Page 15

276 8 0
                                    

*GARARIN RAYUWA*

*MALLAKAR*
  _Ƴar Gafai_
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

                      *PAGE 15*

Sosai rayuwar Humaira ta canza ba kamar daba, Yanzu Humaira bata shiga cikin jama'a Koda yaushe zaka ganta a raku6e gefe guda ne, wani lokacin tayi kukanta ta k'oshi wani lokacin Kuma saidai ta zabga uban tagumi tana tunanin yadda rayuwa ta koma Mata lokaci guda, ga wata azabtacciyar soyayyar Hafiz da tai mata muguwar damk'a, gashi Yanzu Hafiz ko kad'an bayabin ta kanta ba kamar daba, hakan yasa Humaira k'ara shiga cikin matsanancin damuwa tana ganin kamar saboda Wannan lalura d'in datake fama dashi ne, kullum cikin kuka take, Mama Tai Mata fad'an Tai Mata nasihar harta gaji Haka zalika Habiba tana iya bakin k'ok'arin ta na ganin ta kwantar Mata da hankali.
   Yau tana zaune ta zabga tagumi siraran hawaye nabin fuskarta, tana Wasa da yatsun hannunta ita kanta tausayin kanta takeyi a halin yanzu, saboda kullum da Hafiz take kwana take tashi, Yanzu kawai burinta shine Allah ya yaye mata Wannan soyayyar tashi datake fama da ita.
Hafiz ne ya shigo hannunsa ruk'e da wani text book ganin Humaira a zaune ta juya baya yasashi K'are Mata kallo, sosai ta bashi tausayi ganin yadda ta rame lokaci guda, ga wani hasken budurci daya k'ara fito da ainihin kyanta, yaudai yayi aniyar tunkarar ta saboda ya kasa danne zuciyarsa akanta, cikin natsuwa ya k'arasa wajan ya zauna, jin alamun har yanzu tana can duniyar tunani yasashi d'an ta6ata, a birkice ta juyo yayinda idanunta sukai Mata tozali da Hafiz, sosai ta rud'e ganin yadda ya kafeta da sexy eyes d'insa, cikin sanyin murya Tace "Yaya Hafiz Ina wuni?"
Girgiza Mata kanshi yayi tare da yi Mata nuni Lafiya k'alau, shiru tayi ta kawar da kanta gefe saboda yadda zuciyarta ke saurin harbawa, kamar Kuma a mintsineta Tace "Yaya Hafiz Exams d'ita ta WAEC Yaya zanyi" ta k'arashe fad'a tamkar zatai Mai kuka.
Ganin zayyi magana yasata katseshi da cewar "ka rubutamin a wayarka na karanta"
Ba musu ya zaro wayarsa yayi Mata rubutu kamar Haka _"Kinyi matuk'ar kyau"_
Humaira tana duba text d'in batasan lokacin da murmushi ya su6uce mata ba Tace "Nayi fushi, kaida baka kulani Yanzu" ta fad'a tana tuno Mai Baki.
Lumshe idanuwansa yayi saboda hakan ba k'aramin yimai kyau tayi ba, kar6ar wayar yayi ya  rubuta cewar _"Nayi missing d'inki yadda bakya tsammani, I missed you so much"_
Cike da zak'uwa ta kar6i wayar ta karanta batasan lokacin data saki wani k'ayataccan murmushi ba har Saida fararan hak'oranta suka bayyana, lumshe idanuwanta tayi tana mishi wani irin kallan da ita kad'ai ce tasan ma'anarsa, shiru tayi tana kallan sa yayinda shima kallan nata yake murmushi shinfid'e a fuskarsa.
Wayarsa ya ka6a yace "Wai bakya jina ko kad'an?"
Humaira ganin yayi motsi da bakinsa Kuma bataji Mai yace ba yasata 6ata rai, cike da shagwa6a tace "Me kace?"
Hafiz kafeta yayi da Ido Yana Mai Jin sonta har cikin zuciyarsa.
Tashi yayi, yayi Mata nuni da Yana dawowa.
D'aga Masa Kai tayi alamun "To"

_********_

Su Twins ne suka shigo a guje cikin gidan ko wannan su ruk'e da sabon key d'in mota a hannunsu suna dariya sukaje suka cema Hafsa "Mom kalli?" Suka d'aga key d'in suna nuna Mata.
Murmushi Hafsa tayi tace "Nasan Daddy d'inku ne ya siya muku, Allah ya k'ara bud'i"
   Dariya sukayi sukace "Baki cinka ba, Umma ce ta siya Mana, Tace Saura mu runk'a gudu a titi taji labari ta amshe"
   Hafsa Tace "Eyye 'yan gata Kenan, to an gode, Saura ta bakin nata ku runk'a gudu akan titi"
Affan yace "Mom kinsan dai Ni banma iya gudu a mota ba, dama Areef ne yawwa to ogane"
Hafsa Tace "Kun nunawa Auntynku?".
Areef yace "A'a Zamu shigo ita kuma mukaga zata fita"
  Gyad'a kanta tayi Tace "sai kula Banda tuk'in ganganci kunga har yanzu ku yarane"
  Gabaki d'ayansu sukace "Insha Allahu"
Areef ne yace "Bro ajiye key d'in mu zaga gari da mota na"
Ba musu Affan ya ajiye key d'in suka fito yayinda Hafsa tana kallansu murmushi shinfid'e a fuskarta.

Hafiz k'aramar wayarsa ya d'auko had'e da sabon SIM ya mik'a Mata murmushi shinfid'e a fuskarsa, kar6a tayi tana Mai yimai godiya murna fal cikin ranta.
Jin hannunta na vibrating yasata duba wayar text taga ya shigo tana dubawa taga an rubuta _"Ki ruk'e ta a hannnunki zamu runk'a magana"_
Murmushi tayi ta tura masa da text kamar Haka _"Nagode k'warai da gaske Allah ya saka da Alkhairi"_
Murmushi Hafiz yayi ya tura mata da  cewar _"Kinfi Haka, oya shiirya Kizo ki ragani"_
Tsalle tayi ta shiga d'akinsu Dan shiryawa, yayinda Hafiz ya shafa kyakykyawan sajansa Yana Mai yin murmushi.

Areef sai uban gudu suke yake tsalawa yayinda Affan yake mishi magana akan ya rage speed d'in motar, kafin suyi Wani yunk'uri tuni Areef ya d'an goga Hafiz, a tsorace Humaira ta k'walla k'ara tana Kiran Hafiz, Hafiz kakka6e jikinsa yayi tare da Mata nuni Babu komai.

Humaira hararar motar kawai takeyi ganin har yanzu Babu Wanda ya fito a cikinsu, cikin zafin nama ta nufa motar tare dayin knocking, Affan ne ya zagayo Yana Mai Bata hak'uri Amma Ina Humaira ko kad'an batajin sa, cike da masifa Tace "Ku Baku da hankaline Zaku Kama ku bige mutum Amma saboda tsabagin girman Kai bazaku fito kuba mutane hak'uri ba saboda Kun isa..."

Affan ne yake ta faman Bata hak'uri Amma ko kad'an batajin sa, Hafiz ne yacema Affan "Sorry batajine, Babu komai Zaku iya tafiya"
Sosai abun yaba Affan mamaki, kallanta ya tsayayi yana Mai tausaya mata, mota ya shiga yaga Areef a hakince yace "Kai ka had'a gurmi Amma ka banni a ciki"
K'wafa Areef yayi yace aidana fito Dana zabga Mata Mari Naga alamun batada mutunci kana Bata hak'uri Amma sai wani jaraba take maka"
Numfasawa Affan yayi yace "Batajin magana"
Kallan rainin hankali Areef yayi yace "Tayaya hakan zai faru ga muryarta Nan rad'au zakace batajin magana"
Affan yace "Nima abunda nake tunani Kenan"

    Maryam cike da zak'uwa tacema Aneesah ki k'ara gudun motar Nan muyi mu Isa wajan Bokanki.

*Domin samun cigaba da karanta littafin Gararin rayuwa zaku turo da katin MTN na Naira 200 kacal ta wannan Numbern 08130515037, in kuma kina da buƙatar VIP zaki biya akan farashi mai matuƙar sauki akan naira 400 kacal ta wannan Numbern 08130515037, nagode nice taku har kullum Mum Irfaan ina matuƙar alfahari da masoyana💓❤️, asha karatu lafiya sai kunzo*

*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*

Mum Irfaan ceeee
Er-Gafaii

GARARIN RAYUWAWhere stories live. Discover now