Mai gari cike da farin ciki yace "Da ana samun irinku masu hannu da shuni suna taimakon na k'asa dashi da ba k'aramin cigaba Zamu samu ba a k'asar Nan tamu, k'warai naji dad'in Wannan karamcin naki Doctor Hafsa, Allah ya saka da Alkhairi yasa mahaifin ki yaci takarar shugaban k'asar Nigeria"
Murmushi Hafsa tayi Tace "Ameen thumma Ameen, nace inba damuwa ko za'a kaini inda marayun suke na gansu"
Mai gari Jim yayi Yana nazari yace "A gaskiya a watan Nan jarirai biyu muka tsinta, Kuma an samu masu D'aukar su, Saida a cikin biyun Allah yayi ma d'aya rasuwa saboda Rashin Nono da yake fama dashi"
Tuni gaban Hafsa yayi mummunan fad'uwa, saita kanta tayi tace "Allah ya gafarta Mata.."
Mai gari yace "A'a Namijin ne ya rasu, amma macan tana gidan Malam Habu Yana ruk'e ta"
Wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke Tace "To inba damuwa za'a iya kaini gidan Malam Habu d'in?, Kayan mazan Kuma ka aje a hannunka nasan baza'a rasa mabuk'ata ba, ga dubu d'ari biyar Nan please a Bawa marasa k'arfi"
Mai gari washe Baki yayi yace "Allah ya k'ara bud'i yasa kifi haka" waigawa ya farayi yace "Yanzu kuwa Zan Nemo Wanda zai kaiki har gidan", ba tare da 6ata lokaci ba ya samu Wanda zai kaita, Mai gari kuwa ba k'aramin shi Mata Albarka yakeyi ba.
Sosai Hafsa taji dad'in kalaman Mai gari, cike da k'warin gwiwa ta nufa gidan Malam Habu.
Wanda ya rakota ne ya nuna Mata gidan tare da juyawa ya koma fadar Mai gari, zuciyar Hafsa sai faman bugawa take da k'arfi da k'arfi, addu'a d'auke a bakinta ta kutsa cikin gidan, tana tak'wala sallama amma shiru ba'a ansa ba, jin kukan jinjirar yasata kutsawa cikin gidan, tana shiga ta hango Jiddah shinfid'e akan tabarma ga uban ranar datake facing d'inta, daga ita sai wani pant Wanda yayi datti, wani Abu ne ya wuce Mata a mak'ogwaro ta zauna kusa da Jiddah tana K'are mata kallo, shedar datayi matane yasata tabbatar da cewa 'yarta ce ganin yadda ta lalace ta rame ko kumarin jarirai babu a tattare da ita.Kande ce ta fito daga bayi hannunta ruk'e da buta, ganin Hafsa cikin shiga ta Kamala yasata wage bakinta Tace "Mara ba sannunki da zuwa kin shigo Ina bayine shiyasa kikaji gidan tsit"
Hafsa Tace "Ayya Babu komai, sunana Doctor Hafsa nazone akan tallafawa marayu, naji labarin Kuna ruk'e d'aya daga cikin marayun da aka tsinta a garin Nan shine nazo Dan tallafa Mata"
Ta6e Baki Kande tayi tace "In Banda son abun duniya ace Wannan yarinyar Mai tasani da za'a kama a Yar da ita dan kawai son zuciya irin na mutane, nifa kin ganni nan da badan Naga aurena Yana girgid'i ba akan Wannan yarinyar wallahi da tuni tabar gidannan, Kinga yadda Malam yakeji da ita kuwa?, Uhm ninasan ko 'yar da ya Haifa sai Haka wallahi, Wai Nan saboda son asani sunan Mahaifiyar sa ya saka Wai Aisha..."
Hafsa kallan 'yarta tayi sai Taji tausayin ta ya mamaye Mata zuciya, kallan Kande tayi Tace "In Banda abunki Baiwar Allah ai d'a na kowane kikasan irin ranar da zatai Miki wataran"
Kande dariya ta 6alke dashi Tace "Banga alama ba, yarinyar datake cikin shege zataimin Rana, Ina Banga alama ba, ke nifa Bari kiji tunda Naga mijina ya fifita 'yar Nan akaina naji na tsaneta bana k'aunar ta wallahi" waige-waige ta farayi Tace "Kina ta maganar tallafi Wai Mai Kika kawowa yarinyar ne?" Ganin Uban Kaya a bayanta da Kuma gwangwani Madara ta NAN yasata janyo gwangwani tana fad'in "Wannan Kuma menene?"
Ajiyar zuciya Hafsa tayi Tace "Madarar yarace zata Tai maketa k'warai wajan Gina Mata jiki ganin yadda abinci baya isarta"
Washe Baki Kande tayi tace "Ai kuwa kin kyauta dama Malam kusan kullum saiya fita da asuba Dan ya samu tatsatstsiyar Madarar shanu ya Bata, wani sa'in fitar banza yakeyi kafin yaje sun Gama" ta fad'a haka tana k'ok'arin bud'e gwangwani, tana bud'e wa tasa hannunta ta d'iba kad'an takai bakinta, tuni Kande ta lumshe idanuwa tare da fad'in "Ai wannan Madarar Bata Humaira kawai kad'ai harda Maruk'iyarta Dan bazanyi raino a banza ba, uwarta tanacan hankalinta kwance Amma Ni anbarni anan Ina fama da aikin wahala"
YOU ARE READING
GARARIN RAYUWA
ActionLittafin GARARIN RAYUWA Yana d'auke da tausayi, nadama, tsantsan soyayya, nishad'antar wa, fad'akarwa, wa'azantarwa da d'unbun Dana sani, yarinya ce batasan Hawa ba batasan sauka ba, ana haifarta aje a yadda ita ba tare da an k'ara waiwayanta ba, Iy...