Asubar fari mahaifiyar Ado Tazo Dan duba Humaira Amma sai taga bukkar a wangale, tuni gabanta yayi mummunan fad'uwa, dak'yar ta samu ta k'arasa cikin bukkar tana tunani kala-kala, tana shiga ta hango Humaira a sheme tana baccin gajiya, ganin Babu Wani alamun an ta6ata yasata sauke nannauyiyar ajiyar zuciya, k'arasawa tayi ta fara tashinta tana fad'in "Indo!, Indo!!, Tashi kiyi sallah asubahi tayi"
Humaira mik'a tayi tana wuru-wuru da Ido Tace "Inna har asuba tayi?"
Mahaifiyar Ado Tace "Eh, Mai yasa Baki kulle d'akin ba, Kika barshi a bud'e?"
Humaira yatsina fuska tayi tace "Wallahi Inna zafi naji, naga bazan iya kwana d'akin a rufe ba"
Hararar ta tayi Tace "Aiko Dole ki koya rufe Kanki inba Haka ba zaki lalata rayuwarki"
Humaira sakin Baki tayi Tana kallanta tamkar wata sauna Tace "Inna tayaya rayuwar tawa zata lalace?"
Inna shigowa bukkar tayi Tana kalle-kalle Tace "Nasan ke yarinya ce cakal, a matsayina na 'ya mace inaso ki d'auke Ni tamkar mahaifiyar ki, inaso duk abunda nace Miki a gidannan kice to Dan Kare Kanki da kuma darajarki"
Humaira kallanta tayi ta zabga tagumi, tana kallanta kamar da gaske Gane abunda take cewa take.
Sauke ajiyar zuciya mahaifiyar Ado tayi Tace "Nasan ke yarinya ce, bazaki Gane abinda nake nufi ba, Saida inaso na gargad'eki namiji Koda ya ruk'e Miki hannu Karki sake ki yadda ki kurma ihu koma waye insha Allahu zanzo gareki, sannan Karki sake wani namijin ya d'auki hannunki yasashi a sasan jikinsa shima kikaga Haka ki kurma ihu, Karki Bari wani ya ta6a Miki jiki, duk yadda kuke dashi kuwa, inba Haka ba rayuwarki zata lalace ki Zama abun tausayi, kinsan yadda almajirai suke yawon Bara a Baki titi?"
6ata fuska Humaira tayi Tace "Na sansu, Kuma banason Inga ana kyararrasu tausayi suke bani..."
Mahaifiyar Ado Tace "Yawwa idan Kika yadda da abubuwan Dana lissafo Miki kikai ma wani namiji to Haka kema Zaki kasance ki Zama abar kyama ga jama'a, Haka rayuwarki zata K'are a titi, kinji ai, karfa ki yadda"
Tagumi Humaira tayi Tace "Ina Zan yadda Inna, Haka kawai na Zama mabaraciya, dama binni kikace ko makka da saina yadda..."
Inna katseta tayi da cewa "Duk Wanda ya fad'a Miki zai kaiki d'aya daga cikin wa 'yannan k'arya yakeyi, su Mai yasa basuje ba, tashi muje muyi sallah, Karki sake ki yadda da ko wani d'a namiji"
Jinjina Kai Humaira tayi tana mamakin yadda Mahaifiyar Ado take fad'a Mata hakan, ko Mai yasa ohon mata, Amma ta d'auki k'udirin jin shawarar mahaifiyar Ado Dan kuwa Humaira batasan yin Bara ko kad'an a rayuwarta duk da taso cikin rashin gata da Kuma rashin iyaye kusa da ita.
Tun daga lokacin Humaira take kulle d'akin ta saidai taita faman yin fifita, takan yin mamakin yadda Ado da Mahaifin sa suke janta a jiki da kuma yadda suke kashe Mata kud'i, ko kad'an Babu Wanda ya ta6a yin yunk'urin yin lalata da ita, shiyasa Bata kawo komai a ranta takan zauna ta baje taci abunda suka kawo Mata, sai faman yabonsu takeyi ganin yadda suke da kirki.
Yau take Friday yayinda Hafsa da sauran mak'arrabanta suka dawo gida Nigeria, twins sai faman murna suke, yayinda kawu da Sa'eed suke faman tsokanan su, motoci na alfarma ne sukazo D'aukar su, kasancewar Mahaifin Hafsa yaci takarar shugaban k'asa, sosai aka taho da jami'an tsaro Dan Kare lafiyarsu, murna Hafsa take yau zataga family d'inta, tunani kawai take yau Kuma zasu kar6eta, murmushi tayi, ta shiga mota yayinda su twins suka shiga motar da mahaifin su take.
Mahaifiyar Hafsa sosai take farin ciki a zuciyarta zataga 'yarta, yayinda a zahiri Kuma ta nuna halin ko in kula, kasancewar a gidan mahaifan Hafsa za'a sauka yasa suka nufa Villa direct gidan gwamnati, Hafsa kuwa mamaki take yadda rayuwa ta komawa mahaifanta sun samu abunda suke so Wato mulki, murmushin gefen Baki tayi ta cigaba da abunda take.
YOU ARE READING
GARARIN RAYUWA
ActionLittafin GARARIN RAYUWA Yana d'auke da tausayi, nadama, tsantsan soyayya, nishad'antar wa, fad'akarwa, wa'azantarwa da d'unbun Dana sani, yarinya ce batasan Hawa ba batasan sauka ba, ana haifarta aje a yadda ita ba tare da an k'ara waiwayanta ba, Iy...