PART 12

226 14 0
                                    

Tafiya suke cikin natsuwa sunason su Isa Hospital d'in, Humaira kallan Habiba tayi Tace "Aunty Habiba Anya Zamu samu damar ganinta kuwa?, Naji fa kunce 'yar shugaban k'asa ce, kinsan baza'a barta sakaka ba"
  Habiba Tace "Eh Humaira, Nima kwatantawa zanyi idan Naga bazan samu ganinta ba sai mu dawo gida"
Jinjina Kai Humaira tayi suka cigaba da tafiya.
Tafiya kad'an sukayi sai gasu a tafkeken hospital d'in da aka cika da al'umman jama'a, kowa Saida ya zaro idanu tsakanin Habiba, Ummi da Humaira, saboda basuyi tunanin zasuga al'umma Haka ba tamkar ana wani babban bikin mashahurin d'an siyasa, Humaira gaba tayi yayinda Habiba ta ruk'o hannunta Tace "Humaira zauna anan, yaushe Zamu shiga a mammatse mu, kina ganin k'ofar get d'in mak'il da maza"
Humaira Tace "Mu shiga ciki watak'il mu samu ganinta"
Habiba Tace "Waike an fad'a Miki cikin sauk'i Zamu ganta?, Mu tsaya a Nan idan Allah yasa zata wuce na samu tsaida ita Tom, Dan naji an Gama komao fitowarta kawai muke jira"
   Zama sukayi akan wani dandamali, Habiba tana fuskantar Ummi suna Hira.
Yayinda wani d'an iska tunda ya hango Humaira yake kallanta, ganin su Ummi sun juya mata baya yasashi nufo inda take, ba tare data ankara ba taji an saka hannu an ta6a Mata Nononta, a matuk'ar tsorace ta tashi tana faman kalle-kalle ganinshi datayi hankali kwance Yana d'aga Mata gira yasata fusata ta tsinka mishi mari ji kake tass, ta k'ara tsinka mishi Mari a hannunta na dama, ganin ta k'ara d'aga hannunta zata k'ara mishi ya Habiba ruk'o hannunta Tace "Ke Wannan namijin kike duka saiya kamaki ya Miki lahani?"

Kukane ya su6ucewa Humaira Tace "Ina zaune yazo ya ta6amin..."
Shiru tayi ta kasa k'arasawa, yayinda kallo duk ya koma kansu.
A zuciye Wannan matashin yayi kan Humaira zai daka yaji an ruk'e Mai hannu, Yana d'aga idanunsa yaga d'aya daga cikin security d'in Doctor Hafsa ne, yayinda Hafsa tana cikin moto taga duk abunda ya faru tsakanin Humaira da wannan saurayin, tuni zuciyar ta taji Babu dad'i saboda irinsu ne masu lalata tarbiyar Yara, handcuffs aka saka mishi aka tafi dashi yayinda su Humaira kuwa sunyi nisa sai faman shashshek'an kuka takeyi.

Hafiz Yana zaune a dandali ya hango su Habiba ta ruk'o Humaira tana kuka, kallansu yayi cikin rashin fahimta, sai Kuma ya kawar da kanshi gefe ya cigaba da abunda yakeyi, ta gabanshi sukazo suka wuce yaji Habiba tana cewa "Nace kiyi hak'uri ba'a an kamashi ba an tafi dashi Police ba, Nan gaba ko ance yayiwa wata Haka bazai k'ara ba, ki barshi da Allah..."

Jin baya jiyo k'arashen da Habiba tace yasa hankalin sa kasa kwanciya, ji yayi kamar ya bisu, saidai bayaso mutane su fara hango abunda ke zuciyarsa game da Humaira, zamansa yayi ya cigaba da abunda yakeyi, tashi yayi kamar an tsikaresa ya shiga gida, Yana shiga gida yaji Mama Tana cewa "Au iskancin naki ya wuce lungu da d'akin samari saboda zalama da nuna Kun Isa kedashi zai kama tatta6aki cikin dubun al'umma?, Bari Baban nasu ya dawo na fad'a masa duk lalatar da kikeyi Yanzu, wato ya ta6a Miki...."

Hafiz Bai Bari ta k'arasa ba ya kirata da wata irin murya wacca shi kanshi baisan Yana da ita ba yace "Mamaaaa!"

Mama cak tayi tana kallansa jin Kiran nashi bana hankali ba, yayinda Habiba tana tsaye tana matsar hawaye tana Dana sani na fad'awa mahaifiyar ta abunda ya faru, a ganinta ita Mai kwantarwa da Humaira hankali ce, Allah yaso ma Ummi ta tafi gidansu da kunyar da zataji saitafi haka, yayinda Humaira ta kasa magana tana tsaye tana wani irin kuka me ban tausayi, tasan da mahaifiyarta ce da saidai ta rufa Mata asiri Koda kuwa yawon iskancin take, Amma taji tana gani ana lak'aba Mata shaidar Zina itada k'yamar mayyi ma takeyi.

Hafiz tunda ya Kira sunan Mama ta kasa cewa uffan saboda taga yanayinsa tamkar bashi ba ga idanuwansa sun sauya kala, k'arasawa yayi kusa da Humaira ya ruk'o hannunta yace "Wuce muje"

Humaira tsayawa k'am tayi tak'i tafiya taja Tanga ta tsaya, Tace "Ni ba inda zani"
  Hafiz kallanta yayi yace "Ai ba fita nace kiyi ba ki shiga cikin gida"
Make kafad'a tayi Tace "Bazan shiga ba, bazan k'ara kwana a gidanku ba, ku rabu Dani gaba zanyi dama Ni Humaira na Saba *GARARI A RAYUWATA*, na Lura Mama batason zamana a gidan Nan, Mai nai mata da zataimin shedar iskanci, nasan nida 'yar data haifane koda nayi iskancin ita mai rufamin asiri ce, banson Zina banson Mai aikatata Ni bazan k'ara kwana a gidannan ba" ta k'arashe fad'a numfashinta na k'ok'arin d'auke wa, tare da k'ok'arin k'wace hannunta daga hannunsa.
Kallan Habiba yayi da Mama, ba shiri kowa yabar wajan saboda maganar da Humaira ta fad'a har Saida ta ta6a zuciyar Mama, tasan da 'yartace da bazatai Mata Haka ba.
Hafiz ganin da gaske Humaira tafiya zatai yasashi daka Mata tsawa yace "Waike Mai yasa bakyajin maganane, nace ki wuce ki tafi gida"
Kallan shi tayi da idanunta Wanda sukayi matuk'ar canza kala, sai Kuma ta kawar da kanta gefe ta cigaba da k'ok'arin k'wace hannunta, Tace "Nace bazan k'ara kwana a gidannan ba ka sakeni"

GARARIN RAYUWAWhere stories live. Discover now