Humaira ganin gari ya fara duhu yasata jin tsoro ganin irin gonar da Kande ta ajiyeta tamkar Daji, tsugunna wa tayi tana jiranta, ga sanyin yamma ya fara sauka, tsuke jikinta tayi tana rawar sanyi, saboda yanayin wajan, ganin garin na k'ara duhu yasata rushewa da wani irin marayan kuka tana fad'in "Babana" tare da ta6e Baki, kamar an tsikara Mata wani Abu ta tashi a zabure ta tashi tare da k'ullin kayanta a hannu ta fara waige-waige tama rasa Ina zata nufa, gashi ta rasa ta Ina suka taho, ganin gabas yasata nufa tana tafiya tana kuka mai tsuma zuciyar Mai sauraro, tuni Humaira ta kutsa can cikin wannan k'auyan tana kalle-kalle, Bata ankara ba taji tayi karo da mutum, tuni ta k'ara tsorata tare da niyyar guduwa.
Jin Ado yace "Waye anan?" Yasata yin muk'us ta la6e a wata bishiyar kuka tana rarraba idanu, ganin Yana k'ok'arin dubawa yaga ko waye yasata yin shiru tsoro da fargaba ya cika ta, hasko touch light yayi yaga yarinya lafe a jikin bishiya, tsoro da fargaba duk ya cika Mata zuciyarta, addu'a d'auke a bakinsa ya k'arasa inda take yace "Ke wacece?"
Shiru tayi ba amsa, ganin Yana takura Mata da tambaya yasata 6are Baki tahau yimai kuka tana fad'in "Babana"
Tuni Ado ya Gane cewar 6acewa tayi, Dan shi baima ta6a ganinta a garin ba kasancewar k'aramin gari, matsowa yayi kusa da ita, yayinda ta k'ank'ame jikinta tsoro fal zuciyarta.
Ado ganin ta tsorata dasi yace "Ki natsu ba abunda Zan Miki, Zan kaiki wajan Babanki ne kinji"
Tanajin Haka tayi saurin k'arasawa wajansa Tace "Da gaske zaka kaini gun Babana?, Mamace Tace in zauna zata nemomin abinci shine har yanzu Bata dawo ba" ta fad'a tare da rausayar da kanta.
Ado murmushi yayi yace "Karki damu" tunda ya ganta yasan ba 'yar garin bace ganin yadda shigarta tafi tasu, hakan na nufin 'yar wani garin ce daban.
Tafiya Mai d'an nisa sukai suka Isa cikin garin, direct gidansu ya nufa da ita, sasan mahaifin sa ya shiga Nan ya taradda sunyu tuwon dawa miyar ayayo, Zama yayi ya gaidasu, yayinda mahaifiyar sa taita faman kallanshi hannunsa ruk'e Dana Humaira, kasa shiru tayi Tace "Kai Kuma daga Ina na ganka da 'yar mutane?"
Zama yayi kusa da mahaifinsa yace "Dogon labari ne, ku Gama cin abincin tukunna"
Mahaifin sane ya gaza cin abincin yace "Kai kuma Ado a ina ka samo yarinyar Nan mai kyau haka?"
Hararar sa mahaifiyar Ado tayi, Tace "Magana muke maka"
Ado gyara zama yayi ya kwashe duk abunda ya faru tsakanin sa da Humaira yayi sannan ya d'aura da cewa "Ga dukkan alamu 6acewa tayi, Kuma ita kanta batasan garinsu ba, ga shawara mana, maizai Hana mu zauna da ita tunda Inna yanzu Babu wata ragowar 'ya mace a hannunki duk kin aurar dasu"
Inna shiru tayi Tana tunanin Mijinta, da Kuma d'an ta Dan yadda kasan bunsuraye wajan neman matan banza da k'ananan Yara yasata kasa cewar zata ruk'e Humaira, Kar azo a 6atawa yarinyar mutane rayuwa Dan Allah bazai barta ba.
Mijinta ne ya katseta da cewar "Gaskiya Ado kayi matuk'ar tunani da shawara me kyau, kaga sai inje in gyara Mata d'akin Uwani tunda tayi aure saita runk'a Zama acan.
Ado ne yace "Da nace Zan kaita Sasana kaga saita runk'a Taya Hajara hira"
6ata Rai mahaifin sa yayi yace "Wata Hajaran, so kake suyi hauka kawai Dan nasan Halin matarka tass, a barta anan d'in ta runk'a d'ebewa mahaifiyar ka kewa"
Ba Haka Ado yaso ba Amma Babu yadda ya iya haka ya nufa nashi sasan, Ransa Babu dad'i.
Mahaifin Ado kuwa da kanshi ya tashi yaje Yana gyarawa Humaira wajan kwana.
Mahaifiyar Ado ganin Mijin Nata ya fita yasata janyo Humaira Tace "Idan kin shiga d'aki ki tabbatar kin saka sakata, duk Wanda zai buga Miki k'ofa Karki bud'e inba Haka ba dodone zai cinyeki ki mutu, ko muryar Ado kikaji kota mahaifin sa Karki sake ki bud'e fa"
![](https://img.wattpad.com/cover/225790984-288-k856480.jpg)
YOU ARE READING
GARARIN RAYUWA
ActionLittafin GARARIN RAYUWA Yana d'auke da tausayi, nadama, tsantsan soyayya, nishad'antar wa, fad'akarwa, wa'azantarwa da d'unbun Dana sani, yarinya ce batasan Hawa ba batasan sauka ba, ana haifarta aje a yadda ita ba tare da an k'ara waiwayanta ba, Iy...