Mama kuwa tunda ta tabbatar da Hafiz yabar gidan tazo inda Humaira take Tace "Oya maza tashi Kizo ki tafi tunda Mai hanaki zuwan baya Nan"
Ba musu Humaira ta saka Hijab d'inta ta fito daga d'akin da suke kwanciya, Habiba ce Tace "Amma Mama Yaya yafa hanata D'azu, Kuma Kinga Baba ya ganta fad'a zai muku daga ke har ita...."
Bata Bari ta k'arasa ba Tace "Ke Dallah rufamin Baki Kona Zo Nan na maujeki, Baku nakema gata ba, Kuma in k'arajin kinyi magana, Allah yaso Rukayya itama Bata Nan da Ina tunanin dukana zakuyi, gwanda da tatafi can hostel tana kwana", kallan Humaira tayi ta zabga Mata harara Tace "Uban me kike jira da bazakiyi gaba ba"
Hak'uri Humaira ta Bata ta d'auki ragowar tallan Dan kuwa wani almajiri ya d'auka d'azu shiyasa baikai yawan na d'azun ba.
Tana fita ta hango Hafiz zaune cikin abokanan a k'ofar gida, suna had'a Ido tayi sauri ta sadda kanta k'asa ta fara sauri-sauri Dan Kar ya k'ara dakatar da ita Mama Tai Mata abinda batai tsammani ba.Hafiz excuse ya nema wajan a bokanansa ya biyo Humaira, yayinda harta Sha kwana tayi nisa kad'an, cikin sassarfa Hafiz ya cafko hannunta, fuskarsa Babu alamun fara'a yace "Aisha bakyajin magana ko?, Bana hanaki D'aukar tallan Nan ba"
Marairaice fuska tayi tace "Kayi hak'uri Yaya, Naga da sauran abincin ne shiyasa nace Mama ta kawo na fitar Mata dashi wajan masu Saida rake...."
Ganin irin kallan da yake binta dashi ne yasata yin shiru, sauke Mata kayan yayi yace "Tafi gida"
Rau-rau tayi da idanunta tace "Please Yaya kabani na tafi, wallahi bazan iya komawa gida ba, kaima kasan halin Mama fa, ince Mata Ina nakai kayan?"
Kallanta yayi da sexy eyes d'insa Ido cikin Ido, tuni taji kasala na neman kamata, kawar da kanta gefe tayi ta sauke kayan kamar yadda ya Umarceta, kallansa tayi yayinda shima ita yake kallo, ganin Babu hanyar da zata wuce sanadiyyar ya saka hannayansa Tace "Yaya Zan wuce gida"
Kamo hannunta yayi a tare sukaji wani shock, gabaki d'ayansu basusan lokacin da suka rabu da hannayansu ba, kallanta kawai yake, Humaira ita Kuma kanta na k'asa domin kuwa a halin yanzu batasan inda hankalinta yake ba, Dan tsigar jikinta ba k'aramin tashi tayi ba.Hannunsa ya cire, yayinda ya sassauta muryar sa yace "Dan Allah karki min fassara daban"
Shiru tayi kanta na k'asa Dan batasan ta had'a Ido dashi, harta fara tafiya saita tsaya, yayinda Hafiz hannayansa na k'irjinsa Yana kallanta, a hankali Humaira ta jiyo Tace "Yaya Nifa Mama nakejin tsoro, karta tambayeni Ina kayana"Hafiz yace ''Ki tafi Babu damuwa inta tambayeki kice mata Nina amsa"
Ba musu Humaira ta kama hanyar gida zuciyarta cike take da tsoron abunda Mama zatai mata.
Tana raku6e a zauran gidan Tai sallama, Mama jin muryar Humaira yasata fitowa taji menene ya dawo da ita gida, ganin har yanzu Bata shigo ba yasata yin zargin kota 6arar da kayanne, kasa jurewa tayi ta nufa hanyar zauran, ganin Humaira tayi Babu talla akanta, wani Ashar ta mulmula Tace "Ina Kika barmin dukiyata?"Humaira cike da tsoro da fargaba Tace "Ya.....ya...ya...ce...in.. da..wo... gida....Kuma....."
Bata Bari ta k'arasa ba Tace "Kuma Ubanki, muguwar yarinyar, yo muguwa man in Banda mugun Abu irin naki tayaya Zan d'aura Miki talla ki Bari wancan yaron ya ganki, na rantse da girman Allah zaki....."
Habiba ce ta katseta da cewar "Mama!, Haba Mama da iliminki, kinsan abunda kikeyi Bai kamata ba, ki tuna kema kina da 'yaya Mata, Yanzu Dan Allah manene amfanin d'aura Mata talla alhalin mu Koda Wasa Baki ta6a d'aura Mana, Mama d'a fa na kowa ne nasan kinsan da haka...."
Bata Bari ta k'arasa ba ta had'e Rai tare da nunata da hannu Tace "Habiba Ni sa'arki ce?, Ki fita idona ki kiyayeni wallahi zanyi mugun 6ata Miki Rai, bar wajan Nan" ya fad'a tana nuna Mata hanyar shiga cikin gida.
Ba musu Habiba ta tafi ranta Sam Babu dad'i akan abubuwan da mahaifiyarta takema Humaira.
Mama ta bud'e Baki zata k'ara yiwa Humaira fad'a Kenan taji sallamar me gidanta, tuni ta washe Baki tare da rungumota jikinta Tace "Allah yayi Albarka 'yata, Allah ya albarkaci rayuwarki" d'aga Ido tayi ta hango mijin nata fuskarsa d'auke da fara'a yace "Uwargida ran gida"
Murmushi tayi yayinda ta taho amsar kayansa.
Humaira itama kar6ar kayan tayi tana murmushin gefen Baki tana mamakin makirci irin na Mama, Dole kishiyoyi su kasa Zama da ita saboda makircinta.Ai tuni Humaira tayi ajiyar zuciya Kona komai yau zata Shana a cikin gidan.
Tashi tayi ta nufa d'akin kwanciyar su, yayinda Habiba tana cikin d'akin tana safa da marwa, ganin Humaira ta shigo hankali kwance Tace "Humaira ba abunda Mama Tai Miki ko?"Murmushi Humaira tayi Tace "Ai Baba ne ya dawo shiyasa Bata Gama fad'an ba"
Habiba ruk'o hannunta tayi Tace "Dan Allah Humaira ki runk'a hak'uri da halayan Mama, nasan Bata kyauta Miki"
Murmushi Humaira tayi Tace "Wallahi ko kad'an Aunty Habiba bana damuwa da abunda Mama takemin saboda inadaku, ganinku kawai ke Sakani farin ciki"
Murmushi Habiba tayi Tace "Kin Gane lesson d'in da Yaya Hafiz yayi Miki ko Kinaso na maimaita Miki?"
Humaira Tace "Saidai ki k'aramin ko kad'an ne domin kuwa Alhamdulillahi na iya"
Habiba Tace "Oya Jeki d'auko muyi...."
Bata k'arasa ba saiga k'awar Habiba ta shigo tace "K'awata albishirinki?"
Habiba Tace "Goro"
Cike da d'auki tace "Yaudai mutuniyarki tazo zata bud'e Wannan babban hospital d'in"Habiba tace "kar kincemin Doctor Hafsa 'yar president maici Yanzu commissioner of health?"
Dariya Ummi tayi Tace "Wallahi ita, Kinga motoci kuwa da jiniyoyi, to Wallahi tafi kyau a fili akan yadda ake nunata a jaridu da gidan talabijin"
Habiba marairaice fuska tayi Tace "Uhm nasan ko naje baza'a barni na ganta ba"
Ummi Tace "Ki gwada tukunna, Kika sani a Dace, Kinga fa result d'inki yayi kyau, ki duba dai hanyoyin Baba a matsayinsa na Mai gari Amma har Yanzu ba'a d'auke ki aiki ba, Kuma result d'inki yayi kyau sosai, Kuma ki duba kiga tun yaushe Yaya Hafiz ya Gama nashi master's d'in Amma shima shiru kawai akeji na neman aiki, Kizo muje, idan munga Babu halin ganinta sai mu hak'ura, Amma Ina Mai tabbatar Miki kina ganinta aikin warke kisa a ranki kin samu aiki"
Rausayar da kanta tayi ta janyo veil d'inta tace "Muje, Ni Wallahi matar tana bala'in burgeni ne" harta Kai bakin k'ofa ta hango Humaira raku6e a jikin bango Tace "Ko Zaki?"
Da sauri Humaira ta d'aga kanta saboda tasan inhar Baba yabar gidan Ubanta zataci tunda masu ceton nata basa Nan.
Habiba komawa tayi ta d'auki muhimman takaddunta suka Kama hanya dukkaninsu inda ake bud'e tafkeken hospital d'in dake garin.
*#Comments*
*#Votes*
*#Likes**Mum Irfaan ceeee*
*Er-Gafaii*
YOU ARE READING
GARARIN RAYUWA
ActionLittafin GARARIN RAYUWA Yana d'auke da tausayi, nadama, tsantsan soyayya, nishad'antar wa, fad'akarwa, wa'azantarwa da d'unbun Dana sani, yarinya ce batasan Hawa ba batasan sauka ba, ana haifarta aje a yadda ita ba tare da an k'ara waiwayanta ba, Iy...