PART 7

225 15 0
                                    

Hafsa ruk'o hannunsa tayi Tace "Cool down sweetheart, karka tada hankalinka a wannan lamarin, kasan ance in baka iya kama 6arawo ba to 6arawo ya kamaka, inaso kabi komai a Sannu"

K'wafa yayi ya koma ya zauna tare da sassauta muryar sa yace "Please kiramin 'yayana"

Ba musu Hafsa ta tashi taje garden ta Kira Twins, har wani rige-rigen zuwa suke saboda tsegumi, ganin kallan datayi musu ne yasasu natsuwa tace "Dad d'inku ne yazo daga Nigeria....."

Ai Basu Bari ta k'arasa ba suka bi ta gefenta harda bangajeta suka nufa inda Sa'eed yake Kira suke "Dad..."

Sai Kuna sukai shiru tare da hugging d'insa, suna zubda hawaye, Sa'eed d'in shima hawayene suka sauka akan kuncinsa, tare da godewa Allah Wai yau shine da yaransa na jini halak malak, lallai Allah abun godiya ne, maiyin yadda yaso Kuma yaga dama, wata ajiyar zuciya ya sauke a karo na ba adadi Yana shafa bayan yaransa.

Affan ne yayi k'arfin halin cewa "Dad kullum sai mun tambayi Mom d'inmu yaushe zata kaimu wajanka sai Tace Mana ba yau ba, idan ana meeting a school kowa Dad d'insa ne ke zuwa mufa saidai Mom ko kawu su suke zuwan Mana, thank God yau kazo garemu love you so much"

Farin ciki ne ya mamaye zuciyar Sa'eed yace "Nima ina k'aunar ku har cikin zuciyata, Ina matuk'ar sonku, Kuma Zan soku har k'arshen numfashi na"

Murmushi dukkaninsu sukai tare da k'ara k'ank'ame shi, tuni gurin ya koma Happy Family yayinda Hafsa tana tsaye tana kallansu murmushi shinfid'e a fuskarta.

Malam Habu ya tagumi yayi tare da k'unci cikin zuciyarsa, kallan Kande yayi zuciyarsa a raunane yace "Kima Dan girman Allah ki fad'amin Ina Kika Kai Mamana, nasan bakya sonta bakya k'aunarta komi Zaki iyayi akanta Dan ganin kin salwantar min da ita, ki duba irin wahalar danasha wajan nemanta inkinsan inda take ki fad'amin wallahi bazan Miki komai ba, zanje na d'auko ta"

Kande zuciyarta cike da fargaba Tace "Haba Malam Ni duk k'iyayyar da nakema Humaira ai Bata Kai har in d'auke ta na Yar ba saboda wani dalilina na daban, na fad'a maka gaskiya nemanta nayi sama da k'asa na rasa Naga har kayanta Mata ta kwashe tunda sukai fad'a da Aminatu Tai Mata gori tazo gida taita kuka na nemeta na rasa, bakaga neman danai mata ba Amma Babu ita Babu alamunta, Ni kaina bakasan irin tashin hankali Dana shiga ba" ta fad'a tsoro fal cikin zuciyarta.

Kallanta yayi ya rausayar da kanshi yace "Shikenan Zan Bata cigiyarta da garinnan dama mak'otan garin Nan, nidai fatana Allah yasa tana hannu na gari"

"Ameen" Kande Tace, tare makamai harara had'e da gwalo.

Tashi Malam Habu yayi Dan k'ara dubawa ko Allah zaisa ya ganta, sosai Malam Habu ya koma abun tausayi wajan neman Humaira, Dan kuwa takalmansa har Saida suka tsintsinke Dan tsabagin wahala.

Hira kawai Affan da Areef sukewa Sa'eed yayinda Sa'eed ya biye musu sunatayi, Hafsa wani sa'in saidai Tai murmushi ganin yadda shima Sa'eed d'in ya koma tamkar wani k'aramin yaro sai biye musu yakeyi.

Hafsa kallan agogon hannunta tayi taga har yanzu su Kawunta Basu dawo ba, Bata Gama tunaninta ba saijin sallamarsu tayi, shida matarsa d kuma yaransa, ganin Sa'eed a gidan yasashi tamke fuska ya shigo parlourn fuskarsa Babu walwala.

Sa'eed ganin Kawu yasashi fad'ad'a fara'arsa Yana gaishe dashi, Dak'yar ya amsa yace "Kai Kuma saukar yaushe?"

Hafsa ce tayi caraf tana Sosa Kai tace "D'azu da safe yazo Kawu"

Kawun nasu hararar ta yayi yace "Haka mukai dake?"

Sosa Kai tahauyi tare da in-ina, matarshi ce ta katseshi da cewa "Haba Abban Haneefa, tunda ka gansu Haka kaima kasan yanzu ya rugada yasan komai, kuma Alhamdulillahi kaga sun shirya kansu tunda har Sa'eed ya kar6i 'yayansa hannu bibbiyu ai sai mu godewa Allah, yanzu wacca muke tunan itace Jiddah, kamata yayi yanzu ayi gaggawar amsota a sakata a makarantar Boko Dana Arabic saboda gudun jahilci kunga k'auye basu damu da karatu ba"

Gabaki d'aya sunyi amanna da maganarta Dan Haka suka tsaida Date din randa zasu koma Nigeria gabaki d'ayansu.

Murna wajan Sa'eed da Twins ba'a magana, Dan ranar Twins a d'akin Sa'eed suka kwana sunk'i kwanciya a nasu d'akin, Haka Sa'eed ya rungume 'yayansa sukai bacci cikin farin ciki da lumana.

Humaira rarraba idanunta tayi tana kallan 'yar bukkar da aka gyara Mata, har k'ofar d'aki mahaifiyar Ado tazo ta k'ara jajjada Mata ta kulle d'akin duk Wanda yace ta bud'e karta bud'e, gyad'a kanta tayi tana tunanin yadda ake zafin Nan yaushe zata kulle d'akin, ta amsa matane kawai Amma d'akin a bud'e zata kwana Dan bazata kashe kanta ba, domin kuwa gani take kamar mugun ta mahaifiyar Ado tayi mata, saboda yadda taga yau ana zafi a garin.

Tunda taga mahaifiyar Ado ta tafi ta bud'e d'akin, tare da kwanciyar ta iska Mai dad'in gaske tayi gaba da ita, kafin ta ankara  bacci d'auketa.

*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*

Mum Irfaan ceeee🥰

*ER-GAFAII*

GARARIN RAYUWAWhere stories live. Discover now