsi da Baki amma ko kad'an Bata jinsu, shiru tayi tana kallan Hafiz yayinda shima itad'in yake kallo, kawar da kanshi gefe yayi yabar wajan.

Humaira kuwa Dak'yar ta samu ta Gama alwala d'in tunani ya cika Mata zuciya, itama kanta abun ya Bata mamaki batajin komai, hatta Kiran Sallah yau bataji ba da agogo tayi amfani, ajiyar zuciya tayi ta tada sallahr ta ganin lokaci na k'ure wa.
Baba ne yayi gyaran murya yayinda Humaira na tsugunne tana jin mai yasa aka tarasu, Duk da ta Lura Yanzu kome za'ace Mata saidai ayi Mata nuni, Mai Gari ne ya kalli Hafiz yace "Ka Bata letter d'in ta karanta"
Hafiz ya dad'e kafin ya mik'awa Humaira, ganin ana mik'o Mata takadda yasa gabanta mummunan fad'uwa ta kar6a hannunta na rawa, shiru ne ya biyo baya, yayinda ta bud'e takaddar tanason taga menene a ciki, Zama tayi cikin natsuwa ta karanta tsaf.
Kowa fargaba yake yadda Humaira zata kar6i al'amarin, sai Kuma labari yasha bambam bayan ta karanta, murmushi ne shinfid'e a fuskarta Tace "Yanzu Akan wannan *K'ADDARAR RAYUWAR* na _Zainab M bawa_, tawa kuka tada hankalinku?, Babu komai Nina yadda da k'addara Mai kyau ko akasin Haka, Haka Allah yaso ya ganni cikin wannan jarabawar, duk da Ni inajin abinda nake cewa kune in kukai banaji, nidai fatana Allah ya bani ikon cinye Wannan jarabawar" ta k'arashe fad'a fuskarta d'auke da murmushi Tace karku damu Dani Haka Allah ya tsaramin tawa rayuwar, Nagode k'warai da kulawarku gareni.

Gabaki d'aya Saida jikinsu yayi sanyi, Hafiz kuwa tausayin tane ya mamaye Mai zuciyarsa, yasan zata shiga wani Hali ko yayane, saboda ba haka ta taso ba Dole zata Damu a cikin zuciyarta, shiru yayi Yana Mai tausaya mata, Mai Gari ne yayi nuni da kowa ya tafi, ba musu kowa ya tashi, yayinda Humaira zuciyarta kamar zata tsinke, tana mamakin shin da gaskene bazata Kuma jiba, yau itace bazataji ba amma ita za'a jita, hawaye masu d'umi ne suka sauka akan kuncinta tana tunanin rayuwarta, tana tunanin yaushe zata samu natsuwa da farin ciki kamar yadda sauran al'umma sukeji, yaushe zata ga nata iyayan, shiru tayi tana tausayawa rayuwarta.
Hafiz duk abunda Humaira take Yana kallanta, sosai ta bashi tausayi, shiyasa ya kasa tunkarar ta yayi sauri yabar wajan karta ganshi.

Aneesah cikin rashin jin dad'i Tace "Amma Boka kasan na yadda da aikinka ko, Amma Yaya za'ai a wannan Karan a samu tangard'a, kana ganin yadda muka baka kudinka complete Dan Kar a samu matsala Amma Kuma gashi kace Bata mutu ba, Yanzu me kakeso nace Mata" ta fad'a tana Hurar da iskar bakinta.

Tsaki Boka yayi yace "So kike garin in kasheta ni su kasheni Kenan, Alhalin ban shiryawa mutuwa Yanzu ba, Yanzu kud'i zata k'aro Dan a lalatawa yarinyar rayuwarta duk da yanzu Haka bataji, naso ma na had'a Mata da makanta Amma hakan Bai yuwu ba, Yanzu saidai yaushe zakuzo akwai wani aiki Mai matuk'ar muhimmanci da zanyi akanta kafin kuzo"

K'aramin tsaki taja Tace "Shikenan ba damuwa Zan Mata magana naji duk yadda Tace," katse call d'in tayi tana tunanin yadda zata tunkari k'awarta da wannan maganar ta rashin samun nasara da basuyi ba.

Maryam cike dajin haushi Tace "What?, Bai yuwu ba kikace?, 2 millions d'in Dana bayar sun tafi a banza Kenan?, Gaskiya hakan bazai yuwu ba" ta fad'a tana huci.

Aneesah Tace "Ki natsu mana, in Banda abunki maye 2 millions a wajanki Dan kin fitar da ita, kikasan wani irin shiri yayi akanta tunda Wannan yak'i aiki, to Bari ma na fad'a Miki magana Mai dad'i an kurmantar da ita, Yanzu Babu ita Babu jin magana"

Ta6e Baki tayi Tace "Ni nafison a kawar da ita, inba Haka ba asirina ne zai tonu"

Aneesah Tace "Karki damu, Yanzu ki shirya cikin satin Nan zamuje wajansa muji abinda zai Mata Kuma, saidai ince Miki ki tanaji kud'i"

Maryam Tace "kinsan kud'i ba matsalata bace inhar burina zai cika ko nawane Zan bada"

Murmushi Aneesah tayi tace "Ko kefa"

*#Comments*
*#Likes*
*#Votes*

Mum Irfaan ceeee

GARARIN RAYUWAWhere stories live. Discover now