PART 4

289 19 2
                                    

Cike da rashin jin dad'in maganar Director d'in Tace "But Sir ya za'ai a yanke hukuncin Nan ba tare da ansanar Dani ba sai gabda abun ya k'arato?"

Kallanta yayi yace "Sorry Doctor Hafsa, a gaskiya banma sa sunanki a list ba, saboda ganin yadda lokaci ya k'ure a matsayin ki na matar aure shiyasa na saka Safina, to wallahi bansan yadda akai aka saka sunanki ba nasan daga sama ne saboda ganin yadda Kika iya aiki cikin k'warewa da iyawa Shiyasa sukace Lallai ranar Monday dinnan za'a tura ku U.S, Kuma Ina kyautata zaton zaku shafe sama da shekara biyu zuwa uku acan..."

Bata Bari ya k'arasa ba Tace "What!, How?, Gaskiya bazan iyaba saidai na rasa aikina, Yaya zanyi da Mijina da Kuma Family Dina?"

Director gyaran murya yayi yace "Cool down, zaki iya tafiya da mijinki domin an Baku damar yin Haka, Kuma kinsan inhar kikace baza kije Wannan course d'in ba zai ja Miki Matsala wajan aikinki...."

Ba tare data k'ara barin ya k'arasa ba Tace "Am so What, ban damu da hakan ba, nidai na Gama magana Babu inda zani"

Figar Jakarta tayi zuciyarta babu dad'i, tasan Dole taje tunda tasan mahaifiyar ta zataji labari, ita Kuma ganin kamar d'aukaka ce zata riski 'yarta zata Bata Umarnin Lallai sai ta tafi, tausayin kanta kawai takeyi, Babu Wanda ya damu da damuwarta, ga Humaira zata tafi ta barta wajan azzaluma Kande, wunin Ranar Haka ta koma tamkar Mara laka a jiki.

Tunda Hajiya Hajara taji wanna kyakykyawan albishir na an d'auki nauyin su Hafsa akan zasuje babban asibitin dake birnin U.S course farin cikin ta ya kasa 6oyuwa ta k'ara jin kanta a sama, dama burinta da zaran Mijinta ya Samu takarar shugaban k'asa yaba Hafsa minister of health ganin yadda Allah ya d'aukakata ta k'ware wajan aikinta, tunda taji labarin amsar da Hafsa ta bayar tahau jaraba Nan take ta kirata a waya Tai Mata tatas tare da fad'in ta shirya tafiya Babu fashi, itadai Hafsa to kawai Tace, bayan sun Gama wayarne ta kifa kanta taita faman yin kuka.

Sa'eed d'akin Hafsa ya dosa yaji kukanta, shi har mamakin kukanta yake ganin ko gajiya batayi, zuwa yayi ya zauna kusa da ita, tare da saka Mata kanta kan cinyoyinsa, shafa bayanta yake Yana fad'in "Haba Hafsa Wai so kikeyi ki sama Kanki Ciwo ne?, Kullum cikin kuka kike bakya gajiya?, Kwana biyu Ina ganin abun yayi sauk'i Ashe Bata canza zani ba, meya faru kuma?"

Cikin kuka Tace "Ba Umma bace"

Sa'eed yace "Me Umman Tai Miki?"

Hafsa kwashe komai tayi ta fad'a Masa, sannan ta d'aura da cewa, "Dan Allah Ina neman alfarmarka, karka barni na tafi"

Kafeta yayi da Ido yace "Saboda me Hafsa, Wannan abunda ya faru cigabanki ne fa, danme yasa bakyason zuwa?"

Turo mai Baki tayi gaba Tace "Saboda 'yata banason ta shiga *GARARIN RAYUWA* kaida Umma Kun rabani da ita, yanzu Ina bibiyarta nayi Imani inhar nai nesa da ita bansan abunda zai faru da ita Nan gaba ba, Dan Allah Yaya Sa'eed inaso ka zamemin aboki ba Miji ba ka manta da komai nasan ban cuceka ba, ban ha'inceka ba wallahi Dan Allah ka rufamin asiri karka Bari rayuwar 'yata ya salwanta, inba Haka ba wallahi bazan yafe muku ba Kuma bazan yafewa kaina ba"

Sa'eed kallanta yayi yace "Ina Kika kaita?"

Had'iye wani Abu tayi a zuciyarta Tace "Na yadda itane, amma nasan inda take"

Numfasawa yayi yace "Shikenan, ko ba aure a tsakaninmu 'yarki 'yatace, insha Allahu Zan kula Miki da ita, ki shirya gobe ki kaini inda take"

Wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarta ko ba komai ya faranta Mata Rai duk da Tanajin haushinsa, hugging d'insa tayi Tace "Nagode Yayana nasan in kowa Yana juyamin baya Kai bazaka juyamin baya ba, kaid'in na musamman ne"

Murmushi yayi ko ba komai yau zasu kasance cikin farin ciki mara misiltuwa, kallanta yayi yace "Ina fatan Gimbiyata ta yafemin abunda ya faru?"

Had'e fuska tayi tace "Ba yanzu ba tukun"

GARARIN RAYUWAWhere stories live. Discover now