PART 5

232 15 0
                                    

Watan Hafsa biyar Kenan da tafiya k'asar U.S yayinda Humaira ta k'ara wayo, hantara da tsangwama kuwa tana Shansa wajan Kande, Humaira yanzu kuwa ta fara sabawa da Hali irin na Kande, duk da yanzu ta girma ta k'ara wayo,  shak'uwarta da Malam Habu kuwa sai abunda ya k'aru, sosai Malam Habu yake k'aunar Humaira har cikin Ransa, yayinda Kande ta d'auki aniyar salwantar da Humaira tun kafin ta girma ta zame mata  k'arfen k'afa.

Hafsa kuwa ta d'auki aniyar Babu Wanda zata sanarwa maganar cikinta domin kuwa batasan a Yaya zasu d'auki lamarin ba, Haka taje ta samu kawunta, k'anin mahaifiyar ta ta fad'a Masa komai abunda ya faru Bata 6oye Masa komai ba, kasancewar Yana zaune a k'asar shida iyalansa.

Sosai ran shi ya 6aci ganin Koda Wasa Bai ta6ajin Wannan labarin ba, itama Hafsa fad'a yayi mata ta yadda ta biye musu harta Yar da 'yarta domin nasu farin cikin, yanke shawarar yayi akan ta zauna tare dasu tunda hospital d'in da take aiki kusa dasu ne, tare da alwashin bazata koma Nigeria ba har sai sun nemeta da kansu, sun Gane babban kuskuren da suka tafka a rayuwarsu, tuni Hafsa taji dad'in Wannan yanke hukuncin da yayi Amma idan ta tuna 'yarta sai farin cikin Nata ya koma ciki, ganin tana can tana fama da yanayin rayuwa.

_***************_

*IMRAAN*

Kyakykyawan matashin d'an siyasa kenan Wanda yayi shura ta fannin siyasa a Nigeria, Wanda a k'alla zaikai shekara Ashirin da shida, ya kasance Yana ra'ayin siyasa tun Yana yaro Shiyasa yake tare da manyan 'yan siyasa, burinshi a kullum ya Zama wani hamshak'in d'an siyasa, kallan mahaifiyar sa yayi ya lumshe idanuwansa yayinda eye lashes d'insa sukai luf yace "Mom Dan Allah ki barni da harkar siyasa ta, nifa ba d'an bangan siyasa bane, ke Kanki kinsan Haka, insha Allahu bazanyi abunda zai 6ata Miki Rai ba"

Mahaifiyar sa tace "Naji ya batun aure Kuma?"

Murmushi yayi yayinda ainihin kyansa ya bayyana yace "Aure Kuma Mom?, Ni yanzu Dan Allah har nayi girman da Zan cika Miki Ido nayin aure Mom please ki daina maganar Nan, aure lokaci ne, nifa ko budurwa wallahi Mom bani da ita"

Had'e fuska tayi tace "Imraan ka kiyayeni wallahi, nagaji da tatsuniyarka, kullum magana d'aya kakemin, ni gaskiya ka fito da matar da zaka aura, ko kafiso Nima saina mutu ba tare da Naga naka 'yayan ba....."

Sauri yayi ya katseta da fad'in "Please Mom ki daina fad'an Haka Mana, na rasa mahaifi banaso na rasaki a rayuwata, Ni wallahi da gaske nake miki Banda wacca nakeso, saidai idan har Zaki nemamin da Kanki, za6inki shine za6ina"

Murmushi tayi tace "Yawwa Son, Allah yayiwa rayuwarka Albarka ya baka zuri'a d'ayyiba"

Murmushi yayi yace "Ameen thumma Ameen Mom, Bari na tashi inaso zanje gun Governor akwai abunda zanyi acan"

Ajiyar zuciya ta sauke Tace "Ka runk'a kula da kanka kasan 'yan siyasan Nan kansu kawai suka sani"

Murmushi yayi yace "Insha Allahu Mom", fita yayi Yana tafiyar sa ta k'asaita.

Sa'eed tunda Hafsa ta tafi ya nemi contact d'inta ya rasa, kwata-kwata baya samunta, gashi Hafsa ita Tak'i nemansa, Haka soyayyar Hafsa take wahalar dashi a cikin zuciyarsa, shiyasa ya yanke shawarar zuwa can danya isketa, ya samu su k'ara gina wata lafiyayyiyar soyayya ita dashi.

Girman ba wuya a wajan Allah yanzu Humaira tayi wayo dan a k'alla zatakai shekara uku, Humaira yarinya ce Mai hak'uri da kawaici, gata kyakykyawa k'in kowa Wanda ya rasa, duk da tana cikin k'auye Amma kyawunta Bai hanashi fitowa ba, gashi Allah yayi Mata farin jinin mutane, hakan yasa Kande k'ara tsananta.

Humaira ko kad'an Bata damuwa da irin abunda Kande take mata, Dan Kande Babu Imani, Dan ko abinci taci to kwanan dataci sai tace ta wankeshi, gashi ta Bata tsintsiya Wai kamar Humaira ce zatai shara.

GARARIN RAYUWAWhere stories live. Discover now