EPISODE 18

9 0 0
                                    

*✍️MARUBUCIYA✍️*.
   

Daga Alkalamin👇

*Ummu Dilshad*

*Wannan littafin na kuɗine, ₦200 ne kacal zakuyi Mobile Transfer (0158547894, GTBANK, SHAMSIYA ABDULLAHI). Ko Card na MTN zaku ɗauki hoton shi ku turo ta *(07013872581).*

*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin

أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!

                      ✍️_18

Zuwa inajin ƙarar sukuwar yana ƙaruwa.

Altine na Rufe baki, Shugaba ta fara magana cikin ruɗewa da ƙara tace "Akwai hanya ɗaya kowacce ta samu ƙoƙon da aka ɗibi Alkairai ta kife tayi rub da ciki akai har zuwa sanda zance kowa ya tashi karya ɗaga.

Nan take kowacce tayi yadda shugaba tace, suna gama kwaciya akan ƙoƙunan sai waɗannan matasan suka fito daga ɗakin da gudu su dayawa aƙalla zasu kai su ɗari uku da Hamsin.

Suna zuwa fallon sai wasu guda Ɗari da akasha jinin su suka jeru sukayi dogon layi  kowacce ta ɗaga hannayenta biyu kamar mai yin addu'oi bayan hannayen su yana kallon inda waɗannan ƴan ƙungiyar suke, kan kace meye wannan waɗannan matan sun buɗe bakunan su atare suna Faɗin "Allah..Allah..Allah...Allah..Allah..Allah..Allah"   mai maitawa kawai sukeyi babu ƙaƙƙautawa. Duk sanda suka buɗe baki suka faɗi ALLAH sai kiga wani haske ya fito da ƙarfi daga jikin waɗannan members ɗin dake kwance rufda ciki, ya shiga jikin waɗannan hannayen. sukuma members ɗin duk sanda Hasken zai fita daga hannayen su sai suyi wata girgiza wacce ke barazanar ɗagasu daga kan wannan ƙoƙunan da suka kwanta akai.

Sosai suka ƙara ƙanƙame ƙoƙunan, sukuma ƴan matan nata ambatar sunan Allah, Ragowar matan kuma guda  ɗari biyu da Hamsin da ba'a kai ga fara shan jinin su ba sai kawai suka nufi hanyar fita suka dinga barin gurin.

waɗannan da aka sha jinin su basu bar gurin ba har sai da komai na daga jinin su dake jikin waɗannan mutanen ya gama fita ta sigar haske ya koma cikin hannayen su ta kafar da aka yanka su, Sannan suma suka juya suka fice suka bar gurin.

bayan fitar su da ƙyar shugaba ta yunƙura ta tashi ta zauna tana nishi kamar wacce tayi yaƙin badar. cikin muryar kasala ta fara magana tace "kowacce ta tashi ta laluba cikin ƙoƙunan tasaka yatsanta ta lashe ragowar danshin jinin dake ciki dan ta samu Ruhinta ya iya komawa gangar jikin ta.

MARUBUCIYA.....Where stories live. Discover now