Maryam da Aneesah tafe suke cikin k'oshashshiyar motarsu, direct wani k'aramin k'auye suka nufa wajan Bokan Aneesah, sosai k'auyan yake da nisa ga Titin k'auyan ko kad'an bashi dakyau, haka suka Kai k'auyan a wahalce suna faman maida numfashi, wata 'yar bukka can saman wani tsauni Babu abunda kakeji sai kukan tsintsaye, a Haka suka k'arasa suna faman Kama hannayansu saboda yadda sukejin jiri ganin su a can saman tsaunin, Aneesah ce ta fare yaye gyalenta tare da d'an kwalinta tahau yin bori, Maryam kuwa tsayawa kallan ikon Allah tayi, daga cikin bukkar suka jiyo wata irin murya ana cewa "An gaisheki tanbad'ad'd'iya, jinjirin aljani d'an *DUMUMU* na mik'o gaisuwa, shigo da ihu ta raki tare da burgima cikin bukkarmu, Ina fatan da kikai fitsari bakiyi tsarki ba, kin tabbatar kin d'auki Qur'ani kuwa?"
Murmushi Aneesah tayi ta kalli Maryam Tace "Shigo ciki muje"
Ba musu Maryam tabi bayanta tana mamakin hatsabibanci irin na Aneesah Bata d'auka takai Haka ba.
Suna shiga ciki Saida Maryam ta tsorata da ganin Wannan k'asurgumin bokan, saboda yadda Allah yayi mishi munin tsiya gashi a zaune sharaf tamkar kayan wanki, Haka suka shiga suna ihu sai kace mahaukata, samun guri sukayi suka zauna, Aneesah ta bud'e Baki zatayi magana Kenan Bokan yayi wuf ya dakatar da ita tare da cewa "Naaasan Mai ya kawoku wajena, akan Hafsa da 'yayan data Haifa ne musamman yarinyar data 6ata itace kukazo ayi muku aiki akanta ko?"Maryam mamaki ne ya cika ta, yayinda Aneesah kuwa ko jikinta saboda tasan Bokanta shu'umin gaske ne, matan masu hannu da shuni da 'yan siyasa ne suke zuwa wajansa saboda aikinsa tamkar yankan wuk'a Haka yake, murmushi Aneesah ta kumayi Tace "Wannan zancan naka Haka yake, munaso ka kasheta ne kowa ya huta, saboda duk Randa aka ganta to Ina Mai tabbatar maka asirinmu zai tonu, Kuma k'awata zata muzanta a idanun duniya, kayi Mana aiki ko nawane mun maka alk'awarin Zamu biyaka"
Wata uban dariya ya bushe da ita, yayinda ya d'auko wata k'warya da ruwa a cikinsa, sambatu ya farayi saiga hoton Humaira ya fito, murmushin gefen Baki yayi yace "Itace Wannan?"Maryam lek'awa tayi taga yarinyar kamarsu d'aya da Sa'eed ta wani fannin kuma kamarsu d'aya da Hafsa, ta6e Baki tayi Tace "Tunda nake ban ta6a ganin kalanta ba sai yanzu, Babu mamaki itace d'in saboda ga kamanninta Nan sak da Iyayanta....."
Cikin karaji Bokan ya dakatar da ita yace "Ke dakata, duk abunda Kika gani anan to tabbas haka yake a zahiri, wannan itace yarinyar danan gaba in Baki tashi tsaye ba zata hanaki jin dad'in rayuwarki gabaki d'aya, Dan Haka aikinku a k'alla zaikai 2 millions, nai Miki alk'awari saidai kuji ana sanar da mutuwar yarinyar, Humaira tana gidan wani Mai gari adali ne, Haka zalika 'yayansa Suma adalaine, babban yaronsa Yana sonta, da zarar ya furta Yana sonta zata shiga cikin tashin hankali da matsinanciyar damuwa, Dan Haka ki jira gawarta yau ko gobe".
Murmushi Maryam tayi Tace "Ka bani Account number d'inka Yanzu zakaji alert"Murmushi yayi yace "Aljanu sun kwasa kud'in duba balance d'inki"
A d'an tsorace Maryam ta duba kud'in taga an zari 2 Millions d'in kamar yadda yace, tuni tayi believe da cewar zai Gama mata komai.Yak'e tayi tace "Eh sun kwasa, sai Kuma maganar....."
Tuni Bokan ya Tara numfashinta yace "Sai Kuma mazan da mahaifiyarsu ko?"
Girgiza Kai tayi alamun "Eh"
Murmushi yayi yace "Bari na kammala Miki Wannan tukunna komai zai Zama daidai"Godiya sukai, yayinda Basu ankara ba suka gansu a wani wajan had'e da motarsu, Babu tsaunin da bukkar Babu alamunsu, abun ba k'aramin mamaki ya ba Maryam ba, tunani take dama akwai irin wa 'yannan shu'uman bokayan a doron k'asa, murmushi tayi ganin ya kusan tusawa Hafsa bak'in cikin da harta mutu bazata ta6a mantawa da ita ba, tafiya kad'an sukai sai gasu akan kwalta, zuciyar Maryam tass tana farin ciki, Dan ta Gama yadda cewar Humaira ta rugata ta mutu.
_*************_
Dak'yar Hafiz ya tashi jin kanshi yayi nauyi, fitowa yayi Dan gabatar da sallahr Ishsha'i, Yana zuwa wajan famfo ya hango wata kamar Humaira tana alwala, tanayi tana share hawayan fuskarta, murza idanunsa yayi yaga still itace ba wata ba, matsawa kusa da ita yayi yaga tad'an tsorata, sai a lokacin ya yadda da itace, ganin itace yasashi basarwa yaje yayi alwalar sa ya bar mata wajan.
YOU ARE READING
GARARIN RAYUWA
AçãoLittafin GARARIN RAYUWA Yana d'auke da tausayi, nadama, tsantsan soyayya, nishad'antar wa, fad'akarwa, wa'azantarwa da d'unbun Dana sani, yarinya ce batasan Hawa ba batasan sauka ba, ana haifarta aje a yadda ita ba tare da an k'ara waiwayanta ba, Iy...