EPISODE 5

31 4 0
                                    

*✍️MARUBUCIYA✍️*.

*_INTELLIGENT WRITERS_ _ASSOCIATION...®️✍️_*
*_(Onward together)._*

Daga Alkalamin👇
*Ummu Dilshad*
Wattpad @UMMUDILSHAD.

*Dedicated to, Hafsat Hafnan (Lovable Auta💖)*

*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin

أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!

✍️_5
Da ƙarfi ya banko ƙofar ɗakin Amadu, ya fizgoshi ya fara aikamai da duka tako ina harya kaishi ƙasa bai daina dukanshi ba tareda faɗin shege baƙin Azzalumi mu zaka ci amana muyin maka alfarma da sutura mukuma kake ƙoƙarin ganin ka mana tsirara ka tona mana asiri wallahi baka isa ba, yau saina ga bayan ka, dukanshi ya cigaba dayi har sai dayaga ya daina motsi sannan ya fito da gudu daga ɗakin ya maida ƙofar ya rufe, ya nufi call center dake kusa ya bayar da number Alhaji Yusuf aka kiramai shi daga kasuwa ya shaida mai cewa yazo gida yanzu dan babu lafiya, sannan ya dawo ɗakin ya tsaya yana jira.

har Abba ya iso Amadu Ado Kanti bai farfaɗo ba, yana shigowa ɗakin ya taras da su biyun duka akwance nan fa ya ruɗe yafara tanbayar Umar shin me ya samesu ne yagansu a kwance ko mutuwa sukayi?

amsamai yayi da cewa "A'a Abba ba mutuwa sukayi ba, dama ɗazu da Amadu yacemaka bashi da lafiya ne a kasuwa to sai na hangeshi ya nufi shagon kayan ruwa to saina bishi a baya daya fito daga nan sai naga ya nufi shagon magunguna yace a bashi maganin bacci to sai raina sam bai bani cewa yana da gaskiya ba kawai sai na ƙara binshi a baya sai naga kuma ya nufi shagon Ɗan liti, sunata hira da yaran shagon har naji suna tanbayar shi lafiya bai kasance a shangon su ba yanzu, sai yace musu wai wallahi yace maka ya gajine amma kuma wani aiki yakeso yaje yayi sai naji sun kwashe da dariya suna tanbayar shi cewa badai aikin ɗibar roman cika zaije ba yace shine mana ai wannan cikar ma dole sai tana bacci romonta zai shawu dan so yake yana gamawa da ita zai tattara kayanshi yabar garin ya tafi garin su kuma bazai ƙara dawowa ba.

har ya nuna musu abubuwanda ya siyo domin aikin sai suka kwashe da dariya, yabar gurin naga ya hau abun hawa ya wuce.

to nima abun da ya hanani isowa da wuri abu n hawanne ba samu da wuriba.

MARUBUCIYA.....Where stories live. Discover now