Dak'yar Hafsa ta dawo daga hayyacinta yayinda take zubda Hawaye.
Tuni Malam Habu ya nemi rashin lafiyarsa ya rasa, shima hankalinshi a tashe.
Tunda Hafsa ta dawo hayyacinta ya kalli Kande Tace "Komai Zaki iyayi inhar akan Jiddah ne, ko ki fito da ita ko Kuma an Miki abunda bazakiyi tsammani ba, Jiddah inhar zataga Malam Habu to Ina Mai tabbatar Miki bazata gudu ba, Wannan 6acewar da Jiddah tayi dasa hannunki, na fad'a Miki kiyi gaggawar fad'amin inda Kika kaita"Kande tuni cikinta ya d'uri ruwa Tace "Tayaya Zan d'auki yarinya na cillar ai rashin Imanina baikai Nan ba, Dan Haka bani na yarda Humaira ba ahee"
Hafsa Tace "Haka kikace?"
Kande Tace "Haka nace"
Tashi Hafsa tayi a fusace ta nufa motar ta tare da fad'in "Arrest her, duk Randa Ta fad'a inda take maje mu d'auko ta"Saboda taurin Kai irin na Kande Amma tak'i fad'a musu.
Hafsa ganin Malam Habu yayi shiru ana k'ok'arin saka Kande a mota ne yasata fitowa daga motar taje inda yake, cikin sanyin murya Tace "Kayi hak'uri Baba zakaga kamar ban maka adalci ba za'a tafi da matarka, Ina kyautata zaton da saka hannun Kande a 6atan Jiddah, saboda yadda naji jawabin ka jikina Yana bani itace silar komai"Malam Habu ajiyar zuciya ya sauke yace "Babu komai, Nima ina zarginta da saka hannu a 6atan Mamana, kuyi Mata duk abunda zakuyi Dan ganin ta fad'a muku gaskiyar lamari"
Godiya Hafsa tayi Masa tare da bashi kud'i masu yawan gaske, tuni aka saka Kande a motar police.
Tunda Hafsa suka dawo gida tak'i kula kowa, d'akinta ta nufa ta kulle ta kwanta taita rusar kuka tamkar ance Mata Jiddah ta rasu, anyi bugun duniyar Nan amma Hafsa tak'i bud'ewa kuka kawai takeyi tare da fargabar inda Jiddah take, wunin ranar haushin kowa takeji Kuma tak'i bud'e d'aki, hatta mahaifiyar ta Wannan Karan datai Mata magana tak'i sauraranta, Sa'eed tuni ya tuna akwai k'ofar shiga d'akinta ta hanyar kitchen, Nan da Nan ya tashi yaje ya d'auko key d'in kitchen d'in ya shiga d'akinta, tana Nan tana zubda hawaye, Sa'eed ne yayi saurin k'arasawa wajanta Tai saurin dakatar dashi ta hanyar cewa "Ba abunda zaka fad'amin a wannan Karan, yanzu burinku ya cika sai ku zuba ruwa a k'asa kusha, Jiddah ta tafi ta barni a lokacin da nake tsananin buk'atar ta, Kun rabani da ita, bazan yafe muku ba"
Sa'eed jiki a sanyaye ya k'araso inda take duk da tana jifanshi da wani irin kallo, basarwa yayi yayinda shima ya tsuke fuskarsa Babu walwala, kawar da kanta gefe tayi tana kallan wani wurin.
Zama yayi gabda ita yace "Wake meke damunki ne?"
Hafsa Tace "Tambayata ma kakeyi make damuna?, Yarinyata ta 6ata Amma kakemin Wannan tambayar", kukane yaci k'arfin ta Tace "Kune silar komai Kuma ku sani duk abunda ya samu yarinya ta bazan yafe muku ba Wallahi" kuka ta saki Mai ban tausayi yayinda ta tashi tabar mishi wajan ta cigaba da kukanta.
Tashi yayi yabita yace "Kizo kici abinci fa, tun safe Babu abunda kikaci"
"Ban ci" ta fad'a tare da banko Mai k'ofar bedroom d'inta ta kulle ta saka mata key.Watan Kande uku a cell Amma tak'i fad'an inda ta Kai Humaira, amsar d'aya take badawa shine itafa batasan inda Humaira ta nufa ba.
Tunda abun Nan ya faru Hafsa ta daina kula kowa, daga ta dawo daga hospital Bata tsayawa yin Hira da kowa, ta gwammace ta zauna a d'aki taita faman tunanin inda 'yarta take, gashi an tabbatar musu tana Raye, shiyasa hankalin Hafsa ya Gaza kwanciya.
Humaira kallan Ado tayi tace "A'a nifa ban yadda ba Wallahi, Haka kawai naje d'auko maka ka k'ara rufemu a d'aki, Allah yaso Inna ta dawo Tace Ka bud'e da bansan me zakaimin ba" ta fad'a tana mak'ale kafad'a.
Ado ganin yadda yake lalla6ata abun yak'i yuwuwa yayi Mata Jan Ido yace "Zaki shiga ko saina zaneki a gidannan Babu Mai cecenki, Kinga 'yar rainin hankali, da kinbin abun a Sannu da kinfi samun kud'i tunda naki da rainin hankali to Dole sai kin shiga ko nai Miki dukan tsiya"Humaira cogewa tayi Tace "Waikai Yaya Ado d'an iska ne Kai kakeso mu shiga d'aki tare?, Naji Inna Tace duk yarinyar data shiga d'aki da namiji to 'yar iska ce Dan Haka Babu inda zani"
Ran Ado ya Soma 6aci ganin matarshi ta kusan dawowa, a fusace ya hankad'ata cikin d'akin ya kulle, tuni cikin Humaira ya fara k'ugi, ganin window d'in d'akin a wangale Kuma zata iya haurewa yasata nufar wajan, Ado ganin ta nufa window d'in d'akin shima ya yunk'ura zai kamota Amma tuni ta haure, k'afarta kawai yayi nasarar cafkowa da k'arfin ta ta shuresa ta gudu, gudu kawai takeyi cikin dajin Nan tana zubda hawaye, ganin Ado ya nufota yasa ta k'ara kwasawa a guje, tuni ta 6ulla bakin Titi ba tare data tsaya jiran motoci su wuce ba ta kwasa a guje ta tsallake Titin Saura k'iris mota ta kad'e da Dan harta gogi jikinta.
Ado Yana haki ganin Tai Masa nisa yaja Tanga ya tsaya Yana fad'in "Wallahi Zaki dawo ki sameni an fad'a Miki a banza Zan kashe Miki kud'i, bazan kashe Miki kud'i ba gaira ba dalilin ba" k'wafa yayi ya juya ya tafi sai d'ura Mata ashar yakeyi.Humaira ganin Bata hango Ado hakan na nufin ya hak'ura dabin Nata Kenan ya juya gida, tuni ta tausayawa rayuwarta ta cigaba da tafiya ga yunwa da k'ishin ruwa sun hanata sukuni, tafiya kawai takeyi tamkar wacca zata fad'i k'asa, ganin bishiya yasata Zama Dan ta huta, sosai Humaira takejin yunwa, kallan kanta tayi taga daga ita sai takalmi ko mayafi Babu a jikinta, shiru tayi tana tunanin Ado wani irin mutum ne kamar ita wacca Bata wuce goma Sha biyar ba Amma yake k'ok'arin Haye Mata, kukane ya su6uce mata yadda aka yadda ita Babu ruwan irin halin da zata shiga, tunanin tane ya katse ganin wasu Yara suna wanka a wani d'an k'aramin kududdufi, jira take kawai su Gama take Tasha ruwan ko zata daina jin k'ishin datakeji.
Basu d'auki lokaci ba sai gashi kowa ya saka kayansa sun tafi sunbar wajan, tuni ta tashi taje taga wajan, Babu kyan gani domin kuwa k'aramin kududdufi ne, Babu yadda ta iya Haka ta samu wata gora wacca Tasha datti ta wanke ya zuba ruwan, kafa Kai tayi Saida ta shanye ruwannan tass sannan ta sauke ajiyar zuciya, k'ara zuba wani tayi a robar tare dayin alwalar la'asar ta bar wajan ta koma k'ark'ashin bishiyar, tunani kawai takeyi yanzu Ina zata nufa Dan ta Gama yanke wa kanta shawara zamanta a gidansu Ado yau ya K'are, shiru tayi tana tunanin inda zata nufa.
Ganin hanyar da Yaran Nan suka nufa itama ta yankewa kanta shawara hanyar zatayi, tafiya kawai take tana tunanin inda yau zata kwana.Imraan lumshe idanuwansa yayi a karo na ba adadi, Haka kawai yarinyar daya had'u da ita ta kasa fita Mai a cikin Rai, a k'alla yaje gurin da suka had'u babu adadi Amma Koda Wasa Bai k'ara ganinta ba, yanzu kawai ya Gama yanke wa kanshi shawara k'ila Aljana ya gani ba bil adama ba, hakan ba k'aramin damusa yake ba, da tunda yake Bai ta6ajin Haka a wajan wata 'ya mace ba sai akanta, shida Bai ma ta6a soyayya ba tayaya zai tantance hakan, shiru yayi Yana faman nanata sunan a cikin zuciyarsa Wato *Humaira*
Kande ganin zasuyi Mata lahani yasata cewar zata nuna musu inda Humaira take, farin ciki a wajan Hafsa ba'a magana, Hatta Malam Habu Saida aka tafi dashi, ana zuwa wajan da Kande ta ajiye Humaira ta kallesu cike da tsoro da fargaba Tace "Tsakanina da Allah anan na ajiyeta bansan inda kuma tayi ba"
Hafsa kallan wajan tayi taga Babu komai face shukoki da kukan tsintsiyaye sai uban bishiyoyi dake wajan, hawaye ne suka sauka kan kuncinta Tace "Me Tai Miki Haka Zaki kawomin 'ya cikin wannan Dajin?, Meta tsare miki?"
Komawa wajan motarta tayi ta sadda kanta k'asa wani Abu ya tokare Mata cikin zuciyarta, shiga motar tayi tacema policy d'in ku shiga k'auyan garin harma da mak'wabtansu kuyi cigiyarta, ku tafi da Kande tasan fuskarta, Dan a halin yanzu Abu d'aya Zan Gane na Jiddah shine shaidar danai Mata, na dad'e rabona da ita"
Tuni suka cika Umarnin ta danyin cigiyar Humaira, yayinda ita Kuma Hafsa zazza6i mai zafi yayi awon gaba da ita.
Humaira ganinta tayi a babbar kasuwa, duk da yamma tayi wasu ma sun tashi, hakan ya nuna Mata da cikin gari ta shigo, wata rumfa ta samu ta kwanta saboda yadda ta gaji ga yunwa datakeji, kamar ance ta kalli k'asa ta hango wani abinci Wanda kana kallan sa zakasan tun Rana yake, tuni ta janyo plate d'in abinci tahauci hannu baka hannu k'warya, tana gamaci ta d'auko ruwanta Tasha, kafin kace me baccin wahala yayi gaba da ita.
*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*_Mum Irfaan ceeee_
*Er-Gafaii*
YOU ARE READING
GARARIN RAYUWA
ActionLittafin GARARIN RAYUWA Yana d'auke da tausayi, nadama, tsantsan soyayya, nishad'antar wa, fad'akarwa, wa'azantarwa da d'unbun Dana sani, yarinya ce batasan Hawa ba batasan sauka ba, ana haifarta aje a yadda ita ba tare da an k'ara waiwayanta ba, Iy...